< اول قرنتیان 1 >

پولس به اراده خدا رسول خوانده شده عیسی مسیح و سوستانیس برادر، ۱ 1
Bulus, kirayayye daga Almsihu Yesu don zama manzo ta wurin nufin Allah, da dan'uwanmu Sastanisu,
به کلیسای خدا که در قرنتس است، ازمقدسین در مسیح عیسی که برای تقدس خوانده شده‌اند، با همه کسانی که در هرجا نام خداوند ماعیسی مسیح را می‌خوانند که (خداوند) ما و(خداوند) ایشان است. ۲ 2
zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke korinti, zuwa ga wadanda aka kebe su cikin Almasihu Yesu, wadanda aka kira domin su zama al'umma maitsarki. Muna kuma rubuta wa dukan masu kira bisa sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a ko'ina, wato Ubangijinsu da Ubangijinmu kuma.
فیض و سلامتی ازجانب پدر ما خدا و عیسی مسیح خداوند بر شماباد. ۳ 3
Bari alheri da salama su zo gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
خدای خود را پیوسته شکر می‌کنم درباره شما برای آن فیض خدا که در مسیح عیسی به شما عطا شده است، ۴ 4
Kodayaushe ina gode wa Allahna domin ku, saboda alherin Allah da Almasihu Yesu ya yi maku.
زیرا شما از هرچیز دروی دولتمند شده‌اید، در هر کلام و در هرمعرفت. ۵ 5
Ya ba ku arziki ta kowace hanya, cikin dukkan magana da dukkan ilimi.
چنانکه شهادت مسیح در شما استوارگردید، ۶ 6
Kamar yadda shaida game da Almasihu ta tabbata gaskiya a tsakaninku.
بحدی که در هیچ بخشش ناقص نیستیدو منتظر مکاشفه خداوند ما عیسی مسیح می‌باشید. ۷ 7
Saboda haka baku rasa wata baiwa ta ruhaniya ba yayinda kuke marmarin jiran bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
که او نیز شما را تا آخر استوار خواهدفرمود تا در روز خداوند ما عیسی مسیح بی‌ملامت باشید. ۸ 8
Zai kuma karfafa ku zuwa karshe, saboda ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
امین است خدایی که شما را به شراکت پسر خود عیسی مسیح خداوند ماخوانده است. ۹ 9
Allah mai aminci ne shi wanda ya kira ku zuwa zumunta ta Dansa, Yesu Almasihu Ubangijimu.
لکن‌ای برادران از شما استدعا دارم به نام خداوند ما عیسی مسیح که همه یک سخن گوییدو شقاق در میان شما نباشد، بلکه در یک فکر ویک رای کامل شوید. ۱۰ 10
Ina rokon ku, yan'uwa, cikin sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku yarda da juna, kada tsattsaguwa ta kasance tsakanin ku. Ina rokon ku ku zama da zuciya daya da kuma nufi daya.
زیرا که‌ای برادران من، از اهل خانه خلوئی درباره شما خبر به من رسیدکه نزاعها در میان شما پیدا شده است. ۱۱ 11
Gama mutanen gidan Kulowi sun kawo kara cewa akwai tsattsaguwa a cikin ku.
غرض اینکه هریکی از شما می‌گوید که من از پولس هستم، و من از اپلس، و من از کیفا، و من از مسیح. ۱۲ 12
Ina nufin: kowannen ku na cewa, “Ina bayan Bulus,” ko “Ina bayan Afollos,” ko “Ina bayan Kefas,” ko “Ina bayan Almasihu.”
آیا مسیح منقسم شد؟ یا پولس در راه شمامصلوب گردید؟ یا به نام پولس تعمید یافتید؟ ۱۳ 13
Almasihu a rarrabe yake? An gicciye Bulus domin ku? Ko an yi maku baftisma a cikin sunan Bulus?
خدا را شکر می‌کنم که هیچ‌یکی از شما راتعمید ندادم جز کرسپس و قایوس، ۱۴ 14
Na godewa Allah domin ban yi wa wanin ku baftisma ba, sai dai Kirisfus da Gayus.
که مباداکسی گوید که به نام خود تعمید دادم. ۱۵ 15
Na yi wannan saboda kada wani ya ce an yi maku baftisma a cikin sunana.
وخاندان استیفان را نیز تعمید دادم و دیگر یادندارم که کسی را تعمید داده باشم. ۱۶ 16
(Na kuma yi wa iyalin gidan Sitifanas baftisma. Banda haka, ban sani ko na yi wa wani baftisma ba.)
