< Mark 5 >

1 They came to the other side of the sea, into the country of the Gadarenes.
Da su ka zo daya ketaren tekun, wanda ya ke cikin yankin Garasinawa.
2 When he had come out of the boat, immediately a man with an unclean spirit met him out of the tombs.
Sa'adda Yesu ya sauko daga cikin jirgin ruwan sai wani mutum mai aljanu ya fito daga cikin kaburbura ya tarbe shi.
3 He lived in the tombs. Nobody could bind him any more, not even with chains,
Mutumin yana zama a cikin kaburbura. An daure shi da sarkoki da mari
4 because he had been often bound with fetters and chains, and the chains had been torn apart by him, and the fetters broken in pieces. Nobody had the strength to tame him.
An daure shi da sarkoki da mari sau da yawa, amma ya tsuntsunke sarkoki da marin. har ma ba wanda zai iya daure shi kuma.
5 Always, night and day, in the tombs and in the mountains, he was crying out, and cutting himself with stones.
Dare da rana a cikin kabarbarun da duwatsu mutumin ya na ihu ya na yaiyage jikinsa da duwatsu masu kaifi.
6 When he saw Yeshua from afar, he ran and bowed down to him,
Sa'adda ya hango Yesu daga nesa, sai ya tarbi Yesu ya durkusa a gabansa.
7 and crying out with a loud voice, he said, “What have I to do with you, Yeshua, you Son of the Most High God? I adjure you by God, don’t torment me.”
Ya tada muryarsa da karfi ya ce, ina ruwa na da kai? Yesu Dan Allah Madaukaki Ina rokon ka da sunan Allah kada ka bani wahala,
8 For he said to him, “Come out of the man, you unclean spirit!”
Gama Yesu ya ce masa kai aljani ka fito daga cikinsa.”
9 He asked him, “What is your name?” He said to him, “My name is Legion, for we are many.”
Ya tambaye shi, “Yaya sunanka? Ya ce suna na tari gama muna da yawa.
10 He begged him much that he would not send them away out of the country.
Ya yi ta rokonsa kada ya raba su da wannan yankin kasar.
11 Now on the mountainside there was a great herd of pigs feeding.
Akwai babban garken aladu a wurin suna kiwo a gindin tsauni.
12 All the demons begged him, saying, “Send us into the pigs, that we may enter into them.”
Sai suka roke shi ya bar su su shiga cikin wadannan aladun.
13 At once Yeshua gave them permission. The unclean spirits came out and entered into the pigs. The herd of about two thousand rushed down the steep bank into the sea, and they were drowned in the sea.
Shi kuma ya yardar masu. Aljanun suka fita suka shiga cikin aladun su kimanin dubu biyu. Aladun dubu biyu suka gangaro daga gindin tsaunin suka fada cikin ruwa.
14 Those who fed the pigs fled, and told it in the city and in the country. The people came to see what it was that had happened.
Mutanen da ke kiwon aladun su ka shiga cikin gari da kewaye suka bada labarin abin da ya faru. Mutane da yawa suka je su ga abin da ya faru
15 They came to Yeshua, and saw him who had been possessed by demons sitting, clothed, and in his right mind, even him who had the legion; and they were afraid.
Sai suka zo wurin Yesu suka ga mutumin mai aljanun a zaune, cikin hankalinsa, saye da tufafi, sai suka tsorata.
16 Those who saw it declared to them what happened to him who was possessed by demons, and about the pigs.
Wadanda suka zo su ka ga abin da ya faru da mutumin mai aljanun, suka je suka fada wa mutane abin da suka gani game da aladun.
17 They began to beg him to depart from their region.
Mutanen suka roke shi ya fita daga yankin kasarsu.
18 As he was entering into the boat, he who had been possessed by demons begged him that he might be with him.
Shi mutumin da aljanu ke iko da shi, sa'adda ya ga Yesu zai shiga cikin jirgin ruwa ya tafi, ya roki Yesu da ya bi shi.
19 He didn’t allow him, but said to him, “Go to your house, to your friends, and tell them what great things the Lord has done for you and how he had mercy on you.”
Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa ka tafi gidanku, wurin mutanenka ka gaya ma su alherin da Ubangiji ya yi maka.
