< ローマ人への手紙 1 >

1 キリスト・イエスの僕、神の福音のために選び別たれ、召されて使徒となったパウロから
Bulus, bawan Yesu Almasihu, kirayayye ya zama manzo, kuma kebabbe domin bisharar Allah.
2 この福音は、神が、預言者たちにより、聖書の中で、あらかじめ約束されたものであって、
Wannan itace bisharar da ya alkawarta tuntuni ta wurin annabawansa ta wurin tsarkakakkun littattafan sa.
3 御子に関するものである。御子は、肉によればダビデの子孫から生れ、
Game da Dansa ne, haifaffe daga zuriyar Dauda ga zancen jiki.
4 聖なる霊によれば、死人からの復活により、御力をもって神の御子と定められた。これがわたしたちの主イエス・キリストである。
Ta wurin tashinsa daga mattatu aka aiyana shi ya zama Dan Allah ta wurin ikon Ruhu na tsarkakewa. Yesu Almasihu Ubangijimu.
5 わたしたちは、その御名のために、すべての異邦人を信仰の従順に至らせるようにと、彼によって恵みと使徒の務とを受けたのであり、
Ta wurinsa muka karbi alheri da manzanci sabo da biyayyar imani a cikin dukkan al'ummai, domin darajar sunansa.
6 あなたがたもまた、彼らの中にあって、召されてイエス・キリストに属する者となったのである
cikin wadannan al'ummai kwa, ku ma an kiraku ku zama na Yesu Almasihu.
7 ローマにいる、神に愛され、召された聖徒一同へ。わたしたちの父なる神および主イエス・キリストから、恵みと平安とが、あなたがたにあるように。
Wannan wasika ga dukkanku ne da kuke cikin Roma, kaunatattu na Allah, kirayayyun mutane tsarkakakku. Bari alheri ya kasance tare daku, da salama daga Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu.
8 まず第一に、わたしは、あなたがたの信仰が全世界に言い伝えられていることを、イエス・キリストによって、あなたがた一同のために、わたしの神に感謝する。
Abu na farko dai ina yi wa Allah na godiya ta wurin Yesu Almasihu domin ku duka, domin kuwa ana labarta bangaskiyarku ko ina a cikin dukkan duniya.
9
Domin kuwa Allah shi ne shaida ta, wanda nake bautawa a cikin ruhuna a cikin bisharar Dansa, yadda a koyaushe na ke ambaton ku.
10 わたしは、祈のたびごとに、絶えずあなたがたを覚え、いつかは御旨にかなって道が開かれ、どうにかして、あなたがたの所に行けるようにと願っている。このことについて、わたしのためにあかしをして下さるのは、わたしが霊により、御子の福音を宣べ伝えて仕えている神である。
A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah.
11 わたしは、あなたがたに会うことを熱望している。あなたがたに霊の賜物を幾分でも分け与えて、力づけたいからである。
Gama ina marmarin ganin ku, domin in baku wata baiwa ta ruhaniya, domin in karfafa ku.
12 それは、あなたがたの中にいて、あなたがたとわたしとのお互の信仰によって、共に励まし合うためにほかならない。
Wato ina dokin in sami cikakkiyar karfafawa a cikin ku, ta wurin bangaskiyar junanmu, wato tawa da taku.
13 兄弟たちよ。このことを知らずにいてもらいたくない。わたしはほかの異邦人の間で得たように、あなたがたの間でも幾分かの実を得るために、あなたがたの所に行こうとしばしば企てたが、今まで妨げられてきた。
Yanzu fa bana so ku rasa sani, yan'uwa, sau da yawa nake yin niyyar zuwa wurinku, amma har yanzu hakan din bata samu ba. Na so yin hakan din ne don in sami 'ya'ya na ruhu a cikinku kamar dai yadda ya ke a sauran Al'ummai.
14 わたしには、ギリシヤ人にも未開の人にも、賢い者にも無知な者にも、果すべき責任がある。
Ina dauke da nawayar Hellinawa da ta sauran jama'a, masu hikima da marasa hikima.
15 そこで、わたしとしての切なる願いは、ローマにいるあなたがたにも、福音を宣べ伝えることなのである。
Don a shirye na ke in sanar da bishara a gare ku, ku da kuke cikin Roma.
