< Galatas 4 >

1 Dico autem: Quanto tempore heres parvulus est, nihil differt a servo, cum sit dominus omnium:
Ina cewa muddin magaji yaro ne, babu bambancin sa da bawa, ko da yake shine mai mallakan dukan kadarorin.
2 sed sub tutoribus, et actoribus est usque ad praefinitum tempus a patre:
A maimakon haka, yana karkashin masu jagora da amintattu har sai lokacin da mahaifinsa ya ajiye.
3 ita et nos cum essemus parvuli, sub elementis mundi eramus servientes.
Hakannan mu ma, lokaci da muke yara, an rike mu cikin kangi na tushin ka'idojin wannan duniya.
4 At ubi venit plenitudo temporis, misit Deus Filium suum factum ex muliere, factum sub lege,
Amma da lokacin ya yi daidai, Allah ya aiko da dansa, haihuwar mace, haihuwar karkashin shari'a.
5 ut eos, qui sub lege erant, redimeret, ut adoptionem filiorum reciperemus.
Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya.
6 Quoniam autem estis filii, misit Deus Spiritum filii Dei sui in corda vestra clamantem: Abba, Pater.
Domin ku 'ya'ya ne, Allah ya aiko da Ruhun Dansa cikin zuciyarmu, Ruhun wanda ke kirar, “Abba, Uba.”
7 Itaque iam non est servus, sed filius: Quod si filius: et heres per Deum.
Saboda wannan dalilin kai ba kuma bawa ba ne amma da. Idan kai da ne, hakannan kuma kai ma magaji ne ta wurin Allah.
8 Sed tunc quidem ignorantes Deum, iis, qui natura non sunt dii, serviebatis.
Duk da haka a da, da ba ku san Allah ba, bayi ne ku ga alloli wadanda ainihi ba alloli ba ne ko kadan.
9 Nunc autem cum cognoveritis Deum, immo cogniti sitis a Deo: quomodo convertimini iterum ad infirma, et egena elementa, quibus denuo servire vultis?
Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma, yanzu da Allah ya san ku, me ya sa kuke sake komawa zuwa ga tushen ka'idodin nan mara karfi da amfani? Kuna so ku sake komawa zaman bayi kuma daga farko?
10 Dies observatis, et menses, et tempora, et annos.
Kuna kiyaye ranaku na musamman, sabobin watanni, lokatai, da shekaru.
11 Timeo, ne forte sine causa laboraverim in vobis.
Ina ji maku tsoro. Ina tsoro cewa kamar na yi aiki cikinku a wofi.
12 Estote sicut ego, quia et ego sicut vos: fratres obsecro vos. Nihil me laesistis.
Ina rokon ku 'yan'uwa, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma na zama kamar ku. Ba ku yi mani laifin komai ba.
13 Scitis autem quia per infirmitatem carnis evangelizavi vobis iampridem: et tentationem vestram in carne mea
Amma kun sani cewa saboda rashin lafiya ne na yi maku shelar bishara da farko.
14 non sprevistis, neque respuistis: sed sicut Angelum Dei excepistis me, sicut Christum Iesum.
Ko da yake halin da nake ciki cikin jiki a zahiri ya sa ku cikin gwaji, ba ku raina ni ba ko kuma kuka watsar da ni. A maimakon haka, kun karbe ni kamar mala'ikan Allah, kamar ni Almasihu Yesu ne da kansa.
15 Ubi est ergo beatitudo vestra? Testimonium enim perhibeo vobis, quia, si fieri posset, oculos vestros eruissetis, et dedissetis mihi.
Saboda haka, yanzu ina murnar taku? Domin ina shaidar ku, idan mai yiwuwa ne, da kun kwakulo idanunku, kun ba ni.
16 Ergo inimicus vobis factus sum, verum dicens vobis?
To kenan, na zama makiyin ku ne saboda na gaya maku gaskiya?