زیرا که مسیح مرا فرستاد، نه تا تعمید دهم بلکه تا بشارت رسانم، نه به حکمت کلام مبادا صلیب مسیح باطل شود. ۱۷ 17
Gama Almasihu bai aiko ni domin yin baftisma ba, amma domin yin wa'azin bishara. Bai aiko ni domin in yi wa'azi da kalmomin hikimar mutum ba, saboda kada giciyen Almasihu ya rasa ikonsa.
زیرا ذکر صلیب برای هالکان حماقت است، لکن نزد ما که ناجیان هستیم قوت خداست. ۱۸ 18
Gama wa'azin gicciye wauta ne ga wadanda su ke mutuwa. Amma cikin wadanda Allah ke ceto, ikon Allah ne.
زیرا مکتوب است: «حکمت حکما را باطل سازم و فهم فهیمان را نابود گردانم.» ۱۹ 19
Gama a rubuce yake, “Zan watsar da hikimar masu hikima. Zan dode fahimtar masu basira.”
کجا است حکیم؟ کجا کاتب؟ کجا مباحث این دنیا؟ مگرخدا حکمت جهان را جهالت نگردانیده است؟ (aiōn g165) ۲۰ 20
Ina mai hikima? Ina masani? Ina mai muhawara na duniyan nan? Allah bai juya hikimar duniya zuwa wauta ba? (aiōn g165)
زیرا که چون برحسب حکمت خدا، جهان ازحکمت خود به معرفت خدا نرسید، خدا بدین رضا داد که بوسیله جهالت موعظه، ایمانداران رانجات‌بخشد. ۲۱ 21
Tunda duniya cikin hikimarta bata san Allah ba, ya gamshi Allah ta wurin wautar wa'azi ya ceci masu bada gaskiya.
چونکه یهود آیتی می‌خواهند ویونانیان طالب حکمت هستند. ۲۲ 22
Gama Yahudawa suna bidar al'ajibai, Helinawa kuma suna neman hikima.
لکن ما به مسیح مصلوب وعظ می‌کنیم که یهود را لغزش و امت هارا جهالت است. ۲۳ 23
Amma muna wa'azin Almasihu gicciyayye, dutsen tuntube ga yahudawa da kuma wauta ga Helinawa.
لکن دعوت‌شدگان را خواه یهود و خواه یونانی مسیح قوت خدا و حکمت خدا است. ۲۴ 24
Amma ga wadanda Allah ya kira, Yahudawa da Helinawa, muna wa'azin Almasihu a matsayin iko da kuma hikimar Allah.
زیرا که جهالت خدا از انسان حکیمتر است و ناتوانی خدا از مردم، تواناتر. ۲۵ 25
Gama wautar Allah tafi mutane hikima, kuma rashin karfin Allah yafi mutane karfi.
زیرا‌ای برادران دعوت خود را ملاحظه نمایید که بسیاری بحسب جسم حکیم نیستند وبسیاری توانا نی و بسیاری شریف نی. ۲۶ 26
Dubi kiranku, yan'uwa. Ba dukkan ku ke da hikima a ma'aunin mutane ba. Ba dukkan ku ke da iko ba. Ba dukkan ku ke da haifuwa ta sarauta ba.
بلکه خدا جهال جهان را برگزید تا حکما را رسوا سازدو خدا ناتوانان عالم را برگزید تا توانایان را رسواسازد، ۲۷ 27
Amma Allah ya zabi abubuwan da suke wofi na duniya domin ya kunyatar da masu hikima. Allah ya zabi abin da ke marar karfi a duniya domin ya kunyatar da abinda ke mai karfi.
و خسیسان دنیا و محقران را خدابرگزید، بلکه نیستیها را تا هستیها را باطل گرداند. ۲۸ 28
Allah ya zabi abinda ke marar daraja da kuma renanne a duniya. Ya ma zabi abubuwan da ake dauka ba komai ba, domin ya wofinta abubuwan da ake dauka masu daraja.
تا هیچ بشری در حضور او فخر نکند. ۲۹ 29
Ya yi wannan ne domin kada wani ya sami dalilin fahariya a gabansa.
لکن از او شما هستید در عیسی مسیح که از جانب خدابرای شما حکمت شده است و عدالت قدوسیت و فدا. ۳۰ 30
Domin abinda Allah ya yi, yanzu kuna cikin Almasihu Yesu, wanda ya zamar mana hikima daga Allah. Ya zama adalcinmu, da tsarkinmu da fansarmu.
تا چنانکه مکتوب است هر‌که فخر کنددر خداوند فخر نماید. ۳۱ 31
A sakamakon haka, kamar yadda nassi ya ce, “Bari mai yin fahariya, ya yi fahariya cikin Ubangiji.”

< اول قرنتیان 1 >