< Zaccharias Propheta 7 >

1 et factum est in anno quarto Darii regis factum est verbum Domini ad Zacchariam in quarta mensis noni qui est casleu
A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb.
2 et miserunt ad domum Dei Sarasar et Rogomelech et viri qui erant cum eo ad deprecandam faciem Domini
Mutanen Betel sun aika Sharezer da Regem-Melek, tare da mutanensu su nemi tagomashin Ubangiji
3 ut dicerent sacerdotibus domus Domini exercituum et prophetis loquentes numquid flendum mihi est in mense quinto vel sanctificare me debeo sicuti feci iam multis annis
ta wurin tambayar firistocin da kuma annabawan gidan Ubangiji Maɗaukaki, “Ko ya kamata in yi makoki da azumi a wata na biyar, yadda na yi a shekaru masu yawa?”
4 et factum est verbum Domini exercituum ad me dicens
Sai maganar Ubangiji Maɗaukaki ta zo mini ta ce,
5 loquere ad omnem populum terrae et ad sacerdotes dicens cum ieiunaretis et plangeretis in quinto et septimo per hos septuaginta annos numquid ieiunium ieiunastis mihi
“Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi?
6 et cum comedistis et cum bibistis numquid non vobis comedistis et vobismet ipsis bibistis
Kuma sa’ad da kuke ci kuke sha, ba kanku kuke yi wa shagali ba?
7 numquid non sunt verba quae locutus est Dominus in manu prophetarum priorum cum adhuc Hierusalem habitaretur et esset opulenta ipsa et urbes in circuitu eius et ad austrum et in campestribus habitaretur
Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’”
8 et factum est verbum Domini ad Zacchariam dicens
Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa,
9 haec ait Dominus exercituum dicens iudicium verum iudicate et misericordiam et miserationes facite unusquisque cum fratre suo
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna.
10 et viduam et pupillum et advenam et pauperem nolite calumniari et malum vir fratri suo non cogitet in corde suo
Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’
11 et noluerunt adtendere et verterunt scapulam recedentem et aures suas adgravaverunt ne audirent
“Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu.
12 et cor suum posuerunt adamantem ne audirent legem et verba quae misit Dominus exercituum in spiritu suo per manum prophetarum priorum et facta est indignatio magna a Domino exercituum
Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai.
13 et factum est sicut locutus est et non audierunt sic clamabunt et non exaudiam dicit Dominus exercituum
“‘Sa’ad da na yi kira, ba su saurara ba; saboda haka sa’ad da suka kira, ba zan saurara ba,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
14 et dispersi eos per omnia regna quae nesciunt et terra desolata est ab eis eo quod non esset transiens et revertens et posuerunt terram desiderabilem in desertum
‘Na warwatsar da su da guguwa a cikin dukan ƙasashe, inda suka zama baƙi. Aka bar ƙasar ta zama kango bayansu, da har ba mai shiga ko fita. Haka suka sa ƙasan nan mai daɗi ta zama kango.’”

< Zaccharias Propheta 7 >