17 Aemulantur vos non bene: sed excludere vos volunt, ut illos aemulemini.
Suna neman ku da himma ba domin wani alheri ba ne. Suna so su raba ni da ku domin ku bi su.
18 Bonum autem aemulamini in bono semper: et non tantum cum praesens sum apud vos.
Yana da kyau ko yaushe a yi himma domin dalilai masu kyau, ba kuma kawai sa'adda ina tare da ku ba.
19 Filioli mei, quos iterum parturio, donec formetur Christus in vobis.
'Ya'yana kanana, sabili da ku ina cikin zafin nakuda kuma sai Almasihu ya samu kafuwa cikinku.
20 Vellem autem esse apud vos modo, et mutare vocem meam: quoniam confundor in vobis.
Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canza muryata, domin ina damuwa a kanku kwarai.
21 Dicite mihi qui sub lege vultis esse: legem non legistis?
Ku gaya mani, ku da kuke marmarin ku zo karkashin shari'a, ba ku ji abin da shari'ar ta ce ba?
22 Scriptum est enim: Quoniam Abraham duos filios habuit: unum de ancilla, et unum de libera.
A rubuce yake cewa, Ibrahim yana da 'ya'ya maza biyu, daya dan baiwa ne, dayan kuma dan 'yantaciyar mace ne.
23 Sed qui de ancilla, secundum carnem natus est: qui autem de libera, per repromissionem:
Abin lura anan, dan baiwar an haife shi ta hanyar mutuntaka ne, amma dan 'yantaciyar macen, an haife shi ta wurin alkawari ne.
24 quae sunt per allegoriam dicta. Haec enim sunt duo testamenta. Unum quidem in monte Sina, in servitutem generans: quae est Agar:
Ana iya bayyana abubuwan nan a hanyar kwatanci kamar haka, wadannan mata na kama da alkawarai ne guda biyu. Dayan alkawarin daga dutsen Sinayi ne. Ta haifi 'ya'ya da ke bayi ne su. Ita ce Hajaratu.
25 Sina enim mons est in Arabia, qui coniunctus est ei, quae nunc est Ierusalem, et servit cum filiis suis.
Yanzu fa, Hajaratu ita ce dutsen Sinayi da ke Arebiya. Misali ce na Urushalima na yanzu, domin tana cikin bauta tare da 'ya'yanta.
26 Illa autem, quae sursum est Ierusalem, libera est, quae est mater nostra.
Amma Urushalima da ke bisa 'yantacciya ce, ita ce mahaifiyarmu.
27 Scriptum est enim: Laetare sterilis, quae non paris: erumpe, et clama, quae non parturis: quia multi filii desertae, magis quam eius, quae habet virum.
Kamar yadda yake a rubuce, “Ki yi murna, ke bakarariya, ke da ba ki taba haihuwa ba. Ki yi shewa na farinciki, ke da ba ki dandana haihuwan da ba. Domin 'ya'yan bakarariya da yawa suke, fiye da ta mace mai miji.”
28 Nos autem fratres secundum Isaac promissionis filii sumus.
Yanzu fa, 'yan'uwa, kamar yadda Ishaku yake, haka muke, wato 'ya'yan alkawari.
29 Sed quomodo tunc is, qui secundum carnem natus fuerat, persequebatur eum, qui secundum spiritum: ita et nunc.
A lokacin can, shi wanda aka haife shi ta hanyar mutuntaka ya tsananta wa wanda aka haife shi ta hanyar Ruhu. Haka yake har yanzu.
30 Sed quid dicit Scriptura? Eiice ancillam, et filium eius: non heres erit filius ancillae cum filio liberae.
Amma menene nassi ya ce? “Ka kori baiwar nan tare da danta. Domin dan baiwar nan ba za ya ci gado tare da dan macen nan da ke 'yantacciya ba.”
31 Itaque, fratres, non sumus ancillae filii, sed liberae: qua libertate Christus nos liberavit.
Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan baiwa ba ne, a maimakon haka, mu 'ya'yan macen nan ne da ke 'yantacciya.

< Galatas 4 >