< Yoshuwa 4 >

1 Da al’umma gaba ɗaya suka ƙetare Urdun, Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,
When all the people crossed over the Jordan, Yahweh said to Joshua,
2 “Ka zaɓi mutum goma sha biyu daga cikin mutane, ɗaya daga kowace kabila,
“Choose twelve men for yourselves from among the people, one man from each tribe.
3 ka ce musu kowa yă ɗauki dutse ɗaya daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, ku kai su, ku ajiye a inda za ku sauka yau.”
Give them this command: 'Take up twelve stones from the middle of the Jordan where the priests are standing on the dry ground, and bring them over with you and lay them down in the place where you will spend the night tonight.'”
4 Sai Yoshuwa ya kira mutum goma sha biyu da ya zaɓa daga cikin Isra’ilawa, ɗaya daga kowace kabila
Then Joshua called the twelve men whom he had chosen from the tribes of Israel, one from each tribe.
5 ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila,
Joshua said to them, “Go over before the ark of Yahweh your God into the middle of the Jordan. Each of you is to take up a stone upon his shoulder, according to the number of the tribes of the people of Israel.
6 yă zama muku alama. Nan gaba in yaranku suka tambaye ku suka ce, ‘Mece ce ma’anar kasancewar duwatsun nan a nan?’
This will be a sign in your midst for you when your children ask in days to come, 'What do these stones mean to you?'
7 Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.”
Then you will say to them, 'The waters of the Jordan were cut off before the ark of the covenant of Yahweh. When it passed over the Jordan, the waters of the Jordan were cut off. So these stones will be a memorial to the people of Israel forever.'”
8 Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.
The people of Israel did just as Joshua commanded, and they picked up twelve stones from the middle of the Jordan, as Yahweh said to Joshua. They set the stones up according to the number of the tribes of the people of Israel. They carried the stones with them, over to the place where they camped and they set them down there.
9 Yoshuwa ya ɗora duwatsu goma sha biyun a tsakiyar Urdun daidai inda firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya. Suna nan a can har wa yau.
Then Joshua set up twelve stones in the middle of the Jordan River, in the place where the feet of the priests that carried the ark of the covenant stood. The memorial is there to this day.
10 Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Yoshuwa yă gaya wa mutane, kamar yadda Musa ya ce Yoshuwa yă yi. Mutanen suka wuce da sauri.
The priests that carried the ark stood in the middle of the Jordan until everything that Yahweh commanded Joshua to tell the people was completed, according to all that Moses had commanded Joshua. The people hurried and they crossed over.
11 Sai da dukan mutanen suka wuce sa’an nan akwatin alkawari da firistoci suka sha gaba.
When all the people had finished crossing over, the ark of Yahweh and the priests crossed over before the people.
12 Mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse suka ƙetare da shirin yaƙi, suka wuce gaban Isra’ila kamar yadda Musa ya ce su yi.
The tribe of Reuben, the tribe of Gad, and the half tribe of Manasseh passed before the people of Israel formed up as an army, just as Moses said to them.
13 Wajen mutum dubu arba’in shirye domin yaƙi, suka wuce a gaban Ubangiji zuwa filayen Yeriko.
About forty thousand men equipped for war passed before Yahweh, for battle on the plains of Jericho.
14 A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Yoshuwa a gaban Isra’ilawa; suka kuma ba shi girma dukan kwanakin ransa, kamar yadda suka girmama Musa.
On that day Yahweh made Joshua great in the eyes of all Israel. They honored him—just as they honored Moses— all his days.
15 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,
Then Yahweh spoke to Joshua,
16 “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin Shaida su fito daga cikin Urdun.”
“Command the priests who carry the ark of the testimony to come up out of the Jordan.”
17 Sai Yoshuwa ya umarci firistoci ya ce, “Ku fito daga cikin Urdun.”
So, Joshua commanded the priests, “Come up out of the Jordan.”
18 Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a dā.
When the priests carrying the ark of the covenant of Yahweh came up out of the middle of the Jordan, and the soles of their feet were lifted up out on dry ground, then the waters of the Jordan returned to their place and overflowed its banks, just as they were four days before.
19 A rana ta goma ga wata na farko, mutane suka haura daga Urdun suka sauka a Gilgal a gabashin iyakar Yeriko.
The people came up out of the Jordan on the tenth day of the first month. They stayed in Gilgal, east of Jericho.
20 Sai Yoshuwa ya kafa duwatsu goma sha biyun nan da suka ɗauko daga Urdun.
The twelve stones that they took out of the Jordan, Joshua set up in Gilgal.
21 Ya ce wa Isra’ilawa, “Nan gaba in yaranku suka tambayi iyayensu suka ce, ‘Mece ce ma’anar waɗannan duwatsun?’
He said to the people of Israel, “When your descendants ask their fathers in times to come, 'What are these stones?'
22 Ku ce musu, ‘Isra’ilawa sun ƙetare kogin Urdun a kan busasshiyar ƙasa.’
Tell your children, 'This is where Israel crossed over the Jordan on dry ground.'
23 Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa.
Yahweh your God dried up the waters of the Jordan for you, until you had crossed over, just as Yahweh your God did to the Sea of Reeds, which he dried up for us until we passed over,
24 Ya yi wannan ne domin dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji mai iko ne, domin kuma ku zama masu tsoron Ubangiji Allahnku.”
so that all the peoples of the earth may know that the hand of Yahweh is mighty, and that you will honor Yahweh your God forever.”

< Yoshuwa 4 >