20 He went his way, and began to proclaim in Decapolis how Yeshua had done great things for him, and everyone marvelled.
Mutumin ya shiga cikin Dikafolis yana shaidar babban abin da Yesu ya yi masa, dukansu suka cika da mamaki.
21 When Yeshua had crossed back over in the boat to the other side, a great multitude was gathered to him; and he was by the sea.
Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun.
22 Behold, one of the rulers of the synagogue, Jairus by name, came; and seeing him, he fell at his feet
Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa.
23 and begged him much, saying, “My little daughter is at the point of death. Please come and lay your hands on her, that she may be made healthy, and live.”
Ya yi ta rokonsa, yana cewa, “Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu.”
24 He went with him, and a great multitude followed him, and they pressed upon him on all sides.
Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi.
25 A certain woman who had a discharge of blood for twelve years,
Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu.
26 and had suffered many things by many physicians, and had spent all that she had, and was no better, but rather grew worse,
Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi.
27 having heard the things concerning Yeshua, came up behind him in the crowd and touched his clothes.
Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa.
28 For she said, “If I just touch his clothes, I will be made well.”
Domin ta ce “Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke.”
29 Immediately the flow of her blood was dried up, and she felt in her body that she was healed of her affliction.
Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta.
30 Immediately Yeshua, perceiving in himself that the power had gone out from him, turned around in the crowd and asked, “Who touched my clothes?”
Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce “wanene ya taba rigata?”
31 His disciples said to him, “You see the multitude pressing against you, and you say, ‘Who touched me?’”
Almajiransa suka ce, “a cikin wannan taron mutane da yawa ka ce wanene ya taba ni?”
32 He looked around to see her who had done this thing.
Amma Yesu ya waiga ya ga ko wanene ya taba shi.
33 But the woman, fearing and trembling, knowing what had been done to her, came and fell down before him, and told him all the truth.
Matar ta san abin da ya faru sai ta zo cikin tsoro da rawar jiki ta durkusa a gaban Yesu ta fada masa gaskiya.
34 He said to her, “Daughter, your faith has made you well. Go in peace, and be cured of your disease.”
Sai ya ce da ita, “Diya bangaskiyarki ta warkar da ke, ki tafi lafiya kin sami warkewa daga cutarki”.
35 While he was still speaking, people came from the synagogue ruler’s house, saying, “Your daughter is dead. Why bother the Rabbi any more?”
Sa'adda ya ke magana da ita sai ga mutane daga gidan shugaban majami'a suka ce “Diyarka ta mutu me ya sa za ka dami malam?”
36 But Yeshua, when he heard the message spoken, immediately said to the ruler of the synagogue, “Don’t be afraid, only believe.”
Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, “kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai.”
37 He allowed no one to follow him except Peter, Jacob, and Yochanan the brother of Jacob.
Bai bari kowa ya kasance tare da shi ba sai Bitrus da Yakubu da Yahaya dan'uwan Yakubu.
38 He came to the synagogue ruler’s house, and he saw an uproar, weeping, and great wailing.
Suka zo gidan shugaban majami'ar ya ga mutane suna bakin ciki, suna kuka sosai.
39 When he had entered in, he said to them, “Why do you make an uproar and weep? The child is not dead, but is asleep.”
Sa'adda ya shiga gidan ya ce da mutane “Me ya sa kuke damuwa da kuka?” Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi.
40 They ridiculed him. But he, having put them all out, took the father of the child, her mother, and those who were with him, and went in where the child was lying.
Sai su kayi masa dariya. Amma ya fitar da su waje su duka. Ya kira baban yarinyar da mamar ta da wadansu da ke tare da shi su ka shiga wurin da yarinyar ta ke.
41 Taking the child by the hand, he said to her, “Talitha cumi!” which means, being interpreted, “Girl, I tell you, get up!”
Ya kama hannun yarinyar ya ce da ita “Tilatha koum” wato yarinya na ce ki tashi”
42 Immediately the girl rose up and walked, for she was twelve years old. They were amazed with great amazement.
Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya [gama shekarun ta sun kai goma sha biyu]. Nan da nan mutanen suka yi mamaki kwarai da gaske.
43 He strictly ordered them that no one should know this, and commanded that something should be given to her to eat.
Ya ummurce su da gaske kada kowa ya sani. Ya ce da su su ba ta abinci ta ci.

< Mark 5 >