< Јеврејима 9 >

1 Тако и први завет имаше правду богомољства и светињу земаљску.
Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.
2 Јер скинија беше начињена прва, у којој беше свећњак и трпеза и постављени хлебови, што се зове светиња.
An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.
3 А за другим завесом беше скинија, која се зове светиња над светињама,
Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,
4 Која имаше златну кадионицу, и ковчег завета окован свуда златом, у коме беше златан суд с маном, и палица Аронова, која се беше омладила, и плоче завета.
wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.
5 А више њега беху херувими славе, који осењаваху олтар; о чему се не може сад говорити редом.
A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.
6 А кад ово беше тако уређено, улажаху свештеници свагда у прву скинију и савршиваху службу Божију.
Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.
7 А у другу улажаше једном у години сам поглавар свештенички, не без крви, коју приноси за себе и за народна незнања.
Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani.
8 Овим показиваше Дух Свети да се још није отворио пут светих, докле прва скинија стоји;
Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye.
9 Која остаде прилика за садашње време, у које се приносе дари и жртве, и не могу да се сврше по савести оног који служи.
Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.
10 Осим у јелима и пићима, и различном умивању и правдању тела, које је постављено до времена поправљења.
Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.
11 Али дошавши Христос, поглавар свештенички добара која ће доћи, кроз бољу и савршенију скинију, која није руком грађена, то јест, није овог створења,
Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.
12 Ни с крвљу јарчијом, нити телећом, него кроз своју крв уђе једном у светињу, и нађе вечни откуп. (aiōnios g166)
Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. (aiōnios g166)
13 Јер ако крв јунчија и јарчија, и пепео јуничин, покропивши њом опогањене, освећује на телесну чистоту;
In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,
14 А камоли неће крв Христа, који Духом Светим себе принесе без кривице Богу, очистити савест нашу од мртвих дела, да служимо Богу Живом и Истинитом? (aiōnios g166)
balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai! (aiōnios g166)
15 И зато је новом завету посредник, да кроз смрт, која би за откуп од преступака у првом завету, обећање вечног наследства приме звани. (aiōnios g166)
Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko. (aiōnios g166)
16 Јер где је завет ваља да буде и смрт оног који чини завет.
Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,
17 Јер је завет по смрти потврђен: будући да нема никакве силе док је жив онај који га је начинио.
domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.
18 Јер ни први није утврђен без крви.
Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.
19 Јер кад Мојсије изговори све заповести по закону свом народу, онда узе крви јарчије и телеће, с водом и вуном црвеном и исопом, те покропи и књигу и сав народ.
Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.
20 Говорећи: Ово је крв завета који Бог начини с вама.
Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”
21 А тако и скинију и све судове службене покропи крвљу.
Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima.
22 И готово све се крвљу чисти по закону, и без проливања крви не бива опроштење.
Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
23 Тако је требало да се обличја небеских овима чисте, а сама небеска бољим жртвама од ових.
Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.
24 Јер Христос не уђе у рукотворену светињу, која је прилика праве, него у само небо, да се покаже сад пред лицем Божијим за нас;
Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.
25 Нити да много пута приноси себе, као што поглавар свештенички улази у светињу сваке године с крвљу туђом:
Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba.
26 Иначе би Он морао много пута страдати од постања света; а сад једном на свршетку века јави се да својом жртвом сатре грех. (aiōn g165)
Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. (aiōn g165)
27 И као што је људима одређено једном умрети, а потом суд:
Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,
28 Тако се и Христос једном принесе, да узме многих грехе; а другом ће се јавити без греха на спасење онима који Га чекају.
haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

< Јеврејима 9 >