< Luka 3 >

1 A cikin shekara ta goma sha biyar da Tibariyus Kaisar ke mulki, Bilatus Babunti kuma ke jagorar Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, dan'uwansa Filibus yana sarautar yankin Ituriya da Tirakonitis, Lisaniyas kuma na sarautar yankin Abiliya,
Now in the fifteenth year of the reign of Tiberius Caesar, Pontius Pilate being governor of Judea, and Herod being tetrarch of Galilee, and Philip his brother tetrarch of Iturea, and the country of Trachonitis, and Lysanias tetrarch of Abilina;
2 kuma zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, maganar Allah ta zo wurin Yahaya dan Zakariya, a cikin jeji.
Under the high priests Annas and Caiphas; the word of the Lord was made unto John, the son of Zachary, in the desert.
3 Ya yi tafiya cikin dukan yankuna da ke kewaye da Kogin Urdun, yana wa'azin baftismar tuba domin gafarar zunubai.
And he came into all the country about the Jordan, preaching the baptism of penance for the remission of sins;
4 Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, “Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa!
As it was written in the book of the sayings of Isaias the prophet: A voice of one crying in the wilderness: Prepare ye the way of the Lord, make straight his paths.
5 Za a cika kowani kwari, za a fasa kowani dutse a kuma baje kowani tudu, za a mike karkatattun hanyoyi, za a cike hanyoyi masu gargada,
Every valley shall be filled; and every mountain and hill shall be brought low; and the crooked shall be made straight; and the rough ways plain;
6 kuma dukan mutane za su ga ceton Allah.”
And all flesh shall see the salvation of God.
7 Sai Yahaya ya kara fada wa taron jama'ar da ke zuwa domin ya yi masu baftisma, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargadeku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
He said therefore to the multitudes that went forth to be baptized by him: Ye offspring of vipers, who hath shewed you to flee from the wrath to come?
8 Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu.
Bring forth therefore fruits worthy of penance; and do not begin to say, We have Abraham for our father. For I say unto you, that God is able of these stones to raise up children to Abraham.
9 Yanzu kuwa, an rigaya an sa gatari a gindin itatuwa. Sabili da haka, duk itacen da bai ba da 'ya'ya masu kyau ba za a sare shi kasa a kuma jefa shi cikin wuta.”
For now the axe is laid to the root of the trees. Every tree therefore that bringeth not forth good fruit, shall be cut down and cast into the fire.
10 Sai mutanen da ke cikin taron jama'ar suka tambaye shi cewa, “To me za mu yi?”
And the people asked him, saying: What then shall we do?
11 Ya amsa ya ce masu, “Idan wani yana da taguwa biyu, sai ya ba wanda bashi da ita daya, kuma wanda yake da abinci ya yi haka nan.”
And he answering, said to them: He that hath two coats, let him give to him that hath none; and he that hath meat, let him do in like manner.
12 Masu karban haraji ma suka zo domin a yi masu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?”
And the publicans also came to be baptized, and said to him: Master, what shall we do?
13 Ya ce masu, “Kada ku karba kudi fiye da yadda aka umarce ku.”
But he said to them: Do nothing more than that which is appointed you.
14 Wasu sojoji ma suka tambaye shi cewa, “To, mu fa? Yaya za mu yi?” Ya ce masu, “Kada ku kwace wa wani kudi, kada ku kuma yi wa wani zargin karya. Ku dogara ga albashinku.”
And the soldiers also asked him, saying: And what shall we do? And he said to them: Do violence to no man; neither calumniate any man; and be content with your pay.
15 Ana nan da mutane ke sauraron zuwan Almasihu, kowa yana ta tunani a zuciyar sa game da Yahaya, ko shi ne Almasihu.
And as the people were of opinion, and all were thinking in their hearts of John, that perhaps he might be the Christ;
16 Yahaya ya amsa ya ce masu duka, “Game da ni dai, na yi maku baftisma da ruwa, amma akwai wani tafiye wanda ya fi ni iko, ban ma isa in kwance maballin takalmansa ba. Shi zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.
John answered, saying unto all: I indeed baptize you with water; but there shall come one mightier that I, the latchet of whose shoes I am not worthy to loose: he shall baptize you with the Holy Ghost, and with fire:
17 Kwaryar shikarsa na hanun sa domin ya share masussukarsa da kyau ya kuma tara alkama a cikin rumbunsa. Amma zai kona buntun da wuta marar mutuwa.
Whose fan is in his hand, and he will purge his floor, and will gather the wheat into his barn; but the chaff he will burn with unquenchable fire.
