< Ezekiel 25 >

1 And the word of the Lord came to me, saying:
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Son of man, set your face against the sons of Ammon, and you shall prophesy about them.
“Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu.
3 And you shall say to the sons of Ammon: Listen to the word of the Lord God: Thus says the Lord God: Because you have said, ‘Well, well!’ over my sanctuary, when it was profaned, and over the land of Israel, when it was desolated, and over the house of Judah, when they were led into captivity,
Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun ce “Yauwa” a kan wuri mai tsarkina sa’ad da aka ƙazantar da shi da kuma a kan ƙasar Isra’ila sa’ad da aka mai da ita kufai da lokacin da aka kai mutanen Yahuda bautar talala,
4 therefore, I will deliver you to the sons of the East, as an inheritance. And they will arrange their fences within you, and they will place their tents within you. They will eat your crops, and they will drink your milk.
saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku.
5 And I will make Rabbah into the habitation of camels, and the sons of Ammon into the resting place of cattle. And you shall know that I am the Lord.
Zan mai da Rabba wurin kiwo don raƙuma, Ammon kuma wurin hutu don tumaki. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
6 For thus says the Lord God: Because you have clapped your hands and stomped your foot, and have rejoiced with all your heart against the land of Israel,
Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila,
7 therefore, behold, I will extend my hand over you, and I will deliver you as a spoil of the Gentiles. And I will destroy you from the peoples, and I will perish you from the lands, and I will crush you. And you shall know that I am the Lord.
saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’”
8 Thus says the Lord God: Because Moab and Seir have said, ‘Behold, the house of Judah is like all the Gentiles!’
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,”
9 therefore, behold, I will open the shoulder of Moab from the cities, from his cities, I say, and from his borders, the famous cities of the land of Beth-Jesimoth, and Baal-meon, and Kiriathaim,
saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar.
10 with the sons of Ammon, to the sons of the East, and I will give it to them as an inheritance, so that there may no longer be a remembrance of the sons of Ammon among the Gentiles.
Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai;
11 And I will execute judgments in Moab. And they shall know that I am the Lord.
zan hukunta Mowabawa. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.’”
12 Thus says the Lord God: Because Idumea has taken vengeance, so as to vindicate herself against the sons of Judah, and has sinned grievously, and has sought revenge against them,
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Edom ya ɗauki wa kanta fansa a kan gida Yahuda, ta yi babban laifi ta wurin yin haka,
13 therefore, thus says the Lord God: I will extend my hand over Idumea, and I will take from it both man and beast, and I will make it desolate from the south. And those who are in Dedan will fall by the sword.
saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan miƙa hannuna a kan Edom in kashe mutanenta da dabbobinsu. Zan sa ta zama kufai, kuma tun daga Teman har zuwa Dedan za a kashe su da takobi.
14 And I will issue my vengeance upon Idumea, by the hand of my people, Israel. And they shall act in Idumea in accord with my wrath and my fury. And they shall know my vengeance, says the Lord God.
Zan ɗau fansa a kan Edom ta hannun mutanena Isra’ila, za su kuwa hukunta Edom bisa ga fushina da hasalata; za su san sakayyata, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
15 Thus says the Lord God: Because the Philistines have taken vengeance, and have revenged themselves with all their soul, destroying, and fulfilling ancient hostilities,
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Filistiyawa sun yi sakayya, suka ɗauki fansa da mugunta a zukatansu, da kuma daɗaɗɗen ƙiyayya sun nemi su hallaka Yahuda,
16 because of this, thus says the Lord God: Behold, I will extend my hand over the Philistines, and I will destroy those who destroy, and I will perish the remnant of the maritime regions.
saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da miƙa hannuna a kan Filistiyawa, zan kuwa datse Keretawa in kuma hallaka waɗanda suka rage a bakin teku.
17 And I will execute great vengeance against them, reproving them in fury. And they shall know that I am the Lord, when I will send my vengeance upon them.”
Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani cikin hasalata. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.’”

< Ezekiel 25 >