< 2 Corintios 6 >

1 Y ASÍ [nosotros], [como] ayudadores juntamente [con él], [os] exhortamos también á que no recibáis en vano la gracia de Dios,
A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza.
2 (Porque dice: En tiempo aceptable te he oído, y en día de salud te he socorrido: he aquí ahora el tiempo aceptable; he aquí ahora el día de salud: )
Gama ya ce, “A lokacin samun alherina, na ji ka, a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.” Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.
3 No dando á nadie ningún escándalo, porque el ministerio nuestro no sea vituperado:
Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi.
4 Antes habiéndonos en todas cosas como ministros de Dios, en mucha paciencia, en tribulaciones, en necesidades, en angustias;
A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu.
5 En azotes, en cárceles, en alborotos, en trabajos, en vigilias, en ayunos;
Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa.
6 En castidad, en ciencia, en longanimidad, en bondad, en Espíritu Santo, en amor no fingido;
Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya,
7 En palabra de verdad, en potencia de Dios, en armas de justicia á diestro y á siniestro;
da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu,
8 Por honra y por deshonra, por infamia y por buena fama; como engañadores, mas hombres de verdad;
ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya,
9 Como ignorados, mas conocidos; como muriendo, mas he aquí vivimos; como castigados, mas no muertos;
mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba,
10 Como doloridos, mas siempre gozosos; como pobres, mas enriqueciendo á muchos; como no teniendo nada, mas poseyéndolo todo.
cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
11 Nuestra boca está abierta á vosotros, oh Corintios: nuestro corazón es ensanchado.
Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai.
12 No estáis estrechos en nosotros, mas estáis estrechos en vuestras propias entrañas.
Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana.
13 Pues, para corresponder al propio modo (como á hijos hablo), ensanchaos también vosotros.
A wannan zance kam, ina magana da ku kamar’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.
14 No os juntéis en yugo con los infieles: porque ¿qué compañía tiene la justicia con la injusticia? ¿y qué comunión la luz con las tinieblas?
Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?
15 ¿Y qué concordia Cristo con Belial? ¿ó qué parte el fiel con el infiel?
Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi?
16 ¿Y qué concierto el templo de Dios con los ídolos? porque vosotros sois el templo del Dios viviente, como Dios dijo: Habitaré y andaré en ellos; y seré el Dios de ellos, y ellos serán mi pueblo.
Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.”
17 Por lo cual salid de en medio de ellos, y apartaos, dice el Señor, y no toquéis lo inmundo; y yo os recibiré,
Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.”
18 Y seré á vosotros Padre, y vosotros me seréis á mí hijos é hijas, dice el Señor Todopoderoso.
Kuma, “Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama’ya’yana, maza da mata, in ji Ubangiji Maɗaukaki.”

< 2 Corintios 6 >