< مکاشفهٔ یوحنا 9 >

و چون فرشته پنجم نواخت، ستاره‌ای رادیدم که بر زمین افتاده بود و کلید چاه هاویه بدو داده شد. (Abyssos g12) ۱ 1
Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. (Abyssos g12)
و چاه هاویه را گشاد ودودی چون دود تنوری عظیم از چاه بالا آمد وآفتاب و هوا از دود چاه تاریک گشت. (Abyssos g12) ۲ 2
Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. (Abyssos g12)
و از میان دود، ملخها به زمین برآمدند و به آنها قوتی چون قوت عقربهای زمین داده شد ۳ 3
Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya.
و بدیشان گفته شدکه ضرر نرسانند نه به گیاه زمین و نه به هیچ سبزی و نه به درختی بلکه به آن مردمانی که مهر خدا رابر پیشانی خود ندارند. ۴ 4
Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani.
و به آنها داده شد که ایشان را نکشند بلکه تا مدت پنج ماه معذب بدارند و اذیت آنها مثل اذیت عقرب بود، وقتی که کسی را نیش زند. ۵ 5
Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum.
و در آن ایام، مردم طلب موت خواهند کرد و آن را نخواهند یافت و تمنای موت خواهند داشت، اما موت از ایشان خواهدگریخت. ۶ 6
Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu.
و صورت ملخها چون اسبهای آراسته شده برای جنگ بود و بر سر ایشان مثل تاجهای شبیه طلا، و چهره های ایشان شبیه صورت انسان بود. ۷ 7
Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane.
و مویی داشتند چون موی زنان، و دندانهایشان مانند دندانهای شیران بود. ۸ 8
Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki.
و جوشنها داشتند، چون جوشنهای آهنین و صدای بالهای ایشان، مثل صدای ارابه های اسبهای بسیار که به جنگ همی تازند. ۹ 9
Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi.
و دمها چون عقربها با نیشهاداشتند؛ و در دم آنها قدرت بود که تا مدت پنج ماه مردم را اذیت نمایند. ۱۰ 10
Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar.
و بر خود، پادشاهی داشتند که ملک الهاویه است که در عبرانی به ابدون مسمی است و در یونانی او را اپلیون خوانند. (Abyssos g12) ۱۱ 11
Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon. (Abyssos g12)
یک وای گذشته است. اینک دو وای دیگر بعد از این می‌آید. ۱۲ 12
Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa.
و فرشته ششم بنواخت که ناگاه آوازی از میان چهار شاخ مذبح طلایی که در حضور خداست شنیدم ۱۳ 13
Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah.
که به آن فرشته ششم که صاحب کرنابود می‌گوید: «آن چهار فرشته را که بر نهر عظیم فرات بسته‌اند، خلاص کن.» ۱۴ 14
Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.”
پس آن چهارفرشته که برای ساعت و روز و ماه و سال معین مهیا شده‌اند تا اینکه ثلث مردم را بکشند، خلاصی یافتند. ۱۵ 15
Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na’yan Adam.
و عدد جنود سواران، دویست هزار هزار بود که عدد ایشان را شنیدم. ۱۶ 16
Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu.
و به اینطور اسبان و سواران ایشان را دررویا دیدم که جوشنهای آتشین و آسمانجونی وکبریتی دارند و سرهای اسبان چون سر شیران است و از دهانشان آتش و دود و کبریت بیرون می‌آید. ۱۷ 17
Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa.
از این سه بلا یعنی آتش و دود وکبریت که از دهانشان برمی آید، ثلث مردم هلاک شدند. ۱۸ 18
Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu.
زیرا که قدرت اسبان در دهان و دم ایشان است، زیرا که دمهای آنها چون مارهاست که سرها دارد و به آنها اذیت می‌کنند. ۱۹ 19
Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni.
و سایرمردم که به این بلایا کشته نگشتند، از اعمال دستهای خود توبه نکردند تا آنکه عبادت دیوها وبتهای طلا و نقره و برنج و سنگ و چوب را که طاقت دیدن و شنیدن و خرامیدن ندارند، ترک کنند؛ ۲۰ 20
Sauran’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba.
و از قتل‌ها و جادوگریها و زنا و دزدیهای خود توبه نکردند. ۲۱ 21
Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.

< مکاشفهٔ یوحنا 9 >