< テモテへの手紙第一 1 >

1 私たちの救い主なる神と私たちの望みなるキリスト・イエスとの命令による、キリスト・イエスの使徒パウロから、
Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai cetonmu, da Almasihu Yesu begenmu,
2 信仰による真実のわが子テモテへ。父なる神と私たちの主なるキリスト・イエスから、恵みとあわれみと平安とがありますように。
zuwa ga Timoti, dana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah da Almasihu Yesu Ubangijinmu.
3 私がマケドニヤに出発するとき、あなたにお願いしたように、あなたは、エペソにずっととどまっていて、ある人たちが違った教えを説いたり、
Kamar yadda na nanata maka ka yi, da zan tafi Makidoniya cewa, ka dakata a Afisa domin ka umarci wadansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam.
4 果てしのない空想話と系図とに心を奪われたりしないように命じてください。そのようなものは、論議を引き起こすだけで、信仰による神の救いのご計画の実現をもたらすものではありません。
Kada su bata lokacinsu wajen sauraron tatsunniyoyi da kididdiga marar iyaka. Wannan yana haddasa gardandami, maimakon taimakawa shirin Allah, da ke ta wurin bangaskiya.
5 この命令は、きよい心と正しい良心と偽りのない信仰とから出て来る愛を、目標としています。
Manufar shari'a kuwa kauna ce daga tsabtacciyar zuciya, da tsatstsakan lamiri, da kuma sahihiyar bangaskiya.
6 ある人たちはこの目当てを見失い、わき道にそれて無益な議論に走り、
Wadansu sun kauce daga tafarkin sun juya zuwa ga maganganun banza.
7 律法の教師でありたいと望みながら、自分の言っていることも、また強く主張していることについても理解していません。
Suna so su zama malaman sha'ria, amma basu fahimci abin da suke fada ba ko abin da suka tsaya akai.
8 しかし私たちは知っています。律法は、もし次のことを知っていて正しく用いるならば、良いものです。
Amma mun sani shari'a tana da kyau idan an yi amfani da ita bisa ga ka'ida.
9 すなわち、律法は、正しい人のためにあるのではなく、律法を無視する不従順な者、不敬虔な罪人、汚らわしい俗物、父や母を殺す者、人を殺す者、
Gama mun san wannan, shari'a ba domin mai adalci take ba, amma domin marasa bin doka, mutane masu tawaye, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa Allah, da masu sabo. An bada shari'a domin masu kisan iyaye maza da iyaye mata, da masu kisan kai,
10 不品行な者、男色をする者、人を誘拐する者、うそをつく者、偽証をする者などのため、またそのほか健全な教えにそむく事のためにあるのです。
Domin fasikai da 'yan ludu, domin masu satar mutane su kai su bauta, domin makaryata, da masu shaidar zur, da kuma dukan abin da ke gaba da amintaccen umarni.
11 祝福に満ちた神の、栄光の福音によれば、こうなのであって、私はその福音をゆだねられたのです。
Wannan umarni bisa ga daukakkiyar bisharar Allah ne mai albarka, wadda aka bani amana.
12 私は、私を強くしてくださる私たちの主キリスト・イエスに感謝をささげています。なぜなら、キリストは、私をこの務めに任命して、私を忠実な者と認めてくださったからです。
Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijimu. wanda ya karfafa ni, gama ya karbe ni amintacce, ya sani cikin hidimarsa.
13 私は以前は、神をけがす者、迫害する者、暴力をふるう者でした。それでも、信じていないときに知らないでしたことなので、あわれみを受けたのです。
Dama can ni mai sabo ne, mai tsanantawa kuma dan ta'adda. Amma duk da haka aka yi mani jinkai domin na yi su cikin jahilci da rashin bangaskiya.
14 私たちの主の、この恵みは、キリスト・イエスにある信仰と愛とともに、ますます満ちあふれるようになりました。
Amma alherin Ubangijinmu ya kwararo mani tare da bangaskiya, da kauna da ke cikin Almasihu Yesu.
15 「キリスト・イエスは、罪人を救うためにこの世に来られた。」ということばは、まことであり、そのまま受け入れるに値するものです。私はその罪人のかしらです。
Wannan bishara amintacciya ce, ta isa kowa ya karba, cewa Almasihu Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu zunubi, a cikinsu kuwa ni ne mafi lalacewa.
16 しかし、そのような私があわれみを受けたのは、イエス・キリストが、今後彼を信じて永遠のいのちを得ようとしている人々の見本にしようと、まず私に対してこの上ない寛容を示してくださったからです。 (aiōnios g166)
Saboda haka ne na sami jinkai, domin ta wurina ni na farko, a nuna hakurin Yesu Almasihu. Ya yi wannan domin in zama misali ga wadanda za su bada gaskiya zuwa rai madawwami. (aiōnios g166)
17 どうか、世々の王、すなわち、滅びることなく、目に見えない唯一の神に、誉れと栄えとが世々限りなくありますように。アーメン。 (aiōn g165)
Yanzu, ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, boyayye, Allah makadaici girma, da daukaka su tabbata a gare shi har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
18 私の子テモテよ。以前あなたについてなされた預言に従って、私はあなたにこの命令をゆだねます。それは、あなたがあの預言によって、信仰と正しい良心を保ち、勇敢に戦い抜くためです。
Ina danka wannan umarni gareka, dana, Timoti. Ina haka ne bisa ga anabcin da aka yi a baya game da kai, domin ka shiga yaki mai kyau.
19 ある人たちは、正しい良心を捨てて、信仰の破船に会いました。
Ka yi wannan domin ka zama da bangaskiya da kyakkyawan lamiri. Wadansu mutane sun ki sauraron wannan suka yi barin bangaskiyarsu.
20 その中には、ヒメナオとアレキサンデルがいます。私は、彼らをサタンに引き渡しました。それは、神をけがしてはならないことを、彼らに学ばせるためです。
Kamar su Himinayus da Iskandari, wadanda na bada su ga shaidan domin su horu su koyi kin yi sabo.

< テモテへの手紙第一 1 >