< Corinthios Ii 6 >

1 Adiuvantes autem exhortamur ne in vacuum gratiam Dei recipiatis.
haka, tundashike muna aiki tare, na roke ku kar ku yi watsi da alherin Allah.
2 Ait enim: Tempore accepto exaudivi te, et in die salutis adiuvi te. Ecce nunc tempus acceptabile, ecce nunc dies salutis.
Domin ya ce, “A lokacin alheri na saurare ku, kuma a ranar ceto na agaje ku.” Yanzu ne fa, lokacin alheri. Duba, yanzu ne ranar ceto.
3 nemini dantes ullam offensionem, ut non vituperetur ministerium nostrum:
Ba mu sa sanadin faduwa a gaban kowannen ku, domin ba mu so hidimarmu ta zama marar amfani.
4 sed in omnibus exhibeamus nosmetipsos sicut Dei ministros in multa patientia, in tribulationibus, in necessitatibus, in angustiis,
Maimakon haka, mun tabbatar da kan mu ta wurin dukan ayyukanmu, cewa mu bayin Allah ne. Mu bayinsa ne ta wurin yawan jimiri, azaba, kunci, wahala,
5 in plagis, in carceribus, in seditionibus, in laboribus, in vigiliis, in ieiuniis,
duka, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, cikin yunwa,
6 in castitate, in scientia, in longanimitate, in suavitate, in Spiritu sancto, in charitate non ficta,
cikin tsarki, ilimi, hakuri, kirki, cikin Ruhu Mai tsarki, da sahihiyar kauna.
7 in verbo veritatis, in virtute Dei, per arma iustitiae a dextris, et a sinistris,
Mu bayinsa ne cikin kalmar gaskiya, cikin ikon Allah. Muna kuma da makamai na adalci, a hanun dama da hagu.
8 per gloriam, et ignobilitatem, per infamiam, et bonam famam: ut seductores, et veraces, sicut qui ignoti, et cogniti:
Muna aiki cikin daraja da rashin daraja, kushe da yabo. Ana zargin mu a kan mu mayaudara ne, duk da haka mu masu gaskiya ne.
9 quasi morientes, et ecce vivimus: ut castigati, et non mortificati:
Muna aiki kamar ba a san mu ba, gashi kuwa mu sanannu ne. Muna aiki kamar masu mutuwa-duba! -har yanzu muna raye. Muna aiki kamar wadanda aka hukunta, amma ba hukuncin kisa ba.
10 quasi tristes, semper autem gaudentes: sicut egentes, multos autem locupletantes: tamquam nihil habentes, et omnia possidentes.
Muna aiki kamar muna bakinciki, amma a koyaushe muna farinciki. Muna aiki kamar matalauta, amma muna azurta mutane dayawa. Muna aiki kamar ba mu da komai, amma mun mallaki komai.
11 Os nostrum patet ad vos, o Corinthii, cor nostrum dilatatum est.
Mun fada maku dukan gaskiyar, Korantiyawa, kuma zuciyar mu a bude ta ke.
12 Non angustiamini in nobis: angustiamini autem in visceribus vestris:
Ba mu kange zukatan ku ba, ku ne kuka kange zukatanku a gare mu.
13 eandem autem habentes remunerationem, tamquam filiis dico: dilatamini et vos.
Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku.
14 Nolite iugum ducere cum infidelibus. Quae enim participatio iustitiae cum iniquitate? Aut quae societas luci ad tenebras?
Kada ku yi cudanya da marasa bangaskiya. Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Ko kuma wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu?
15 Quae autem conventio Christi ad Belial? Aut quae pars fideli cum infideli?
Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? ko kuma me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya?
16 Quis autem consensus templo Dei cum idolis? Vos enim estis templum Dei vivi, sicut dicit Deus: Quoniam inhabitabo in illis, et inambulabo inter eos, et ero illorum Deus, et ipsi erunt mihi populus.
ko wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka? Domin kuwa mu haikali ne na Allah mai rai, kamar yadda Allah ya ce: ''Zan zauna a cikin su, in kuma yi tafiya a tsakanin su. Zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.”
17 Propter quod exite de medio eorum, et separamini, dicit Dominus, et immundum ne tetigeritis:
Sabili da haka, ''Ku fito daga cikin su, kuma ku zama kebabbu,'' in ji Ubangiji. ''Kada ku taba kazamin abu, zan kuma karbe ku.
18 et ego recipiam vos: et ero vobis in patrem, et vos eritis mihi in filios, et filias, dicit Dominus omnipotens.
Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama 'ya'ya maza da mata a gare ni,'' in ji Ubangiji Mai iko duka.

< Corinthios Ii 6 >