< Numbers 3 >

1 These are the generations of Aaron and Moses, in the day when the Lord spoke to Moses on mount Sinai.
Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa a lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai.
2 And these are the names of the sons of Aaron: his firstborn Nadab, then Abihu, and Eleazar, and Ithamar.
Sunayen’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar.
3 These are the names of the sons of Aaron, the priests who were anointed and whose hands were filled and consecrated in order to exercise the priesthood.
Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Haruna, shafaffun firistocin da aka naɗa domin su yi aiki firist.
4 For Nadab and Abihu died without children, when they offered, in the sight of the Lord, a strange fire, in the desert of Sinai. And so, Eleazar and Ithamar exercised the priesthood in the sight of Aaron, their father.
Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.
5 And the Lord spoke to Moses, saying:
Ubangiji ya ce wa Musa,
6 “Bring forward the tribe of Levi, and cause them to stand in the sight of Aaron the priest, in order to minister to him. And let them keep watch outside,
“Ka kawo mutanen Lawi, ka kuma gabatar da su ga Haruna firist, don su taya shi aiki.
7 and let them observe whatever pertains to the ritual for the multitude, in front of the tabernacle of the testimony,
Za su yi wa Haruna da dukan al’umma aikace-aikace a Tentin Sujada, ta wurin yin aikin tabanakul.
8 and let them take care of the vessels of the tabernacle, serving in its ministry.
Za su lura da dukan kayayyakin Tentin Sujada, suna cika hakkin Isra’ilawa ta wurin yin aiki a tabanakul.
9 And you shall give the Levites as a gift to Aaron and his sons; for they have been delivered to them by the sons of Israel.
Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi.
10 But you shall appoint Aaron and his sons over the service of the priesthood. The outsider who approaches to minister shall be put to death.”
Ka naɗa Haruna da’ya’yansa su yi aiki firistoci; duk wanda ya yi shisshigi a wuri mai tsarki kuwa dole a kashe shi.”
11 And the Lord spoke to Moses, saying:
Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
12 “I have taken the Levites from the sons of Israel. For the Levites, and all the firstborn who open the womb among the sons of Israel, shall be mine.
“Ga shi na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon ɗan fari na kowace mace a Isra’ila. Lawiyawa nawa ne,
13 For every firstborn is mine. From the time that I struck the firstborn in the land of Egypt, I have sanctified for myself whatever is born first in Israel. From man, even to beast, they are mine. I am the Lord.”
gama duk’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”
14 And the Lord spoke to Moses in the desert of Sinai, saying:
Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai ya ce,
15 “Number the sons of Levi by the houses of their fathers and their families, every male from one month and above.”
“Ka ƙidaya Lawiyawa bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya kowane ɗan jinjiri mai wata ɗaya ko fiye.”
16 Moses numbered them, just as the Lord had instructed,
Saboda haka Musa ya ƙidaya su duka, kamar yadda maganar Ubangiji ta umarta.
17 and there were found the sons of Levi by their names: Gershon and Kohath and Merari.
Ga sunayen’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.
18 The sons of Gershon: Libni and Shimei.
Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi
19 The sons of Kohath: Amram, and Izhar, Hebron and Uzziel.
Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
20 The sons of Merari: Mahli and Mushi.
Dangin Merari su ne. Mali da Mushi. Ga kabilan Lawiyawa bisa ga iyalansu.
21 From Gershon were two families: the Libnites, and the Shimeites.
A wajen Gershonawa, kabilarsa su ne Libniyawa, da Shimeyiyawa; waɗannan su ne mutanen Gershom.
22 The people of these were numbered, of the male sex, from one month and above: seven thousand five hundred.
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya zuwa gaba da haihuwa su kai 7,500.
23 These shall encamp behind the tabernacle, toward the west,
Kabilar Gershonawa za su yi sansani ta fuskar yamma, a bayan tabanakul.
24 under the leader Eliasaph the son of Lael.
Eliyasaf ɗan Layel shi ne shugaban iyalan Gershonawa.
25 And they shall keep watch over the tabernacle of the covenant:
A Tentin Sujada, Gershonawa su ne za su lura da mazauni da tabanakul da kuma tentin, abubuwan rufensa, labule a ƙofar Tentin Sujada,
26 the tabernacle itself, and its covering; the tent that is drawn before the doors of the covering of the covenant; and the curtains of the atrium; likewise, the tent that is suspended at the entrance of the atrium of the tabernacle; and whatever pertains to the ritual of the altar; the cords of the tabernacle and all its implements.
da labulen filin da yake kewaye da tabanakul da kuma bagade, da igiyoyi, da kuma kowane abin da ya danganci aikinsu.
27 The kinship of Kohath includes the peoples of the Amramites and Izharites and Hebronites and Uzzielites. These are the families of the Kohathites, having been counted by their names,
Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa.