18 Da gargadi masu yawa ya yi wa mutanen wa'azin bishara.
And many other things exhorting, did he preach to the people.
19 Yahaya kuma ya tsauta wa sarki Hirudus domin ya auri matar dan'uwansa, Hiruduya, da kuma sauran abubuwan da Hirudus ya yi.
But Herod the tetrarch, when he was reproved by him for Herodias, his brother’s wife, and for all the evils which Herod had done;
20 Amma Hirudus ya kara yin wani mugun abu. Ya sa an kulle Yahaya a cikin kurkuku.
He added this also above all, and shut up John in prison.
21 Ana nan, lokacin da ake yiwa dukan mutane baftisma, aka yiwa Yesu mai baftisma. Lokacin da yake yin addu'a, sai sama ta bude,
Now it came to pass, when all the people were baptized, that Jesus also being baptized and praying, heaven was opened;
22 kuma Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa a kamanin kurciya, sai wata murya ta fito daga sama, “Kai ne kaunataccen Da na. Ina jin dadin ka.”
And the Holy Ghost descended in a bodily shape, as a dove upon him; and a voice came from heaven: Thou art my beloved Son; in thee I am well pleased.
23 Ana nan Yesu da kansa, da ya fara, yana kimanin shekara talatin. Shi dan (kamar yadda ake tsammani) Yusufu ne, dan Heli,
And Jesus himself was beginning about the age of thirty years; being (as it was supposed) the son of Joseph, who was of Heli, who was of Mathat,
24 dan Matat, dan Lawi, dan Malki, dan Yanna, dan Yusufu,
Who was of Levi, who was of Melchi, who was of Janne, who was of Joseph,
25 dan Matatiya, dan Amos, dan Nahum, dan Hasli, dan Najjaya,
Who was of Mathathias, who was of Amos, who was of Nahum, who was of Hesli, who was of Nagge,
26 dan Ma'ata, dan Matatiya, dan Shimeya, dan Yuseka, dan Yoda,
Who was of Mahath, who was of Mathathias, who was of Semei, who was of Joseph, who was of Juda,
27 dan Yowana, dan Resa, dan Zarubabila, dan Shiyaltiyel, dan Niri,
Who was of Joanna, who was of Reza, who was of Zorobabel, who was of Salathiel, who was of Neri,
28 dan Malki, dan Addi, dan Kosama, dan Almadama, dan Er,
Who was of Melchi, who was of Addi, who was of Cosan, who was of Helmadan, who was of Her,
29 dan Yosi, dan Aliyeza, dan Yorima, dan Matat, dan Lawi,
Who was of Jesus, who was of Eliezer, who was of Jorim, who was of Mathat, who was of Levi,
30 dan Saminu, dan Yahuda, dan Yusufu, dan Yonana, dan Aliyakima,
Who was of Simeon, who was of Judas, who was of Joseph, who was of Jona, who was of Eliakim,
31 dan Malaya, dan Mainana, dan Matata, dan Natan, dan Dauda,
Who was of Melea, who was of Menna, who was of Mathatha, who was of Nathan, who was of David,
32 dan Yesse, dan Obida, dan Bu'aza, dan Salmon, dan Nashon,
Who was of Jesse, who was of Obed, who was of Booz, who was of Salmon, who was of Naasson,
33 dan Amminadab, dan Adimi, dan Arama, dan Hezruna, dan Feresa, dan Yahuda,
Who was of Aminadab, who was of Aram, who was of Esron, who was of Phares, who was of Judas,
34 dan Yakubu, dan Ishaku, dan Ibrahim, dan Tera, dan Nahor,
Who was of Jacob, who was of Isaac, who was of Abraham, who was of Thare, who was of Nachor,
35 dan Serug, dan Reyu, dan Feleg, dan Abiru, dan Shela,
Who was of Sarug, who was of Ragau, who was of Phaleg, who was of Heber, who was of Sale,
36 dan Kainana, dan Arfakshada, dan Shem, dan Nuhu, dan Lamek,
Who was of Cainan, who was of Arphaxad, who was of Sem, who was of Noe, who was of Lamech,
37 dan Metusela, dan Anuhu, dan Yaret, dan Mahalel, dan Kainana,
Who was of Mathusale, who was of Henoch, who was of Jared, who was of Malaleel, who was of Cainan,
38 dan Enosh, dan Shitu, dan Adamu, dan Allah.
Who was of Henos, who was of Seth, who was of Adam, who was of God.

< Luka 3 >