< Hebræos 2 >

1 Propterea abundantius oportet observare nos ea, quae audivimus ne forte pereffluamus.
Saboda haka, lalle ne mu kara mai da hankali musamman da abubuwan da mu ka ji, don kada mu yi sakaci, su sullube mana.
2 Si enim qui per Angelos dictus est sermo, factus est firmus, et omnis praevaricatio, et inobedientia accepit iustam mercedis retributionem:
Idan kuwa maganar nan da aka fada ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowanne keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su,
3 quomodo nos effugiemus si tantam neglexerimus salutem? quae cum initium accepisset enarrari per Dominum ab eis, qui audierunt, in nos confirmata est,
ta kaka za mu tsira, in mun ki kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji da kansa, shi ne ya fara sanar da shi, wadanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi.
4 contestante Deo signis et portentis, et variis virtutibus, et Spiritus sancti distributionibus secundum suam voluntatem.
San'nan kuma Allah da kansa ya shaida ta wasu alamu, da abubuwan al'ajabai, da mu'ajizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.
5 Non enim Angelis subiecit Deus orbem terrae futurum, de quo loquimur.
Ai ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar nan da za a yi, wanda muke zance.
6 Testatus est autem in quodam loco quis, dicens: Quid est homo quod memor es eius, aut filius hominis quoniam visitas eum?
Amma wani ya shaida a wani wuri cewa, 'Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi? Ko dan mutum ma, har da za ka kula da shi?'
7 Minuisti eum paulominus ab Angelis: gloria et honore coronasti eum: et constituisti eum super opera manuum tuarum.
Ka sa mutum ya gaza mala'iku; Ka nada shi da daukaka da girma. Bisa dukkan hallitta.
8 Omnia subiecisti sub pedibus eius: In eo enim quod omnia ei subiecit, nihil dimisit non subiectum ei. Nunc autem necdum videmus omnia subiecta ei.
Ka dora shi a kan dukkan halittarka, ka kuma mallakar da kome a karkashin sawayensa. Domin Allah ya mallakar da dukkan abubuwa a karkashinsa. Bai bar kome a kebe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba tukuna.
9 Eum autem, qui modico quam Angeli minoratus est, videmus Iesum propter passionem mortis, gloria et honore coronatum: ut gratia Dei, pro omnibus gustaret mortem.
Amma mun ga wani wanda dan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, shine Yesu, an nada shi da daukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa, wanan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.
10 Decebat enim eum, propter quem omnia, et per quem omnia, qui multos filios in gloriam adduxerat, auctorem salutis eorum per passionem consummari.
Saboda haka, ya dace ga Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance domin sa, ta gare shi, domin ya kawo 'ya'ya masu yawa ga samun daukaka. Domin a kammala cetonsu ta wurin shan wuyarsa.
11 Qui enim sanctificat, et qui sanctificantur, ex uno omnes. Propter quam causam non confunditur fratres eos vocare, dicens:
Domin da shi mai tsarkakewar da kuma wadanda aka tsarkaken, duk tushensu daya ne. Saboda wanan dalili ne shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su 'ya'uwansa.
12 Nunciabo nomen tuum fratribus meis: in medio Ecclesiae laudabo te.
Da yace, ''zan sanar da sunanka ga ya'uwana, a tsakiyar taronsu zan yabe ka da waka.''
13 Et iterum: Ego ero fidens in eum. Et iterum: Ecce ego, et pueri mei, quos dedit mihi Deus.
Har wa yau, yace, ''Zan dogara a gare shi.'' Da kuma ''Ga ni nan, ni da 'ya'yan da Allah ya ba ni.''
14 Quia ergo pueri communicaverunt carni, et sanguini, et ipse similiter participavit eisdem: ut per mortem destrueret eum, qui habebat mortis imperium, id est, diabolum:
Wato tun da yake 'ya'yan Allah duk suna da nama da jini, Yesu ma ya dauki kamannin haka, ta wurin mutuwa ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis.
15 et liberaret eos, qui timore mortis per totam vitam obnoxii erant servituti.
Ya kuma 'yanta duk wadanda tun haihuwarsu suke zaman bauta sabo da tsoron mutuwa.
16 Nusquam enim Angelos apprehendit, sed semen Abrahae apprehendit.
Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako.
17 Unde debuit per omnia fratribus similari, ut misericors fieret, et fidelis pontifex ad Deum, et ut repropitiaret delicta populi.
Saboda haka, lalle ne ya zama kamar yan'uwansa ta kowacce hanya, domin ya zama babban Firist, mai jinkai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, ya kuma mika hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.
18 In eo enim, in quo passus est ipse et tentatus, potens est et eis, qui tentantur, auxiliari.
Tun da yake Yesu ma da kansa ya sha wahala, sa'adda aka gwada shi, don haka, zai taimaki wadanda ake yi wa gwaji.

< Hebræos 2 >