< Uafisawa 1 >

1 Bulus gono kaduran Kristi Yisa nin yinnu Kutellẹ, udu kiti nale na ina fera nani bara Kutellẹ nan nya Afisus, ale na ina yinin nin Yisa Kristi.
Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu.
2 Na ubollu nin tọp Kutellẹ so nan ghinu unuzu kitime uchif bit a Cikilari bit Yisa Kristi.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
3 Na issu Liru Kutellẹ nin Chiff in Cikilari bit Yisa Kristi. Amere na tinari vat uruhu nmari mongo na midi kitene kani nan nya Kristi.
Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.
4 Bara na Kutellẹ na fere nari alle na iyinna nin Kristi uworu a idutu sa ukẹ in yï. Ana fere nari tinan yita lau sa ndinong nbun me.
Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa.
5 Nan nya nsu Kutellẹ yiru nari atta nono me mun nan nya Yisa Kristi. Anan su nani nan nya lanzun mang nilemon na adinin su asu.
A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri.
6 Vat nile imone iwasu, inan su liru Kutellẹ nan nya ngongong nbolu me ulle na ana filli nari nan nya kinayi me.
Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.
7 Kutanki
A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah
8
wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta.
9 Kutellẹ na durso nari ushiri kidegen ka naki nyeshin nafo usu kibinayi me na aduro nan nya Kristi.
Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi.
10 Asa kubin nmalzunu nshiri me nkullo aba munu imon kitene kani nin in yï ulele vat kiti kirum nan nya Kristi.
Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.
11 In nan nya Kristi iwa fere nari uworsu nafo ushiri me na adin su imon vat nin kpilizu kibinayi me.
A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi.
12 Kutellẹ na tinani tinan yita achine bara uzazinu ngongon Me, arikere ale na tiwa yarin uyinnu nin Kristi.
Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah.
13 Kitin Kristiari iwa lanza ligbulang kidegen ulliru lai nin un tuchu mine kitin Kristi, ulle na anung na yinni mun tutun iyatca minu nin likawali nfip milau.
An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki.
14 Uruhari likaran ngadu bit se tinin se uso nan nya kipin tigo Kutellẹ bara liru ngongong me.
Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.
15 Bara nani un woru kubi ko na nwanlanza ubelle yinnu mine sa uyene nan nyan Cikilari Yisa, nin belle nsu vat nale na ina fere nani bara ame.
Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah,
16 Na in sunna ugodo Kutellẹ bara anughe nin yichu tisa mine nyan lira ning ba.
ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina.
17 Ndin lira Kutellẹn Cikilari Yisa Kristi, uchifi ngongonng, ma niminu uruhu inyiru nin puzunu in yinnu me,
Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau.
18 Ndin lire bara iyizi nibinayi mine ti kanang, tinang yinno inyari likara inciwu nibinayi bite. Ndi nlira inan yinnu inyarri ngbardang ngonbong gadu nan nya nalle na issosin lissosin me.
Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa.
19 Iyaghari katin likaran gbardang me nin yiru me kiti nale iyinna, nafo na in gbardang likara katame din su.
Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan
20 Lo likarere wasu katah nan nya Kristi na Kutellẹ wa fiyghe kisek a sonkoghe nchara ulime me nan nya niti kitene kani.
da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya.
21 Ubun nin vat tigoh, a udursuzun nbatinu, likara, usu ligo a kolome lissa lo na ina ni. Ana chewu Kristi ku na nko kuje chas ba, nin du kujin bun wang. (aiōn g165)
Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. (aiōn g165)
22 Kutellẹ nani imon vat nabunu Kristi, amini na tighe asso liti nimon vat kuti nlira.
Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya.
23 Na kunnere kidowo me, ukullu mere din kulusu imon vat tibau ngangang.
Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

< Uafisawa 1 >