< Kaudial 16 >

1 O I ronger ngil laud eu sang nan im en kaudok o, mamasani ong tounlang isimen: Komail kowei, wudokedi ong sappa dal isu, me audekier ongiong en Kot.
Na ji babban murya na kira daga cikin haikali tana ce wa malai'iku bakwai, ''Ku je ku zuba tasoshi bakwai na fushin Allah a kan duniya.”
2 Men mas ap kotiwei wudokila ong sappa a dal, ap wiala kins sued ong aramas akan, me kilelekidi kilel en man o, o me pongi a kilel.
Mala'ika na fari ya je ya zuba tasarsa a kan duniya; munanan gyambuna masu zafi suka fito wa mutane wadanda suke da alamar dabbar, wadanda suka bauta wa siffarsa.
3 O kariamen wudokila a dal ong nan madau ap wiala nta due nt’ en melar amen, ari me maur karos nan madau ap melar.
Mala'ika na biyu ya zuba tasarsa cikin teku. Ya zama jini, kamar jinin wanda ya mutu, kuma kowane abu mai rai da ke cikin tekun ya mutu.'
4 O kasilimen wudokila a dal pon pilap o utun pil akan, rap ntalar.
Malaika na uku ya zuba tasarsa a cikin rafuffuka da mabulbulan ruwa, sai suka zama jini.
5 I ronger tounlang en pil akan masani: Komui me pung, me kotikot, o me kotikot mas, me saraui, pwe komui kadeikada due met.
Na ji mala'ikan ruwaye ya ce, ''Kai mai adalci ne - wanda ya ke yanzu wanda yake kuma a da, Mai Tsarkin nan, domin ka shari'anta wadannan abubuwa.
6 Pwe irail kieledier ntan me saraui o saukop akan, ari, kom kotin katungole kin ir nta; ari, me mau ong irail.
Domin sun zubar da jinin masu ba da gaskiya da annabawa, ka basu jini su sha; shine abinda da ya dace da su.
7 I ronger me pei saraui o masani: Ei, Maing Kot, Kaun en meakaros, melel o me pung omui kadeik kan.
Na ji bagadi ya amsa, ''I, Ubangiji Allah Mai iko duka, shari'un ka gaskiya ne da adalci.''
8 A kapamen wudokila a dal pon katipin, a kapi ong i, en isiki kisiniai aramas akan.
Mala'ika na hudu ya zuba tasarsa a kan rana, kuma aka ba shi izini ya kone jama'a da wuta.
9 Ari, aramas rongkila karakar kaualap, o re lalaue mar en Kot, me Kaun pan kamekam pukat; a re sota kalukila, pwen wauneki i.
Suka kone da zafi mai tsanani, kuma suka sabi sunan Allah, wanda ke da iko akan annobai. Ba su tuba ba ko su daukaka shi.
10 O tounlang kalimen wudokila a dal pon mol en man o; ari a wei rotorotala; o re ke pasang lo arail pweki motakan madak.
Sai malaika na biyar ya zuba tasarsa a kan kursiyin dabban, sai duhu ya rufe mulkinsa. Suka cicciji harsunansu saboda zafi.
11 O irail lalaue Kot en lang, aki ar madak o ar kins akan, o re sota kalukila ar wiawia kan.
Suka yi sabon Allah na sama domin zafi da gyambunansu, suka kuma ki su tuba daga abin da suka yi.
12 O tounlang kawonemen wudokila a dal pon pilap Oiprat, a pil ap ngalengaledi, pwen kaonopada al mon nanmarki, me kotido sang ni pali mas en lang.
Mala'ika na shida ya zuba tasarsa cikin babban rafi, Yufiretis. Ruwansa ya bushe domin a shirya hanya da sarakuna za su zo daga gabas.
13 O i kilanger, me sang nan au en drake, o sang nan au en man o, o sang nan au en saukop likam ngen samin silu dueta pros kai koda sang.
Na ga kazamun ruhohi uku suna kama da kwadin da ke fitowa daga bakin diragon, da makaryacin annabi.
14 Ir ngen en tewil kai, wiawia kilel kai, me kin pwaralang nanmarki en sappa kan, en kapokon ir penang mauin en ran lapalap en Kot manaman.
Gama su ruhohin aljanu ne masu aikata alamun ban mamaki. Sun fita za su wurin sarakunan dukan duniya domin su tattaro su wuri daya saboda yaki a babbar ranar Allah Mai iko duka.
15 Kilang, I pwarado dueta lipirap amen; meid pai, me kin masamasan, nekinekid a likau kan, pwe a de kilisola, rap kilang a kanamenok.
(''Duba! Ina zuwa kamar barawo! Mai albarka ne wanda ke zaune a fadake, wanda ke sanye da tufafinsa domin ba zai fita tsirara a ga tsiraicin sa ba.”)
16 O re kapokon ir penang wasa, me ad a ni lokaia en Ipru Armakedon.
Aka kawo su tare a wurin da ake kira Armagiddon da Ibraniyanci.
17 O tounlang kaisimen wudokila a dal nin wäwä, ngil laud ap pwaradar sang im en kaudok nanlang, sang ni mol o mamasani: A wiauier.
Mala'ika na bakwai ya zuba tasarsa cikin iska. Sa'annan babbar murya ta fito daga cikin haikali da kuma kursiyin, cewa, ''An gama!''
18 Ari, liol o ngil kai o nansapwe wiauier, o sappa rerer kaualap, sota due sang tapin aramas mi sappa, pwe me lapalap o mulatok.
Aka yi walkiya, da kararraki masu tsanani, da aradu da babbar girgizar kasa - girgizar da ta fi kowacce da aka taba yi tun da 'yan adam suke a duniya, girgizar da girma ta ke.
19 Ari, kanim lapalap pal pasang wiala silekis silu, o kanim en sap akan rongk pasang, o Kot kotin tamanda kanim Papilon, pwen kotiki ong i dal en wain en a ongiong lapalap.
Babban birnin ya rabu kashi uku, kuma biranen al'ummai suka fadi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, sai ya ba wancan birnin koko cike da ruwan innabi wanda aka yi daga fushinsa mai tsanani.
20 O dake karos mokid wei sang o nana kan solar sansal.
Kowanne tsibiri ya bace, sai ba a kara ganin duwatsun ba.
21 O akel lapalap, toutouki paun epuki, me moredi sang lang lel aramas akan, o aramas lalaue Kot pweki kamekam akel, pwe iei kamekam me lapalapia.
Manyan duwatsun kankara, masu nauyin talanti, suka fado daga sama kan mutane. Suka zagi Allah domin annobar kankarar saboda annobar ta yi tsanani.

< Kaudial 16 >