< Јудина 1 >

1 Од Јуде, Исуса Христа слуге, а брата Јаковљевог, званима, који су освећени Богом Оцем и одржани Исусом Христом:
Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi:
2 Милост и мир и љубав да вам се умножи.
bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku.
3 Љубазни! Старајући се једнако да вам пишем за опште ваше спасење, би ми потребно да вам пишем молећи да се борите за праведну веру, која је једанпут дана светима.
Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari.
4 Јер се увукоше неки безбожни људи, који су давно одређени на ово суђење, и Бога нашег благодат претварају у нечистоту, и јединог Господара Бога и Господа нашег Исуса Христа одричу се.
Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu.
5 Али ћу вам напоменути, кад и ви знате ово једанпут, да Господ избави народ из земље мисирске, потом погуби оне који не вероваше.
Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba.
6 И анђеле који не држаше своје старешинство него оставише свој стан чува у вечним оковима под мраком за суд великог дана. (aïdios g126)
Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. (aïdios g126)
7 Као што Содом и Гомор, и околни њихови градови, који су се прокурвали онако као и они, и ходили за другим месом, поставише се углед и муче се у вечном огњу: (aiōnios g166)
Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka. (aiōnios g166)
8 Тако дакле и ови што сањајући тело погане, а поглаварства се одричу, и на славу хуле.
Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka.
9 А Михаило Арханђел, кад се препираше с ђаволом и говораше за Мојсијево тело, не смеше проклети суд да изговори, него рече: Господ нека ти запрети.
Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, “Bari Ubangiji ya tsauta maka!''
10 А ови хуле на оно што не знаду; а шта знаду по природи као неразумна животиња, у оном се распадају.
Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan.
11 Тешко њима! Јер путем Каиновим пођоше и у превару Валамове плате падоше, и у буни Корејевој изгибоше.
Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora.
12 Ово су они што погане ваше милостиње једући с вама без страха и гојећи се; облаци безводни, које ветрови разносе; јесенска дрвета неродљива, која су двапут умрла, и из корена ишчупана;
Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa.
13 Бесни валови морски, који се пене својим срамотама, звезде лажне, којима се чува мрак вечне таме. (aiōn g165)
Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada. (aiōn g165)
14 Али и за овакве пророкова Енох, седми од Адама, говорећи: Гле, иде Господ с хиљадама светих анђела својих
Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, “Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai.
15 Да учини суд свима, и да покара све безбожнике за сва њихова безбожна дела којима безбожност чинише, и за све ружне речи њихове које безбожни грешници говорише на Њ.
Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi.”
16 Ово су незадовољни викачи, који по жељама својим живе, и уста њихова говоре поносите речи, и за добитак гледају ко је ко.
Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu.
17 А ви, љубазни, опомињите се речи које напред казаше апостоли Господа нашег Исуса Христа,
Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da.
18 Јер вам казаше да ће у последње време постати ругачи, који ће ходити по својим жељама и безбожностима.
Sun ce maku, “A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada,”
19 Ово су они што се одвајају (од јединости вере), и јесу телесни, који духа немају.
Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu.
20 А ви, љубазни, назиђујте се својом светом вером, и молите се Богу Духом Светим.
Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki.
21 И сами себе држите у љубави Божијој, чекајући милост Господа нашег Исуса Христа за живот вечни. (aiōnios g166)
Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada. (aiōnios g166)
22 И тако разликујући једне милујте.
Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta.
23 А једне страхом избављајте и из огња вадите; а карајте са страхом, мрзећи и на хаљину опогањену од тела.
Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma.
24 А Ономе који вас може сачувати без греха и без мане, и поставити праве пред славом својом у радости,
Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa,
25 Једином премудром Богу и Спасу нашем, кроз Исуса Христа Господа нашег, слава и величанство, држава и власт пре свију векова и сад и у све векове. Амин. (aiōn g165)
zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin. (aiōn g165)

< Јудина 1 >