< Romanos 10 >

1 Irmãos, o bom desejo do meu coração e a oração a Deus por Israel, é para sua salvação.
'Yan'uwana, muradin zuciyata da dukkan addu'oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton.
2 Porque lhes dou testemunho de que têm zelo de Deus, mas não com entendimento.
Domin na shaida game da su cewa suna da kwazo game da Allah, amma ba a kan sani ba.
3 Porque, não conhecendo a justiça de Deus, e procurando estabelecer a sua própria justiça, não se sujeitaram à justiça de Deus.
Don, ba su da sani akan adalcin Allah, suna kokarin tabbatar da adalcin kansu. Ba su bada kan su ga adalcin Allah ba.
4 Porque o fim da lei é Cristo para justiça de todo aquele que crê.
Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata.
5 Porque Moisés descreve a justiça que é pela lei, dizendo: O homem que fizer estas coisas viverá por elas.
Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari'a: ''mutumin da ya aikata adalcin shari'a, zai rayu ta wurin wannan adalcin.''
6 Mas a justiça que é pela fé diz assim: Não digas em teu coração: Quem subirá ao céu? (isto é, a trazer do alto a Cristo)
Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, ''Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?''(don ya sauko da Almasihu kasa).
7 Ou, quem descerá ao abismo? (isto é, a tornar a trazer, dos mortos a Christo). (Abyssos g12)
Kada ku ce, ''Wa zai gangara zuwa kasa?'' (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu). (Abyssos g12)
8 Mas que diz? A palavra está junto de ti, na tua boca e no teu coração; esta é a palavra da fé, que pregamos,
Amma me yake cewa? “kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka.” Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa.
9 A saber: Se com a tua boca confessares ao Senhor Jesus, e em teu coração creres que Deus o resuscitou dos mortos, serás salvo.
Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.
10 Porque com o coração se crê para a justiça, e com a boca se faz confissão para a salvação.
Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto.
11 Porque a escritura diz: Todo aquele que nele crer não será confundido.
Don nassi na cewa, ''Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba,''
12 Porque não há diferença entre judeu e grego; porque um mesmo é o Senhor de todos os que o invocam.
Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi.
13 Porque todo aquele que invocar o nome do Senhor será salvo.
Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto.
14 Como pois invocarão aquele em quem não creram? e como crerão naquele de quem não ouviram? e como ouvirão, se não há quem pregue?
To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba?
15 E como pregarão, se não forem enviados? como está escrito: Quão formosos são os pés dos que anunciam a paz, dos que anunciam coisas boas!
Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa'azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa'azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, “Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!”
16 Mas nem todos obedecem ao evangelho; porque Isaias diz: Senhor, quem creu na nossa pregação?
Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, ''Ubangiji, wa ya gaskata da sakon?
17 De sorte que a fé é pelo ouvir, e o ouvir pela palavra de Deus.
Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu.
18 Mas digo: Porventura não ouviram? Sim, por certo, pois por toda a terra saiu o som deles, e as suas palavras até aos confins do mundo.
Amma na ce, “ko basu ji ba ne? I, tabbas'' muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya.''
19 Mas digo: Porventura Israel não o conheceu? Primeiramente diz Moisés: Eu vos meterei em ciúmes com aqueles que não são povo, com gente insensata vos provocarei à ira.
yau, na ce, ''Ko Isra'ila basu sani ba ne?'' Da farko Musa ya ce, “Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al'umma ba. Abin da nake nufi nan shine al'ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali.''
20 E Isaias se atreve, e diz: Fui achado pelos que me não buscavam, fui manifestado aos que por mim não perguntavam.
Amma Ishaya da karfin hali ya ce, ''Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba.
21 Mas contra Israel diz: Todo o dia estendi as minhas mãos a um povo rebelde e contradizente.
''Amma ga Isra'ila kam ya ce, '' na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai.''

< Romanos 10 >