< Iohannem 14 >

1 Non turbetur cor vestrum. Creditis in Deum, et in me credite.
“Kada zuciyarku ta bachi. Kun gaskata da Allah, sai kuma ku gaskata da ni.
2 In domo Patris mei mansiones multæ sunt. si quo minus dixissem vobis: Quia vado parare vobis locum.
A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. Da ba haka ba, da na fada maku, domin zan tafi in shirya maku wuri.
3 Et si abiero, et præparavero vobis locum: iterum venio, et accipiam vos ad meipsum, ut ubi sum ego, et vos sitis.
In kuwa na je na shirya maku wuri, zan dawo in karbe ku zuwa wurina domin inda nake kuma ku kasance.
4 Et quo ego vado scitis, et viam scitis.
Kun san hanya inda zan tafi.”
5 Dicit ei Thomas: Domine, nescimus quo vadis: et quo modo possumus viam scire?
Toma ya ce wa Yesu, “Ubangiji, bamu san inda za ka tafi ba, yaya za mu san hanyar?”
6 Dicit ei Iesus: Ego sum via, et veritas, et vita. nemo venit ad Patrem, nisi per me.
Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai; Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.
7 Si cognovissetis me, et Patrem meum utique cognovissetis: et amodo cognoscetis eum, et vidistis eum.
Da kun san ni, da kun san Ubana kuma. Amma daga yanzu kun san shi, kuma kun gan shi.”
8 Dicit ei Philippus: Domine, ostende nobis Patrem, et sufficit nobis.
Filibus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu.”
9 Dicit ei Iesus: Tanto tempore vobiscum sum: et non cognovistis me? Philippe, qui videt me, videt et Patrem. Quomodo tu dicis: Ostende nobis Patrem?
Yesu ya ce masa, “Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban. Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'?
10 Non creditis quia ego in Patre, et Pater in me est? Verba, quæ ego loquor vobis, a me ipso non loquor. Pater autem in me manens, ipse fecit opera.
Baka gaskata cewa Ina cikin Uban, Uban kuma yana ciki na ba? Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba, amma Uban ne da yake zaune a ciki na yake yin ayyukansa.
11 Non creditis quia ego in Patre, et Pater in me est?
Ku gaskata ni cewa ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na, ko kuwa ku bada gaskiya domin ayyukan kansu.
12 Alioquin propter opera ipsa credite. Amen, amen dico vobis, qui credit in me, opera, quæ ego facio, et ipse faciet, et maiora horum faciet: quia ego ad Patrem vado.
“Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba.
13 Et quodcumque petieritis Patrem in nomine meo, hoc faciam: ut glorificetur Pater in Filio.
Duk abinda kuka roka da sunana, zan yi shi domin a daukaka Uban cikin Dan.
14 Si quid petieritis me in nomine meo, hoc faciam.
Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi.
15 Si diligitis me: mandata mea servate.
“Idan kuna kaunata, za ku kiyaye dokokina.
16 Et ego rogabo Patrem, et alium paraclitum dabit vobis, ut maneat vobiscum in æternum, (aiōn g165)
Sa, annan zan yi addu'a ga Uba, zai kuwa baku wani mai ta'aziya domin ya kasance tare daku har abada. (aiōn g165)
17 Spiritum veritatis, quem mundus non potest accipere, quia non videt eum, nec scit eum. vos autem cognoscetis eum: quia apud vos manebit, et in vobis erit.
Ruhun gaskiya. Wanda duniya ba zata iya karba ba, domin bata gan shi ba, ko ta san shi. Amma ku kun san shi, domin yana tare da ku, zai kuma kasance a cikin ku.
18 Non relinquam vos orphanos: veniam ad vos.
Ba zan barku ku kadai ba; zan dawo wurin ku.
19 Adhuc modicum: et mundus me iam non videt. Vos autem videtis me: quia ego vivo, et vos vivetis.
Sauran dan gajeren lokaci, duniya kuma ba zata ka ra gani na ba, amma ku kuna gani na. Saboda ina raye, kuma zaku rayu.
20 In illo die vos cognoscetis quia ego sum in Patre meo, et vos in me, et ego in vobis.
A wannan rana zaku sani ina cikin Ubana, ku kuma kuna ciki na, ni ma ina cikin ku.
21 Qui habet mandata mea, et servat ea: ille est, qui diligit me. Qui autem diligit me, diligetur a Patre meo: et ego diligam eum, et manifestabo ei meipsum.
Shi wanda yake da dokokina yake kuma bin su, shine ke kauna ta, kuma shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi, Ni ma kuma zan kaunace shi in kuma bayyana kaina gare shi.”
22 Dicit ei Iudas, non ille Iscariotes: Domine, quid factum est, quia manifestaturus es nobis tepisum, et non mundo?
Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce ma Yesu, “Ubangiji, meyasa za ka bayyana kanka a gare mu, ba ga duniya ba?”
23 Respondit Iesus, et dixit ei: Si quis diligit me, sermonem meum servabit, et Pater meus diliget eum, et ad eum veniemus, et mansionem apud eum faciemus:
Yesu ya amsa ya ce masa,”Kowa yake kauna ta, zai kiyaye maganata. Ubana kuwa zai kaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.
24 qui non diligit me, sermones meos non servat. Et sermonem, quem audistis, non est meus: sed eius, qui misit me, Patris.
Shi wanda baya kauna ta, ba ya kiyaye maganganuna. Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni take.
25 Hæc locutus sum vobis apud vos manens.
Na fada maku wadannan abubuwa, sa'adda nake tare da ku.
26 Paraclitus autem Spiritus sanctus, quem mittet Pater in nomine meo, ille vos docebit omnia, et suggeret vobis omnia, quæcumque dixero vobis.
Saidai, mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya maku kome, kuma zai tunashe ku dukan abinda na fada maku.
27 Pacem relinquo vobis, pacem meam do vobis: non quomodo mundus dat, ego do vobis. Non turbetur cor vestrum, neque formidet.
Na bar ku da salama; ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa Nake bayarwa ba. Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata.
28 Audistis quia ego dixi vobis: Vado, et venio ad vos. Si diligeretis me, gauderetis utique, quia vado ad Patrem: quia Pater maior me est.
Kun ji dai na fada maku, 'zan tafi, kuma Zan dawo gare ku'. Idan kuna kaunata, za ku yi farinciki domin za ni wurin Uban, gama Uban ya fi ni girma.
29 Et nunc dixi vobis prius quam fiat: ut cum factum fuerit, credatis.
Yanzu na fada maku kafin ya faru, domin idan ya faru, ku gaskata.
30 Iam non multa loquar vobiscum. venit enim princeps mundi huius, et in me non habet quidquam.
Ba zan kara magana mai yawa da ku ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Bashi da iko a kai na,
31 Sed ut cognoscat mundus quia diligo Patrem, et sicut mandatum dedit mihi Pater, sic facio. Surgite, eamus hinc.
amma domin duniya ta san cewa ina kaunar Uban, Ina yin daidai abinda Uban ya Umarce ni. Mu tashi mu tafi daga nan.

< Iohannem 14 >