< Lucam 2 >

1 Factum est autem in diebus illis, exiit edictum a Caesare Augusto ut describeretur universus orbis.
Ananan cikin kwanakin, sai Kaisar Augustas ya yi shela ya umarta a kidaya dukan mutane da ke zaune a cikin duniya.
2 Haec descriptio prima, facta est a praeside Syriae Cyrino:
Wannan itace kidaya ta farko da aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin Suriya.
3 et ibant omnes ut profiterentur singuli in suam civitatem.
Sabili da haka, kowa ya koma garinsa domin a yi masa rijista domin kidayan.
4 Ascendit autem et Ioseph a Galilaea de civitate Nazareth in Iudaeam in civitatem David, quae vocatur Bethlehem: eo quod esset de domo, et familia David,
Yusufu kuma ya tashi ya bar birnin Nazarat zuwa garin Baitalami da ke Yahudiya, wanda ake kuma kira birnin Dauda, domin shi daga zuriyar iyalin Dauda ne.
5 ut profiteretur cum Maria desponsata sibi uxore praegnante.
Ya je can ya yi rijista tare da Maryamu, wadda yake tashi tana kuma da juna biyu.
6 Factum est autem, cum essent ibi, impleti sunt dies ut pareret.
Ya zama sa'adda suke can, lokaci ya yi da za ta haifi danta.
7 Et peperit filium suum primogenitum, et pannis eum involvit, et reclinavit eum in praesepio: quia non erat ei locus in diversorio.
Ta haifi da, dan farinta kuwa, ta nade shi da kyau da 'yan tsummoki. Ta sa shi cikin wani kwami na dabbobi, gama babu daki dominsu a masaukin.
8 Et pastores erant in regione eadem vigilantes, et custodientes vigilias noctis super gregem suum.
A cikin wannan yankin, akwai makiyaya wadanda suke zama a sarari suna tsaron garken tumakinsu da dare.
9 Et ecce angelus Domini stetit iuxta illos, et claritas Dei circumfulsit illos, et timuerunt timore magno.
Nan da nan, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare su, daukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, sai suka figita kwarai.
10 Et dixit illis angelus: Nolite timere: ecce enim evangelizo vobis gaudium magnum, quod erit omni populo:
Sai mala'ikan ya ce masu, “Kada ku ji tsoro, domin na kawo maku labari mai dadi da zai kawo murna da yawa ga dukan mutane.
11 quia natus est vobis hodie Salvator, qui est Christus Dominus in civitate David.
Yau an haifi maku mai ceto a cikin birnin Dauda! Shine Almasihu Ubangiji!
12 Et hoc vobis signum: Invenietis infantem pannis involutum, et positum in praesepio.
Wannan itace alama da za a ba ku. Za ku ga dan jariri nade cikin 'yan tsummoki kwance cikin kwamin dabbobi.”
13 Et subito facta est cum angelo multitudo militiae caelestis laudantium Deum, et dicentium:
Nan take, sai ga babban taro daga sama tare da mala'ikan suna yabon Allah, suna cewa,
14 Gloria in altissimis Deo, et in terra pax hominibus bonae voluntatis.
“Daukaka ga Allah daga bisa, bari salama ta kasance a duniya tsakanin mutanen da ya ke jin dadinsu.”
15 Et factum est, ut discesserunt ab eis Angeli in caelum: pastores loquebantur ad invicem: Transeamus usque ad Bethlehem, et videamus hoc verbum, quod factum est, quod fecit Dominus, et ostendit nobis.
Ya zama sa'adda mala'iku suka bar su zuwa cikin sama, sai makiyayan su ka ce wa junansu, “Bari mu je Baitalami mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya nuna mana.”
16 Et venerunt festinantes: et invenerunt Mariam, et Ioseph, et infantem positum in praesepio.
Su ka yi hamzari suka tafi can sun iske Maryamu da Yusufu, suka ga jaririn kuwa kwance a cikin kwamin dabbobin.
17 Videntes autem cognoverunt de verbo, quod dictum erat illis de puero hoc.
Bayan da sun ga wannan, suka gaya wa mutane abinda aka gaya masu game da wannan yaro.
18 Et omnes, qui audierunt, mirati sunt: et de his, quae dicta erant a pastoribus ad ipsos.
Dukan wadanda su ka ji, su ka yi mamaki kwarai game da abin da makiyayan su ka gaya masu.
