< Luka 20 >

1 In zgodí se enega tistih dnî, ko je učil ljudstvo v tempeljnu in je oznanjeval evangelj, pridejo véliki duhovni in pismarji s starešinami,
Ana nan wata rana, Yesu yana kan koyarwa a haikali da wa'azin bishara, sai shugaban firistoci da marubuta suka zo wurinsa da dattawa.
2 In rekó mu, govoreč: Povej nam, s kakošno oblastjo to delaš, ali kdo ti je dal to oblast?
Suka yi magana, su na ce masa, “Gaya mana da wanne iko ne ka ke yin wadannan abubuwan? Ko wanene ya baka wannan ikon?”
3 Odgovarjajoč pa, reče jim: Vprašal bom tudi jaz vas eno besedo, in povejte mi:
Ya amsa sai ya ce masu, “Ni ma zan yi maku tambaya. Gaya mani game
4 Krst Janezov je li bil z neba, ali od ljudî?
da baptisman Yahaya. Daga sama take ko kuwa daga mutane ne?”
5 A oni so pomišljevali v sebi govoreč: Če rečemo: Z neba, poreče: Za kaj mu torej niste verovali?
Sai suka yi mahawara da junansu, suna cewa, “In mun ce, 'Daga sama,' zai ce, 'To don me ba ku ba da gaskiya gareshi ba?'
6 Če pa rečemo: Od ljudî, vse ljudstvo nas bo kamenjalo: kajti prepričano je, da je bil Janez prerok.
Amma in mun ce, 'Daga mutane ne,' dukan mutane za su jejjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata a ransu Yahaya annabi ne.”
7 Ter odgovoré, da ne vedó, odkod.
Sai suka amsa cewa ba su san ko daga ina ne take ba.
8 Pa jim Jezus reče: Tudi jaz ne bom povedal vam, s kakošno oblastjo to delam.
Yesu yace masu, “To haka ni ma ba zan gaya maku ko da wanne iko nake yin wadannan abubuwan ba.”
9 A ljudstvu začne praviti tole priliko: Neki človek je zasadil vinograd, in dal ga je vinogradnikom v najem, in odpotoval je na veliko časa.
Ya gaya wa mutane wannan misali, “Wani mutum ya dasa gonar inabi, ya ba wadansu manoma jinginarta, sai ya tafi wata kasa har ya dade.
10 In o svojem času pošlje k vinogradnikom hlapca, naj mu dadó od sadú vinogradovega; a vinogradniki ga pretepó, in odpošljejo praznega.
Da lokacin girbi ya yi sai ya aiki wani bawansa zuwa wurin manoman, saboda su bashi daga cikin anfanin gonar. Amma manoman suka doke shi, sai suka kore shi hannu wofi.
11 In zopet pošlje drugega hlapca; a oni tudi tega pretepó, in zasramoté, in odpošljejo praznega.
Ya aike wani bawa kuma sai suka daddoke shi, suka kunyatar da shi, suka kore shi hannu wofi.
12 In zopet pošlje tretjega: in oni tudi tega ranijo, in izženó.
Ya kuma sake aike na uku suka yi masa rauni, suka jefar da shi a waje.
13 Tedaj reče gospodar vinograda: Kaj bom storil? Poslal bom sina svojega ljubljenega; ko bodo tega videli, ne mara, da se bodo bali.
Sai mai gonar inabin ya ce, 'Me zan yi? Zan aiki kaunattacen dana. Watakila zasu ba shi daraja.'
14 Ko ga pa vinogradniki ugledajo, posvetovali so se med seboj, govoreč: Ta je dedič; pridite, ubijmo ga, da bo dedovina naša.
Amma sa'adda manoman suka gan shi, suka yi shawara a tsakaninsu, cewa, 'Wannan ne magajin. Bari mu kashe shi, saboda gadon ya zama namu.'
15 In vržejo ga ven iz vinograda, in ubijejo. Kaj jim bo torej gospodar vinograda storil?
Suka jefar da shi waje daga gonar, suka kashe shi. Menene ubangijin gonar inabin zai yi da su?