28 all those of the male gender, from one month and above: eight thousand six hundred. They shall keep watch over the Sanctuary,
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 8,600 ne. Kohatawa ne suke lura da wuri mai tsarki.
29 and they shall encamp toward the south side.
Kohatawa za su yi sansani a kudu da tabanakul.
30 And their leader shall be Elisaphan the son of Uzziel.
Shugaban kabilar Kohatawa shi ne Elizafan ɗan Uzziyel.
31 And they shall take care of the ark, and the table and the lampstand, the altars and the vessels of the Sanctuary, by which they minister, and the veil, and all the articles of this kind.
Su ne da hakkin kula da akwatin alkawari, tebur, wurin ajiye fitila, bagade, kayayyakin wuri mai tsarki da ake amfani da su a sujada, labule, da kuma kome da ya danganci aikinsu.
32 But the leader of the leaders of the Levites, Eleazar the son of Aaron the priest, shall be over those who watch over the care of the Sanctuary.
Babban shugaban Lawiyawa shi ne Eleyazar ɗan Haruna, firist. An naɗa shi a kan waɗanda suke kula da wuri mai tsarki.
33 And truly, from Merari are the peoples of the Mahlites and Mushites, having been counted by their names,
Kabilar Merari su ne Maliyawa da Mushiyawa; waɗannan su ne kabilar Merari.
34 all those of the male gender, from one month and above: six thousand two hundred.
Jimillar dukan jarirai maza daga wata ɗaya ko fiye, 6,200 ne.
35 Their leader is Suriel the son of Abihaiel. They shall make camp on the north side.
Shugaban iyalan Merari shi ne Zuriyel ɗan Abihayil. Za su yi sansani arewa da tabanakul.
36 Under their care shall be the panels of the tabernacle, and the bars, and the columns with their bases, and all the things which pertain to service of this kind,
Kabilar Merari ne aka sa su lura da katakan tabanakul, sandunanta, dogayen sandunanta, tarukanta, dukan kayan aiki da kowane abin da ya danganci aikinsu,
37 and the columns of the surrounding atrium with their bases, and the tent pegs with their cords.
da ginshiƙai kewaye da filin tare da rammuka da turaku da igiyoyinsu.
38 Moses and Aaron, with their sons, shall make camp before the tabernacle of the covenant, that is, on the east side, holding the custody of the Sanctuary in the midst of the sons of Israel. Whatever foreigner approaches it shall die.
Musa da Haruna da’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi.
39 All the Levites, whom Moses and Aaron numbered by their families according to the precept of the Lord, of the male gender, from one month and above, were twenty-two thousand.
Jimillar Lawiyawan da Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga umarnin Ubangiji bisa ga danginsu, haɗe da kowane jariri daga wata ɗaya ko fiye, 22,000 ne.
40 And the Lord said to Moses: “Number the firstborn of the male sex from the sons of Israel, from one month and above, and you shall take their total.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ƙidaya dukan’ya’yan fari na Isra’ilawa maza daga wata ɗaya da kuma fiye ka kuma rubuta sunayensu.
41 And you shall bring the Levites to me, in place of all the firstborn of the sons of Israel, and you shall bring their cattle to me, in place of all the firstborn of the cattle of the sons of Israel. I am the Lord.”
Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”
42 Moses took a census, just as the Lord had instructed, of the firstborn of the sons of Israel.
Haka Musa ya ƙidaya’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
43 And the males by their names, from one month and above, were twenty-two thousand two hundred seventy-three.
Jimillar’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne.
44 And the Lord spoke to Moses, saying:
Sai Ubangiji ya kuma yi magana da Musa ya ce,
45 “Take the Levites, in place of the firstborn of the sons of Israel, and the cattle of the Levites, in place of their cattle, and so the Levites shall be mine. I am the Lord.
“Ka ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan’ya’yan fari na Isra’ila, dabbobin Lawiyawa kuma a maimakon dabbobinsu. Lawiyawa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.
46 But for the price of the two hundred and seventy-three, which exceed the number of the Levites compared to the number of firstborn of the sons of Israel,
Don a fanshi’ya’yan fari 273 na Isra’ilawa da suka fi Lawiyawa yawa,
47 you shall take five shekels for each head, by the measure of the Sanctuary. A shekel has twenty obols.
ka karɓi shekel biyar domin kowannensu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda yake da nauyin gera ashirin.
48 And you shall give the money to Aaron and his sons as the price of those that are in excess.”
Ka ba wa Haruna da’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na’ya’yan farin Isra’ilawa.”
49 Therefore, Moses took the money for those that were in excess, and whom they had redeemed from the Levites
Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.
50 in place of the firstborn of the sons of Israel: one thousand three hundred sixty-five shekels, according to the weight of the Sanctuary.
Daga’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
51 And he gave it to Aaron and his sons, according to the word by which the Lord had instructed him.
Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi.

< Numbers 3 >