19 Maria autem conservabat omnia verba haec, conferens in corde suo.
Amma ita Maryamu ta ci gaba da tunani akan wadanan abubuwa da ta ji, tana tunani mai zurfi a cikin zuciyarta.
20 Et reversi sunt pastores glorificantes, et laudantes Deum in omnibus, quae audierant, et viderant sicut dictum est ad illos.
Makiyayan suka koma suna ta daukaka da yabon Allah domin dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, dadai da yadda aka gaya masu.
21 Et postquam consummati sunt dies octo ut circumcideretur puer: vocatum est nomen eius Iesus, quod vocatum est ab angelo prius quam in utero conciperetur.
Da ya kai kwana takwas, lokacin da za a yi wa jaririn kaciya, sai aka rada masa suna Yesu, sunan da mala'ikan ya bashi kamin a yi cikinsa.
22 Et postquam impleti sunt dies purgationis eius secundum legem Moysi, tulerunt illum in Ierusalem, ut sisterent eum Domino,
Da kwanakin tsarkakewar su ya wuce bisa ga shari'ar Musa, Yusufu da Maryamu suka kawo shi cikin haikali a Urushalima dominsu mika shi ga Ubangiji.
23 sicut scriptum est in lege Domini: Quia omne masculinum adaperiens vulvam, sanctum Domino vocabitur.
Kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, “Za a kira duk da na fari kebabbe ga Ubangiji.”
24 et ut darent hostiam secundum quod dictum est in lege Domini par turturum, aut duos pullos columbarum.
Suka kuma zo su mika hadaya bisa ga yadda aka fada a shari'ar Ubangiji, “Kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu.”
25 Et ecce homo erat in Ierusalem, cui nomen Simeon, et homo iste iustus, et timoratus, expectans consolationem Israel, et Spiritus sanctus erat in eo.
Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa.
26 Et responsum acceperat a Spiritu sancto, non visurum se mortem, nisi prius videret Christum Domini.
An kuma bayyana masa ta wurin Ruhu Mai-tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kristi na Ubangiji.
27 Et venit in spiritu in templum. Et cum inducerent puerum Iesum parentes eius, ut facerent secundum consuetudinem legis pro eo:
Wata rana Siman ya zo cikin haikali ta wurin jagorar Ruhu Mai-tsarki. Da iyayen suka kawo yaron ciki, wato Yesu, domin su cika sharudan da shari'ar ke bukata,
28 et ipse accepit eum in ulnas suas, et benedixit Deum, et dixit:
sai Siman ya karbe shi cikin hanuwansa, ya yabi Allah ya ce,
29 Nunc dimittis servum tuum Domine, secundum verbum tuum in pace:
“Yanzu bari bawanka ya tafi da salama, Ubangiji, bisa ga kalmarka.
30 Quia viderunt oculi mei salutare tuum,
Domin idanuna sun ga cetonka,
31 Quod parasti ante faciem omnium populorum.
wanda ka shirya a gaban dukan mutane:
32 Lumen ad revelationem gentium, et gloriam plebis tuae Israel.
Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila.”
33 Et erat pater et mater eius mirantes super his, quae dicebantur de illo.
Mahaifin yaron da Mahaifiyarsa, sun yi mamaki kwarai domin abubuwan da aka fada akansa.
34 Et benedixit illis Simeon, et dixit ad Mariam matrem eius: Ecce positus est hic in ruinam, et in resurrectionem multorum in Israel: et in signum, cui contradicetur:
Sai Siman ya albarkace su ya ce wa uwatasa Maryamu, “Ki ji da kyau, wannan yaro zai zama sanadiyar faduwa da tashin mutane dayawa a Isra'ila, kuma alama wadda ake kushen ta.
35 et tuam ipsius animam pertransibit gladius ut revelentur ex multis cordibus cogitationes.
Kuma takobi zai tsaga zuciyar ki yadda tunanin mutane za ya bayyana.”
36 Et erat Anna prophetissa, filia Phanuel, de tribu Aser: haec processerat in diebus multis, et vixerat cum viro suo annis septem a virginitate sua.