16 Prišel bo, in pogubil bo vinogradnike té, in dal bo vinograd drugim. Ko so pa to slišali, rekó: Bog ne daj!
Zai zo ya halakar da wadannan manoma, sai ya ba wadansu gonar.” Da suka ji wannan, suka ce, “Allah ya sawake!”
17 On pa pogledavši na-nje, reče: Kaj je torej to, kar je pisano: "Kamen, kterega so zidarji zavrgli, on je postal glava oglu?"
Amma Yesu ya kalle su, sai yace, “Menene ma'anar wannan nassi? 'Dutsen da magina suka ki, an mayar da shi kan kusurwa'?
18 Vsak, kdor pade na ta kamen, razbil se bo; na kogar pa on pade, razdrobil ga bo.
Duk wanda ya fadi kan dutsen zai farfashe. Amma duk wanda dutsen ya fadi a kansa, zai rugurguza shi.”
19 In iskali so véliki duhovni in pismarji, da bi položili na-nj roke v ta čas; ali zbojé se ljudstva: kajti spoznali so, da je za-nje povedal to priliko.
Sai marubutan da manyan firistocin suka so su kama shi a wannan sa'a, domin sun sani ya yi wannan misali a kansu ne. Amma sun ji tsoron mutane.
20 In pazeč na-nj, pošljejo prežuhe, kteri naj bi se hlinili pravične, da bi ga vjeli v besedi in ga po tem izročili gosposki in oblasti poglavarjevej.
Suna fakonsa, suka aiki magewaya, wadanda suke kamar masu adalci, saboda su sami kuskure cikin maganarsa, don su mika shi ga hukumci da kuma ikon gwamna.
21 In vprašajo ga, govoreč: Učenik, vémo, da prav govoriš in učiš, in ne gledaš na lice, nego v resnici pot Božjo učiš:
Suka tambaye shi, cewa, “Malam, mun sani da cewa kana fada da koyar da abin ke daidai, kuma ba wanda yake cusa maka ra'ayi, amma kana koyar da gaskiya game da hanyar Allah.
22 Smemo li cesarju davek dajati, ali ne?
Wai shin doka ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”
23 Spoznavši pa njih zvijačo, reče jim: Kaj me izkušate?
Amma Yesu ya gane makircinsu, sai ya ce masu,
24 Pokažite denar. Čegavo podobo ima in napis? Odgovarjajoč pa rekó: Cesarjevo.
“Nuna mani dinari. Sifar wanene da kuma rubutun wanene akan sa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.”
25 A on jim reče: Dajte tedaj, kar je cesarjevega, cesarju, a kar je Božjega, Bogu.
Sai ya ce masu, “To sai ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma ba Allah, abin da ke na Allah.”
26 In niso mogli besede njegove zavreči pred ljudstvom; in začudijo se odgovoru njegovemu, in umolknejo.
Marubutan da manyan firistocin ba su sami abin zargi cikin maganarsa, a gaban mutane ba. Suka yi mamakin amsar sa, ba su kuma ce komai ba.
27 Pristopivši pa nekteri od Saducejev, kteri pravijo, da ni vstajanja, vprašajo ga,
Sa'adda wadansu Sadukiyawa suka zo wurinsa, wadan da suka ce babu tashin mattatu,
28 Govoreč: Učenik! Mojzes nam je napisal, da če komu umrè brat, kteri ima ženo, in on brez otrók umrè, naj vzeme brat njegov ženo, in vzbudí seme bratu svojemu.
suka tambaye shi, cewa, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, mai mace kuma ba shi da yaro, sai dan'uwansa ya auri matar, ya samar wa dan'uwansa yaro.
29 Bilo je pa sedem bratov. In prvi je vzel ženo, in umrl je brez otrók;
Akwai 'yan'uwa guda bakwai kuma na farin ya yi aure, sai ya mutu babu da,
30 In vzel je ženo drugi, in tudi ta je umrl brez otrók.
haka ma na biyun.
