Preface
Read
+
Publisher
Nainoia, Inc.
PO Box 462, Bellefonte, PA 16823
(814) 470-8028
Nainoia Inc, Publisher
LinkedIn/NAINOIA-INC
Third Party Publisher Resources
Request Custom Formatted Verses
Please contact us below
Submit your proposed corrections
I understand that the Aionian Bible republishes public domain and Creative Commons Bible texts and that volunteers may be needed to present the original text accurately. I also understand that apocryphal text is removed and most variant verse numbering is mapped to the English standard. I have entered my corrections under the verse(s) below. Proposed corrections to the Hausa Contemporary Bible, Psalms Chapter 119 https://www.AionianBible.org/Bibles/Hausa---Contemporary/Psalms/119 1) Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji. 2) Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu. 3) Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa. 4) Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su. 5) Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana! 6) Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka. 7) Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci. 8) Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum. 9) Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka. 10) Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka. 11) Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi. 12) Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. 13) Da leɓunana na ba da labarin dukan dokokin da suka fito bakinka. 14) Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa. 15) Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka. 16) Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba. 17) Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu; zan yi biyayya da maganarka. 18) Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka. 19) Ni baƙo ne a duniya; kada ka ɓoye mini umarnanka. 20) Zuciyata ta ƙosa saboda marmari don dokokinka koyaushe. 21) Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka. 22) Ka cire mini ba’a da reni, gama ina kiyaye farillanka. 23) Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna, bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka. 24) Farillanka ne abin farin cikina; su ne mashawartana. 25) An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka. 26) Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka. 27) Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka. 28) Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka. 29) Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka. 30) Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka. 31) Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya. 32) Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka’yantar da zuciyata. 33) Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe. 34) Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata. 35) Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki. 36) Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba. 37) Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka. 38) Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka. 39) Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne. 40) Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka. 41) Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka; 42) sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka. 43) Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka. 44) Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin. 45) Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka. 46) Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba, 47) gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu. 48) Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka. 49) Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege. 50) Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina. 51) Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba. 52) Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu. 53) Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka. 54) Ƙa’idodinka su ne kan waƙata a duk inda na sauka. 55) Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka. 56) Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka. 57) Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka. 58) Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka. 59) Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka. 60) Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka. 61) Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba. 62) Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci. 63) Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka. 64) Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. 65) Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji. 66) Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka. 67) Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka. 68) Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka. 69) Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata. 70) Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka. 71) Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka. 72) Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu. 73) Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka. 74) Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka. 75) Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni. 76) Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka. 77) Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina. 78) Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka. 79) Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka. 80) Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya. 81) Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka. 82) Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?” 83) Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba. 84) Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini? 85) Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka. 86) Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili. 87) Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba. 88) Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka. 89) Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai. 90) Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama. 91) Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima. 92) Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana. 93) Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina. 94) Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka. 95) Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka. 96) Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka. 97) Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini. 98) Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni. 99) Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka. 100) Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka. 101) Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka. 102) Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini. 103) Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina! 104) Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba. 105) Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata. 106) Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci. 107) Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka. 108) Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka. 109) Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba. 110) Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba. 111) Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata. 112) Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe. 113) Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka. 114) Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka. 115) Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna! 116) Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata. 117) Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci. 118) Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne. 119) Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka. 120) Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka. 121) Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai; kada ka ni a hannun masu danne ni. 122) Ka tabbatar da lafiyar bawanka; kada ka bar masu girman kai su danne ni. 123) Idanuna sun gaji, da jiran cetonka, da jiran alkawarinka mai adalci. 124) Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka ka kuma koya mini ƙa’idodinka. 125) Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi don in gane farillanka. 126) Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji; ana karya dokarka. 127) Saboda ina ƙaunar umarnanka fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla, 128) saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau, na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba. 129) Farillanka masu banmamaki ne; saboda haka nake yin biyayya da su. 130) Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi. 131) Ina hakkin da bakina a buɗe, ina marmarin umarnanka. 132) Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka. 133) Ka bi da sawuna bisa ga maganarka; kada ka bar zunubi yă mallake ni. 134) Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka. 135) Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka. 136) Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka. 137) Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne. 138) Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai. 139) Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka. 140) An gwada alkawuranka sarai, bawanka kuwa yana ƙaunarsu. 141) Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni, ba na manta da farillanka. 142) Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce. 143) Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina. 144) Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu. 145) Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka. 146) Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka. 147) Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka. 148) Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka. 149) Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka. 150) Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka. 151) Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne. 152) Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada. 153) Ka dubi wahalata ka cece ni, gama ban manta da dokarka ba. 154) Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni, ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta! 155) Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka. 156) Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji; ka kiyaye raina bisa ga dokokinka. 157) Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini, amma ban rabu da farillanka ba. 158) Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka. 159) Dubi yadda nake ƙaunar farillanka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka. 160) Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne. 161) Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka. 162) Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma. 163) Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka. 164) Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci. 165) Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe. 166) Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka. 167) Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai. 168) Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka. 169) Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji; ka ba ni ganewa bisa ga maganarka. 170) Bari roƙona yă zo gabanka; ka cece ni bisa ga alkawarinka. 171) Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka. 172) Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne. 173) Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni, gama na zaɓi farillanka. 174) Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina. 175) Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni. 176) Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba. Additional comments?
Refresh Captcha
The world's first Holy Bible un-translation!