< Kološanom 3 >

1 Če ste bili torej vred zbujeni s Kristusom, iščite, kar je gori, kjer sedí Kristus na desnici Božji.
Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah.
2 V mislih imejte, kar je gori, ne kar je na zemlji;
Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba.
3 Kajti umrli ste, in življenje vaše je skrito s Kristusom v Bogu;
Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah.
4 Kader se prikaže Kristus, življenje naše, tedaj se prikažete tudi vi v slavi z njim.
Sa'anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa'anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa.
5 Morite torej ude svoje zemeljske, kurbarijo, nečistost, strast, hudo poželenje in lakomnost, katera je malikovanje;
Ku kashe sha'awacce-sha'awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha'awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka.
6 Po čemer prihaja jeza Božja nad nepokorščine sinove,
Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya.
7 Med katerimi ste tudi vi živeli nekdaj, ko ste bivali med njimi;
A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu.
8 Sedaj pa odložite tudi vi vse, jezo, srd, hudobnost, obrekovanje, nesramno besedovanje iz svojih ust.
Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku.
9 Ne lagajte med seboj, slecite starega človeka z dejanji njegovimi,
Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa,
10 In oblecite novega, ponovljenega v spoznanje po podobi njega, ki ga je vstvaril;
kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi.
11 Kjer ni Grka in Juda, obreze in neobreze, tujca, Scita, hlapca, svobodnjaka; nego vse in v vseh Kristus.
A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka.
12 Oblecite torej, ker ste izvoljeni in ljubljeni sveti Božji, milosrčnost, blagovoljnost, ponižnost, krotkost, potrpežljivost;
A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri.
13 Da se prenašate med seboj, in si odpuščate, če ima kdo tožbo do koga, kakor je tudi Kristus odpustil vam, tako tudi vi;
Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku.
14 Poleg vsega tega pa ljubezen, katera je popolnosti vez.
Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla.
15 In mir Božji naj vlada v srcih vaših, v katerega ste bili tudi poklicani v enem telesu; in hvaležni bodite!
Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya.
16 Beseda Kristusova prebivaj v vas obilo, v vsej modrosti; učite in opominjajte se med seboj s psalmi in hvalospevi in pesmami duhovnimi, v milosti pójte v srci svojem Gospodu.
Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah.
17 In vse, kar počenjate v besedi in dejanji, vse v imenu Gospoda Jezusa, zahvaljujoč se Bogu in očetu po njem.
Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
18 Žene, bodite pokorne svojim možem, kakor se spobodi v Gospodu.
Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji.
19 Možje, ljubite žene svoje in ne hudujte se nad njimi.
Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu.
20 Otroci, bodite poslušni roditeljem v vsem, kajti to je po volji Gospodu.
Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai.
21 Očetje, ne dražite otrók svojih, da ne bodo malosrčni.
Ku Ubanni, kada ku cakuni 'ya'yanku domin kada su karaya.
22 Hlapci, bodite poslušni v vsem gospodom po mesu, ne po okoslužnosti kakor ljudem ugajajoč, nego v preprostosti srca, boječ se Boga.
Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji.
23 In vse kar storite, delajte iz duše, kakor Gospodu, in ne ljudém;
Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba.
24 Vedóč, da od Kristusa dobóte zato povračilo dedščine; kajti Gospodu Kristusu hlapčujete;
Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa.
25 Krivični pa bode prejel, kar je krivičnega storil; in ni ga licegledja.
Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.

< Kološanom 3 >