< Thessalonicenses I 3 >

1 propter quod non sustinentes amplius placuit nobis remanere Athenis solis
Saboda haka, da bamu iya jimrewa ba, sai mukayi tunanin cewa ya dace mu dakata a Atina tukunna.
2 et misimus Timotheum fratrem nostrum et ministrum Dei in evangelio Christi ad confirmandos vos et exhortandos pro fide vestra
Sai muka aikaTimoti, dan'uwanmu dakuma bawan Allah a bisharar Almasihu, domin karfafaku ya kuma ta'azantar daku a fannin bangaskiya.
3 ut nemo moveatur in tribulationibus istis ipsi enim scitis quod in hoc positi sumus
Mun yi haka ne saboda kada waninku ya raunana domin wadannan wahaloli. Domin ku da kanku kun sani cewa don haka aka kiraye mu.
4 nam et cum apud vos essemus praedicebamus vobis passuros nos tribulationes sicut et factum est et scitis
Hakika, a lokacin da muke tare daku, mun gaya maku cewa muna daf da shan wahala, haka ya kuma kasance, kamar yadda kuka sani.
5 propterea et ego amplius non sustinens misi ad cognoscendam fidem vestram ne forte temptaverit vos is qui temptat et inanis fiat labor noster
Domin haka, da ban iya jimrewa ba, sai na aiko domin in san yadda bangaskiyar ku take. Watakila ko magafci a wata hanya ya rinjaye ku, sai ya kasance wahalarmu ta zama a banza.
6 nunc autem veniente Timotheo ad nos a vobis et adnuntiante nobis fidem et caritatem vestram et quia memoriam nostri habetis bonam semper desiderantes nos videre sicut nos quoque vos
Amma Timoti da ya dawo daga gareku sai ya kawo mamu labari mai dadi akan bangaskiyarku da kuma kaunarku. Yako gaya mana cewa kuna kyakkyawan tunani a kanmu, kuma kuna marmarin ganinmu yadda muke marmarin ganinku.
7 ideo consolati sumus fratres in vobis in omni necessitate et tribulatione nostra per vestram fidem
Sabili da haka, 'yan'uwana, mun sami ta'aziyya tawurinku domin bangaskiyarku, a cikin dukkan bakin cikinmu da shan wuyamu.
8 quoniam nunc vivimus si vos statis in Domino
Yanzu a raye muke, idan kun tsaya da karfi a cikin Ubangiji.
9 quam enim gratiarum actionem possumus Deo retribuere pro vobis in omni gaudio quo gaudemus propter vos ante Deum nostrum
Gama wace irin godiya zamu ba Allah sabili da ku, domin dukan farin cikin da muke dashi a gaban Allah domin ku?
10 nocte et die abundantius orantes ut videamus faciem vestram et conpleamus ea quae desunt fidei vestrae
Dare da rana muke yi maku addu'a sosai domin muga fuskokinku kuma mu cika abin da kuka rasa cikin bangaskiyarku.
11 ipse autem Deus et Pater noster et Dominus Iesus dirigat viam nostram ad vos
Bari Allah da kuma Ubanmu da kansa, da Ubangijinmu Yesu, ya bida sawayen mu zuwa gareku.
12 vos autem Dominus multiplicet et abundare faciat caritatem in invicem et in omnes quemadmodum et nos in vobis
Bari Ubangiji yasa ku karu ku kuma ribambamya a kaunar 'yan'uwanku da dukan mutane, kamar yadda muke maku.
13 ad confirmanda corda vestra sine querella in sanctitate ante Deum et Patrem nostrum in adventu Domini nostri Iesu cum omnibus sanctis eius amen
Bari yayi haka domin ya karfafa zukatanku marassa abin zargi a cikin tsarki a gaban Allah da Ubanmu a lokacin zuwan Ubangijinmu Yesu da dukan tsarkakansa.

< Thessalonicenses I 3 >