16 わたしは福音を恥としない。それは、ユダヤ人をはじめ、ギリシヤ人にも、すべて信じる者に、救を得させる神の力である。
Don kuwa ni ba na jin kunyar yin bishara, don ita ce ikon Allah don samun ceto ga duk wanda ya gaskata, da farko dai Yahudawa kana kuma Hellinawa,
17 神の義は、その福音の中に啓示され、信仰に始まり信仰に至らせる。これは、「信仰による義人は生きる」と書いてあるとおりである。
Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, “Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya.”
18 神の怒りは、不義をもって真理をはばもうとする人間のあらゆる不信心と不義とに対して、天から啓示される。
Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su.
19 なぜなら、神について知りうる事がらは、彼らには明らかであり、神がそれを彼らに明らかにされたのである。
Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri.
20 神の見えない性質、すなわち、神の永遠の力と神性とは、天地創造このかた、被造物において知られていて、明らかに認められるからである。したがって、彼らには弁解の余地がない。 (aïdios g126)
Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja. (aïdios g126)
21 なぜなら、彼らは神を知っていながら、神としてあがめず、感謝もせず、かえってその思いはむなしくなり、その無知な心は暗くなったからである。
Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta.
22 彼らは自ら知者と称しながら、愚かになり、
Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye.
23 不朽の神の栄光を変えて、朽ちる人間や鳥や獣や這うものの像に似せたのである。
Sun musanya daukakar Allah madawwami da ta kamannin abubuwan da basa dawwama, kamar mutum, da tsuntsaye, da dabbobi masu kafafu hurhudu, da masu jan ciki.
24 ゆえに、神は、彼らが心の欲情にかられ、自分のからだを互にはずかしめて、汚すままに任せられた。
Saboda haka Allah ya bashe su ga sha'awoyin kazantar zukatansu, su wulakantar da jukunansu a junansu.
25 彼らは神の真理を変えて虚偽とし、創造者の代りに被造物を拝み、これに仕えたのである。創造者こそ永遠にほむべきものである、アァメン。 (aiōn g165)
Sune suka musanya gaskiyar Allah da karya, Kuma suke sujada da bauta ga halittaccen abu, maimakon Mahaliccin, Wanda yake abin yabo har abada. Amin. (aiōn g165)
26 それゆえ、神は彼らを恥ずべき情欲に任せられた。すなわち、彼らの中の女は、その自然の関係を不自然なものに代え、
Saboda haka Allah ya bashe su, ga sha'awowin su na lalata da wulakanci, har matansu suka canza ka'idar jima'i da aka saba zuwa madigo mace da mace.
27 男もまた同じように女との自然の関係を捨てて、互にその情欲の炎を燃やし、男は男に対して恥ずべきことをなし、そしてその乱行の当然の報いを、身に受けたのである。
Mazajensu ma suka sauya ka'idar jima'i tsakanin mace da miji zuwa namiji da namiji suna yin aikin lalata. Maza su na kwana da maza suna aikata aikin ban kyama, suna kuwa girbe sakamakon aiknsu na ban kyama.
28 そして、彼らは神を認めることを正しいとしなかったので、神は彼らを正しからぬ思いにわたし、なすべからざる事をなすに任せられた。
Tunda shike ba su amince da Allah a cikkin al'amuransu ba, Allah ya bashe su ga bataccen hankalinsu, su aikata wadannan munanan abubuwa.
29 すなわち、彼らは、あらゆる不義と悪と貪欲と悪意とにあふれ、ねたみと殺意と争いと詐欺と悪念とに満ち、また、ざん言する者、
Suna cike da dukkan rashin adalci, mugunta, kyashi, keta, kuma cike da kishi, kisan kai, tarzoma, makirci, da kuma munanan manufafofi.
30 そしる者、神を憎む者、不遜な者、高慢な者、大言壮語する者、悪事をたくらむ者、親に逆らう者となり、
Masu gulma da kage, makiyan Allah. Masu tada zaune tsaye, masu taurin kai, da ruba, masu kaga kowadanne miyagun abubuwa, kuma masu kin yin biyayya ga iyayensu.
31 無知、不誠実、無情、無慈悲な者となっている。
Masu duhun zuciya; masu cin amana, marasa soyayya, da kuma rashin tausayi.
32 彼らは、こうした事を行う者どもが死に価するという神の定めをよく知りながら、自らそれを行うばかりではなく、それを行う者どもを是認さえしている。
Suna sane da tsarin Allah cewa masu yin irin wadannan al'amura sun cancanci hukuncin mutuwa. Ba kuwa yin wadannan abubuwan ka dai suke yi ba, harma goyon bayan masu yinsu suke yi.

< ローマ人への手紙 1 >