< اول قرنتیان 2 >

و من‌ای برادران، چون به نزد شما آمدم، با فضیلت کلام یا حکمت نیامدم چون شمارا به‌سر خدا اعلام می‌نمودم. ۱ 1
Lokacin da na zo wurin ku, yan'uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah [ a yayinda na bada shaida game da Allah].
زیرا عزیمت نکردم که چیزی در میان شما دانسته باشم جزعیسی مسیح و او را مصلوب. ۲ 2
Domin na kudura a zuciyata kada in san komai lokacin da nake tare da ku, sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye.
و من در ضعف وترس و لرزش بسیار نزد شما شدم، ۳ 3
Ina tare da ku cikin kasawa, da tsoro, da fargaba mai yawa.
و کلام ووعظ من به سخنان مقنع حکمت نبود، بلکه به برهان روح و قوت، ۴ 4
Kuma sakona da shelata basu tare da kalmomin hikima masu daukar hankali. Maimakon haka, sun zo da bayyanuwar Ruhu da iko,
تا ایمان شما در حکمت انسان نباشد بلکه در قوت خدا. ۵ 5
saboda kada bangaskiyarku ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah.
لکن حکمتی بیان می‌کنیم نزد کاملین، اماحکمتی که از این عالم نیست و نه از روسای این عالم که زایل می‌گردند. (aiōn g165) ۶ 6
Yanzu muna maganar hikima ga wadanda suka ginu, amma ba hikima ta duniyan nan ba, ko ta masu mulkin wannan zamani, wadanda suke shudewa. (aiōn g165)
بلکه حکمت خدا را درسری بیان می‌کنیم، یعنی آن حکمت مخفی را که خدا پیش از دهرها برای جلال ما مقدر فرمود، (aiōn g165) ۷ 7
Maimakon haka, muna maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya, boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin daukakarmu. (aiōn g165)
که احدی از روسای این عالم آن را ندانست زیرا اگر می‌دانستند خداوند جلال را مصلوب نمی کردند. (aiōn g165) ۸ 8
Babu wani mai mulki na zamanin nan da ya san wannan hikimar, domin inda sun gane ta a wancan lokacin, da basu gicciye Ubangijin daukaka ba. (aiōn g165)
بلکه چنانکه مکتوب است: «چیزهایی را که چشمی ندید و گوشی نشنید و به‌خاطر انسانی خطور نکرد، یعنی آنچه خدا برای دوستداران خود مهیا کرده است.» ۹ 9
Amma kamar yadda yake a rubuce, “Abubuwan da babu idon da ya gani, babu kunnen da ya ji, babu zuciyar da ta yi tsammanin sa, abubuwan da Allah ya shirya wa wadanda suke kaunarsa.
اما خدا آنهارا به روح خود بر ما کشف نموده است، زیرا که روح همه‌چیز حتی عمقهای خدا را نیز تفحص می‌کند. ۱۰ 10
Wadannan ne abubuwan da Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu yana bincika komai, har ma abubuwa masu zurfi na Allah.
زیرا کیست از مردمان که امور انسان رابداند جز روح انسان که در وی می‌باشد. همچنین نیز امور خدا را هیچ‌کس ندانسته است، جز روح خدا. ۱۱ 11
Gama wanene ya san tunanin mutum, sai dai ko ruhun mutumin da ke cikinsa? Haka ma, babu wanda ya san abubuwa masu zurfi na Allah sai dai Ruhun Allah.
لیکن ما روح جهان را نیافته‌ایم، بلکه آن روح که از خداست تا آنچه خدا به ما عطا فرموده است بدانیم. ۱۲ 12
Ba mu karbi ruhu na duniya ba, amma Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin mu san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah.
که آنها را نیز بیان می‌کنیم نه به سخنان آموخته شده از حکمت انسان، بلکه به آنچه روح‌القدس می‌آموزد و روحانیها را باروحانیها جمع می‌نماییم. ۱۳ 13
Muna maganar wadannan abubuwa da kalmomin da hikimar da mutum baza ta iya koyarwa ba, amma wadanda Ruhu ke koyar da mu. Ruhu yana fassara kalmomi na ruhaniya da hikima ta ruhaniya.
اما انسان نفسانی‌امور روح خدا را نمی پذیرد زیرا که نزد او جهالت است و آنها را نمی تواند فهمید زیرا حکم آنها ازروح می‌شود. ۱۴ 14
Mutum marar ruhaniya ba ya karbar abubuwan da suke daga Ruhun Allah, gama wauta suke a gareshi. Ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su.
لکن شخص روحانی در همه‌چیز حکم می‌کند و کسی را در او حکم نیست. ۱۵ 15
Shi wanda yake mai ruhaniya yana shari'anta dukan abubuwa, amma shi baya karkashin shari'ar sauran mutane.
«زیرا کیست که فکر خداوند را دانسته باشد تااو را تعلیم دهد؟» لکن ما فکر مسیح را داریم. ۱۶ 16
“Wa zai iya sanin zuciyar Ubangiji, da zai iya ba shi umarni?” Amma mu muna da lamiri irin na Almasihu.

< اول قرنتیان 2 >