31 In vzel jo je tretji; in tako tudi vseh sedem: in niso pustili otrók, in pomrli so.
Na ukun ya aure ta, haka nan na bakwai ma bai bar yaya ba, har suka mutu.
32 A naposled za vsemi umrla je tudi žena.
Daga baya sai matar ma ta mutu.
33 O vstajanji torej, čegava od njih bo žena! kajti sedem jo jih je imelo za ženo.
To a ranar tashin mattatu, matar wa za ta zama? Domin duka bakwai din sun aure ta.”
34 In odgovarjajoč, reče jim Jezus: Sinovi tega sveta se ženijo in možé; (aiōn g165)
Yesu ya ce masu, “'Ya'yan duniyan nan suna aure, ana kuma ba da su ga aure. (aiōn g165)
35 Ali ti, kteri bodo vredni, da zadobé drugi svet, in da vstanejo od mrtvih, ne bodo se ženili ne možile, (aiōn g165)
Amma wadanda aka ga cancantarsu a waccan tsara, sun isa su sami tashin mattatu, ba za suyi aure ko a aurar da su ba. (aiōn g165)
36 Ker tudi umreti ne morejo več: enaki so namreč angeljem, in sinovi so Božji, ko so sinovi vstajanja.
Gama ba za su mutu kuma ba, domin suna daidai da mala'iku kuma su 'ya'yan Allah ne, da shike su 'ya'yan tashin matattu ne.
37 Da pa mrtvi vstajajo, pokazal je tudi Mojzes pri grmu, ko imenuje Gospoda "Boga Abrahamovega in Boga Izakovega in Boga Jakobovega."
Amma batun tashi matattu, ko Musa ma ya nuna wannan, a cikin jeji, inda ya kira Ubangiji, Allah na Ibrahim da kuma Allah na Ishaku da Allah na Yakubu.
38 Bog pa ni Bog mrtvih, nego živih; kajti njemu so vsi živi.
Yanzu shi ba Allahn matattu ba ne, amma na masu rai, saboda duka suna raye a wurinsa.”
39 Odgovarjajoč pa nekterí od pismarjev, rekó: Učenik, dobro si povedal.
Wadansu marubuta suka amsa, “Malam, ka amsa da kyau.”
40 In nič več ga niso smeli vpraševati.
Gama ba su sake yi masa wadansu tambayoyi ba.
41 Reče jim pa: Kako pravijo, da je Kristus sin Davidov?
Yesu ya ce masu, “Yaya suke cewa Almasihu dan Dauda ne?
42 In sam David pravi v bukvah psalmov: "Rekel je Gospod gospodu mojemu: Sédi meni na desno,
Gama Dauda da kansa ya ce a cikin littafin Zabura, Ubangiji ya ce wa Ubangiji na, 'Zauna a hannun dama na,
43 Dokler ne položim sovražnikov tvojih nogam tvojim za podnožje."
sai na maida makiyanka a karkashin tafin sawunka.'
44 David ga torej imenuje Gospoda, in kako je sin njegov?
Dauda ya kira Kristi 'Ubangiji', to ta yaya ya zama dan Dauda?”
45 A ko ga je vse ljudstvo poslušalo, reče učencem svojim:
Dukan mutane suna ji ya ce wa almajiransa,
46 Varujte se pismarjev, kteri hočejo v dolgih oblačilih hoditi, in ljubijo pozdrave po ulicah, in prve stole po shajališčih, in prve prostore na gostijah.
“Ku yi hankali da marubuta, wadanda suna son tafiya da manyan riguna, suna kuma son a gaishe su a cikin kasuwanni, da mayan wuraren zama a cikin majami'u, da kuma manyan wurare a wurin bukukkuwa.
47 Kteri požirajo hiše vdovam, in na videz dolgo molijo: ti bodo prejeli ostrejo sodbo.
Suna kuma kwace wa gwamraye gidaje, suna kuma badda kama ta wurin yin doguwar addu'a. Wadannan za su sha hukumci mai girma.”

< Luka 20 >