Wata annabiya mai suna Annatu ta na nan wurin. Ita diyar Fanuyila ce daga kabilar Ashiru. Ta riga ta manyanta a shekaru sosai. Ta kasance da maigidanta shekaru bakwai bayan auren ta,
37 Et haec vidua erat usque ad annos octoginta quattuor: quae non discedebat de templo, ieiuniis, et obsecrationibus serviens nocte, ac die.
sannan ta yi zama gwambranci na shekaru tamanin da hudu. Ba ta taba barin haikali ba, tana ci gaba da yi wa Ubangiji sujada, dare da rana.
38 Et haec, ipsa hora superveniens, confitebatur Domino: et loquebatur de illo omnibus, qui expectabant redemptionem Israel.
A dadai lokacin nan, ta hau zuwa wurinsu ta fara yi wa Allah godiya. Ta gaya wa dukan wadanda ke jiran fansar Urushalima.
39 Et ut perfecerunt omnia secundum legem Domini, reversi sunt in Galilaeam in civitatem suam Nazareth.
Da su ka gama komai da aka bukace su suyi bisa ga tafarkin shari'ar Ubangiji, sai suka koma Galili, zuwa birninsu, Nazarat.
40 Puer autem crescebat, et confortabatur plenus sapientia: et gratia Dei erat in illo.
Yaron kuma ya yi girma ya zama da karfi, yana karuwa da hikima, alherin Ubangiji kuma yana kansa.
41 Et ibant parentes eius per omnes annos in Ierusalem, in die sollemni Paschae.
Iyayensa sukan tafi Urushalima kowacce shekara domin idin ketarewa.
42 Et cum factus esset annorum duodecim, ascendentibus illis Ierosolymam secundum consuetudinem diei festi,
Da yana shekara goma sha biyu, suka sake haurawa daidai lokacin idin a al'adance.
43 consummatisque diebus, cum redirent, remansit puer Iesus in Ierusalem, et non cognoverunt parentes eius.
Bayan da sun cika dukan kwanakin idin, sun fara dawowa gida. Amma dan yaron Yesu ya jinkirta ya zauna a Urushalima, kuma iyayensa basu sani ba.
44 Existimantes autem illum esse in comitatu, venerunt iter diei, et requirebant eum inter cognatos, et notos.
Suna tsammani yana tare da sauran mutane da suke tafiya tare, sai suka yi tafiya na kwana daya. Suka fara neman sa a cikin danginsu da abokansu.
45 Et non invenientes, regressi sunt in Ierusalem, requirentes eum.
Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima suna cigiyar sa a can.
46 Et factum est, post triduum invenerunt illum in templo sedentem in medio doctorum, audientem illos, et interrogantem eos.
Ya zama bayan kwanaki uku, su ka same shi a cikin haikali, yana zama a tsakiyar malamai, yana sauraron su yana kuma yi masu tambayoyi.
47 Stupebant autem omnes, qui eum audiebant, super prudentia, et responsis eius.
Dukan wadanda suka ji shi suna ta mamakin fahimtar sa da amsoshin sa.
48 Et videntes admirati sunt. Et dixit mater eius ad illum: Fili, quid fecisti nobis sic? ecce pater tuus, et ego dolentes quaerebamus te.
Da suka gan shi, suka yi mamaki kwarai. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Da na, don me ka yi mana haka? Ka ji, mahaifinka da ni muna ta neman ka rai a bace.”
49 Et ait ad illos: Quid est quod me quaerebatis? nesciebatis quia in his, quae patris mei sunt, oportet me esse?
Ya ce masu, “Don me kuke nema na? Ba ku sani cewa dole in kasance a gidan Ubana ba?”
50 Et ipsi non intellexerunt verbum, quod locutus est ad eos.
Amma ba su gane abin da yake nufi da kalmomin nan ba.
51 Et descendit cum eis, et venit Nazareth: et erat subditus illis. Et mater eius conservabat omnia verba haec in corde suo.
Sa'annan ya koma gida tare da su zuwa Nazarat yana kuma masu biyayya. Mahaifiayarsa kuma ta ajiye dukan wadannan abubuwa a zuciyarta tana yin tunani akansu.
52 Et Iesus proficiebat sapientia, et aetate, et gratia apud Deum, et homines.
Amma Yesu ya ci gaba da hikima da girma, ya kuma karu da tagomashi wurin Allah da mutane.

< Lucam 2 >