< Titum 2 >

1 Tu autem loquere quae decent sanam doctrinam:
Amma kai, ka fadi abinda yayi daidai da amintaccen umarni.
2 Senes ut sobrii sint, pudici, prudentes, sani in fide, in dilectione, in patientia:
Dole tsofaffin mazaje su zama masu kamun kai, masu daraja kansu, masu-hankali, masu aminci cikin bangaskiya, cikin kauna da jurewa.
3 Anus similiter in habitu sancto, non criminatrices, non multo vino servientes, bene docentes:
Haka ma tsofaffin mataye su kame kansu da girma, ba magulmata ba. Kada su zama bayi wajen yawan shan ruwan inabi. Su koyar da abubuwa masu kyau
4 ut prudentiam doceant adolescentulas, ut viros suos ament, filios suos diligant,
domin su koyar da kananan mataye da hikima su kaunaci mazajensu da 'ya'yansu.
5 prudentes, castas, sobrias, domus curam habentes, benignas, subditas viris suis, ut non blasphemetur verbum Dei.
Su horar dasu su zama masu hikima da tsabtar zuci, masu tsaron gidajensu, kuma masu biyayya da mazajensu. Suyi wadannan abubuwa saboda kada maganar Allah ta sami zargi.
6 Iuvenes similiter hortare ut sobrii sint.
Ta haka kuma, ka karfafa samari, su zama masu hankali.
7 In omnibus teipsum praebe exemplum bonorum operum, in doctrina, in integritate, in gravitate,
A kowanne fanni, ka mayar da kan ka abin koyi a cikin kyawawan ayyuka; idan kayi koyarwa, ka nuna mutunci da martaba.
8 verbum sanum, irreprehensibile: ut is, qui ex adverso est, vereatur, nihil habens malum dicere de nobis:
Ka bada sako lafiyayye marar abin zargi, yadda masu hamayya da maganar Allah zasu ji kunya, domin rashin samun mugun abin fadi akan mu.
9 Servos dominis suis subditos esse, in omnibus placentes, non contradicentes,
Bayi suyi biyayya ga iyayengijin su a cikin komai. Su faranta masu rai, ba suyi gardama dasu ba.
10 non fraudantes, sed in omnibus fidem bonam ostendentes: ut doctrinam Salvatoris nostri Dei ornent in omnibus.
Kada suyi sata. Maimakon haka, sai su nuna dukan bangaskiya mai kyau, domin suyi wa koyarwarmu game da Allah mai cetonmu kwalliya a cikin dukan komai.
11 Apparuit enim gratia Dei Salvatoris nostri omnibus hominibus,
Domin alherin Allah ya bayyana ga dukan mutane.
12 erudiens nos, ut abnegantes impietatem, et saecularia desideria: sobrie, et iuste, et pie vivamus in hoc saeculo, (aiōn g165)
Yana koya mana mu musanci miyagun ayyuka, da sha'awoyin duniya. Yana horar damu muyi zama cikin hankali, da adalci a cikin hanyar allahntaka a wannan zamani (aiōn g165)
13 expectantes beatam spem, et adventum gloriae magni Dei, et Salvatoris nostri Iesu Christi:
yayin da muke cigaba da jiran karba albarkataccen begenmu, wato bayyanuwar daukakar Ubangiji Allah da kuma mai cetonmu Yesu Almasihu.
14 qui dedit semetipsum pro nobis, ut nos redimeret ab omni iniquitate, et mundaret sibi populum acceptabilem, sectatorem bonorum operum.
Yesu ya bada kansa domin mu, domin ya cece mu daga rashin kiyaye doka ya mai damu masu tsarki, domin sa, mutane na musamman wadanda suke da marmarin aikata kyawawan ayyuka.
15 Haec loquere, et exhortare, et argue cum omni imperio. Nemo te contemnat.
Ka yi magana da karfi ka karfafawa wadannan abubuwa. Ka yi gyara da dukan iko. Kada ka bar wani ya raina ka.

< Titum 2 >