< 2 Chronicles 13 >

1 In the eighteenth year of king Jeroboam, Abijah reigned over Judah.
A shekara ta sha takwas ta sarautar Yerobowam, Abiya ya zama sarkin Yahuda,
2 He reigned for three years in Jerusalem, and the name of his mother was Micaiah, the daughter of Uriel, from Gibeah. And there was war between Abijah and Jeroboam.
ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru uku. Sunan mahaifiyarsa Mikahiya ce,’yar Uriyel na Gibeya. Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Abiya da Yerobowam.
3 And when Abijah had undertaken the conflict, and he had with him four hundred thousand elect men, very fit for war, Jeroboam set up a battle line opposite him of eight hundred thousand men, who were also elect and very strong in warfare.
Abiya ya tafi yaƙi tare da mayaƙa dubu ɗari huɗu jarumawa, Yerobowam kuwa ya ja dāgār yaƙi a kan Abiya da mayaƙa dubu ɗari takwas jarumawa.
4 Then Abijah stood upon mount Zemaraim, which was in Ephraim, and he said: “Listen to me, Jeroboam and all of Israel.
Abiya ya tsaya a Dutsen Zemarayim, a ƙasar tudu ta Efraim ya ce, “Yerobowam da dukan Isra’ila, ku saurare ni!
5 Are you ignorant that the Lord, the God of Israel, gave David the kingship over Israel for all time, to him and to his sons, by a covenant of salt?
Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba?
6 But Jeroboam, the son of Nabat, the servant of Solomon, son of David, rose up and rebelled against his lord.
Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa,
7 And there were gathered to him very vain men, and sons of Belial. And they prevailed against Rehoboam, the son of Solomon. For Rehoboam was inexperienced, and he had a fearful heart, and so he was unable to resist them.
sai ya tara wa kansa’yan iska da mugayen mutane suka yi gāba da Rehobowam ɗan Solomon. Rehobowam lokacin kuwa ba shi da wayo, don haka bai iya tsai da su ba.
8 Now therefore, you say that you are able to resist the kingdom of the Lord, which he possesses through the sons of David, and you have a great multitude of people, and gold calves, which Jeroboam made for you as gods.
“Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.
9 And you have cast out the priests of the Lord, the sons of Aaron, as well as the Levites. And like all the peoples of the lands, you have made priests for yourselves. Anyone who is willing to come and perform the ritual by his hand, with a bull from the herd and with seven rams, is made a priest of those who are not gods.
Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji,’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.
10 But the Lord is our God, and we have not forsaken him. And the priests who minister to the Lord are from the sons of Aaron. And the Levites are in their proper order.
“Gare mu kuwa, Ubangiji shi ne Allah, kuma ba mu yashe shi ba. Firistocin da suke bauta wa Ubangiji’ya’yan Haruna maza ne, Lawiyawa ne kuwa suke taimakonsu.
11 Also, they offer holocausts to the Lord, each and every day, morning and evening, and incense composed according to the precept of the law, and the bread of the presence on a very pure table. And there is with us the gold lampstand with its lamps, so that they may burn continually in the evening. For certainly, we keep the precepts of the Lord our God, whom you have forsaken.
Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi.
12 Therefore, God is the commander of our army, with his priests, who sound the trumpets that ring out against you. O sons of Israel, do not choose to fight against the Lord, the God of your fathers. For it is not expedient for you.”
Allah yana tare da mu; shi ne shugabanmu. Firistocinsa tare da ƙahoni za su busa kirarin yaƙi a kanku. Mutanen Isra’ila, kada ku yi yaƙi da Ubangiji Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”
13 While he was speaking these things, Jeroboam set in motion an ambush behind them. And while they stood facing the enemy, without Judah realizing it, his army circled around.
To, fa, Yerobowam ya aiki mayaƙa su zagaya daga baya, domin yayinda yake a gaban Yahuda, sai’yan kwanto su kasance a bayansu.
14 And looking back, Judah saw the war threatening in front and behind, and they cried out to the Lord. And the priests began to sound the trumpets.
Yahuda ya juya sai ya ga cewa ana yaƙe su gaba da baya. Sai suka yi kuka ga Ubangiji. Firistoci suka busa ƙahoni
15 And all the men of Judah shouted out. And behold, when they cried out, God terrified Jeroboam, and all of Israel who were standing in opposition to Abijah and Judah.
mutanen Yahuda kuwa suka tā da kirarin yaƙi. Da ji kirarin yaƙi, Allah ya fatattake Yerobowam da dukan Isra’ila a gaban Abiya da Yahuda.
16 And the sons of Israel fled from Judah, and the Lord delivered them into their hand.
Isra’ilawa suka gudu a gaban Yahuda, Allah kuwa ya bashe su a hannuwansu.
17 Therefore, Abijah and his people struck them with a great slaughter. And five hundred thousand strong men of Israel fell wounded.
Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila.
18 And the sons of Israel were humiliated at that time. And the sons of Judah were very greatly strengthened, because they had trusted in the Lord, the God of their fathers.
Aka cinye mutanen Isra’ila a wannan lokaci, mutanen Yahuda kuwa suka yi nasara domin sun dogara ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
19 Then Abijah pursued the fleeing Jeroboam. And he seized cities from him: Bethel and her daughters, and Jeshanah with her daughters, and also Ephron and her daughters.
Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi.
20 And Jeroboam no longer had the strength to resist, in the days of Abijah. And the Lord struck him, and he died.
Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.
21 And so Abijah, having been strengthened in his authority, took fourteen wives. And he procreated twenty-two sons and sixteen daughters.
Amma Abiya ya ƙara ƙarfi. Ya auri mata goma sha huɗu, ya kuma kasance da’ya’ya maza ashirin da biyu da kuma’ya’ya mata goma sha shida.
22 Now the rest of the words of Abijah, and his ways and works, have been written very diligently in the book of Iddo, the prophet.
Sauran ayyukan sauratar Abiya, abin da ya yi da abin da ya faɗa, a rubuce suke a cikin rubuce-rubucen annabi Iddo.

< 2 Chronicles 13 >