< 1 Chronicles 23 >

1 Then David, being old and full of days, appointed his son Solomon as king over Israel.
Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila.
2 And he gathered together all the leaders of Israel, with the priests as well as the Levites.
Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa.
3 And the Levites were numbered from the age of thirty years and upward. And there were found thirty-eight thousand men.
Aka ƙidaya Lawiyawan da suke’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas.
4 Of these, twenty-four thousand were chosen and distributed to the ministry of the house of the Lord. Then six thousand were overseers and judges.
Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.
5 Moreover, four thousand were porters. And the same number were the singers of psalms to the Lord, with the musical instruments which he had made for the music.
Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”
6 And David distributed them into courses according to the sons of Levi, specifically, Gershom, and Kohath, and Merari.
Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.
7 The sons of Gershom: Ladan and Shimei.
Na Gershonawa, Ladan da Shimeyi.
8 The sons of Ladan: the leader Jahiel, and Zetham, and Joel, three.
’Ya’yan Ladan maza su ne, Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.
9 The sons of Shimei: Shelomoth, and Haziel, and Haran, three. These were the leaders of the families of Ladan.
’Ya’yan Shimeyi maza su ne, Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka. Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.
10 Then the sons of Shimei: Jahath, and Zizah, and Jeush, and Beriah. These were the sons of Shimei, four.
’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne, Yahat, Zina, Yewush da Beriya. Waɗannan su ne’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.
11 Now Jahath was first, Zizah second, but Jeush and Beriah did not have many sons, and for this reason they were reckoned as one family and one house.
Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.
12 The sons of Kohath: Amram and Izhar, Hebron and Uzziel, four.
’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.
13 The sons of Amram: Aaron and Moses. Now Aaron was separated so that he might minister in the Holy of Holies, he and his sons forever, and so that he might burn incense to the Lord, according to his rite, and so that he might bless his name in perpetuity.
’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.
14 The sons of Moses, the man of God, were also numbered in the tribe of Levi.
An ƙidaya aka kuma haɗa’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.
15 The sons of Moses: Gershom and Eliezer.
’Ya’yan Musa maza su ne, Gershom da Eliyezer.
16 The sons of Gershom: Shebuel the first.
Zuriyar Gershom su ne, Shebuwel ne ɗan fari.
17 Now the sons of Eliezer were Rehabiah the first. And there were no other sons for Eliezer. But the sons of Rehabiah were multiplied exceedingly.
Zuriyar Eliyezer su ne, Rehabiya ne ɗan fari. Eliyezer ba shi da waɗansu’ya’ya maza, amma’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.
18 The sons of Izhar: Shelomith the first.
’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari.
19 The sons of Hebron: Jeriah the first, Amariah the second, Jahaziel the third, Jekameam the fourth.
’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
20 The sons of Uzziel: Micah the first, Isshiah the second.
’Ya’yan Uzziyel maza su ne, Mika na fari da Isshiya na biyu.
21 The sons of Merari: Mahli and Mushi. The sons of Mahli: Eleazar and Kish.
’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi.’Ya’yan Mali maza su ne, Eleyazar da Kish.
22 Then Eleazar died, and had no sons, but only daughters. And so the sons of Kish, their brothers, married them.
Eleyazar ya mutu ba’ya’yan maza, yana da’ya’ya mata ne kawai.’Yan’uwansu,’ya’yan Kish maza, suka aure su.
23 The sons of Mushi: Mahli, and Eder, and Jeremoth, three.
’Ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.
24 These are the sons of Levi, in their kindred and families, leaders in turns, and the number of each of the heads who were doing the works of the ministry of the house of the Lord, from twenty years of age and upward.
Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.
25 For David said: “The Lord, the God of Israel, has given rest to his people, and a habitation in Jerusalem even unto eternity.
Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada,
26 Neither shall it be the office of the Levites any more to carry the tabernacle with all its equipment for use in the ministry.”
Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.”
27 Also, according to the last precepts of David, the sons of Levi shall be counted by number from twenty years of age and upward.
Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga’yan shekara ashirin ko fiye.
28 And they shall be under the hand of the sons of Aaron, in the care of the house of the Lord, in the vestibule, and in the chambers, and in the place of purification, and in the sanctuary, and in all the works of the ministry of the temple of the Lord.
Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah.
29 But the priests shall be over the bread of the presence, and the sacrifice of fine wheat flour, and the unleavened cakes, and the frying pan, and the roasting, and over every weight and measure.
Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.
30 Yet truly, the Levites shall stand to confess and to sing to the Lord, in the morning, and similarly in the evening,
Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma
31 as much in the oblation of the holocausts of the Lord, as in the Sabbaths and new moons and other solemnities, according to the number and ceremonies for each and every matter, perpetually before the Lord.
da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.
32 And let them keep the observances of the tabernacle of the covenant, and the rituals of the sanctuary, and the observance of the sons of Aaron, their brothers, so that they may minister in the house of the Lord.
A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.

< 1 Chronicles 23 >