< 士師記 11 >

1 さてギレアデびとエフタは強い勇士であったが遊女の子で、エフタの父はギレアデであった。
Yefta mutumin Gileyad, jarumi ne ƙwarai. Mahaifinsa ne Gileyad; mahaifiyar kuwa karuwa ce.
2 ギレアデの妻も子供を産んだが、その妻の子供たちが成長したとき、彼らはエフタを追い出して彼に言った、「あなたはほかの女の産んだ子だから、わたしたちの父の家を継ぐことはできません」。
Matar Gileyad ta haifa masa’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”
3 それでエフタはその兄弟たちのもとから逃げ去って、トブの地に住んでいると、やくざ者がエフタのもとに集まってきて、彼と一緒に出かけて略奪を事としていた。
Saboda haka Yefta ya tsere daga’yan’uwansa ya zauna a ƙasar Tob, inda waɗansu’yan iska suka kewaye shi suka bi shi.
4 日がたって後、アンモンの人々はイスラエルと戦うことになり、
Ana nan, sa’ad da Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa hari,
5 アンモンの人々がイスラエルと戦ったとき、ギレアデの長老たちは行ってエフタをトブの地から連れてこようとして、
dattawan Gileyad suka je suka nemo Yefta daga ƙasar Tob.
6 エフタに言った、「きて、わたしたちの大将になってください。そうすればわたしたちはアンモンの人々と戦うことができます」。
Suka ce masa, “Ka zo ka zama mana shugaba, don mu yaƙi Ammonawa.”
7 エフタはギレアデの長老たちに言った、「あなたがたはわたしを憎んで、わたしの父の家から追い出したではありませんか。しかるに今あなたがたが困っている時とはいえ、わたしのところに来るとはどういうわけですか」。
Yefta ya ce musu, “Ba kun ƙi ni kuka kuma kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuke zuwa wurina yanzu sa’ad da kuke cikin wahala?”
8 ギレアデの長老たちはエフタに言った、「それでわたしたちは今、あなたに帰ったのです。どうぞ、わたしたちと一緒に行って、アンモンの人々と戦ってください。そしてわたしたちとギレアデに住んでいるすべてのものとのかしらになってください」。
Mutanen Gileyad suka ce masa, “Duk da haka, muna juyo wajenka yanzu, ka zo tare da mu mu yaƙi Ammonawa, za ka kuma zama shugaban duk wanda yake zama a Gileyad.”
9 エフタはギレアデの長老たちに言った、「もしあなたがたが、わたしをつれて帰って、アンモンの人々と戦わせるとき、主が彼らをわたしにわたされるならば、わたしはあなたがたのかしらとなりましょう」。
Yefta ya ce, “A ce kun dawo da ni in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna, zan zama shugabanku?”
10 ギレアデの長老たちはエフタに言った、「主はあなたとわたしたちの間の証人です。わたしたちは必ずあなたの言われるとおりにしましょう」。
Dattawan Gileyad suka ce, “Ubangiji ne shaidanmu; za mu yi duk abin da ka ce.”
11 そこでエフタはギレアデの長老たちと一緒に行った。民は彼を立てて自分たちのかしらとし、大将とした。それでエフタはミヅパで、自分の言葉をことごとく主の前に述べた。
Saboda haka Yefta ya tafi tare da dattawan Gileyad, mutanen kuwa suka naɗa shi shugabansu da kuma sarkinsu. Ya kuwa maimaita dukan maganarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.
12 かくてエフタはアンモンの人々の王に使者をつかわして言った、「あなたはわたしとなんのかかわりがあって、わたしのところへ攻めてきて、わたしの国と戦おうとするのですか」。
Sa’an nan Yefta ya aiki jakadu zuwa wurin sarkin Ammonawa su tambaya, “Me ya haɗa ka da ni, da ka kawo wa ƙasata yaƙi?”
13 アンモンの人々の王はエフタの使者に答えた、「昔、イスラエルがエジプトから上ってきたとき、アルノンからヤボクに及び、またヨルダンに及ぶわたしの国を奪い取ったからです。それゆえ今、穏やかにそれを返しなさい」。
Sarkin Ammonawa ya ce wa jakadu, “Sa’ad da Isra’ilawa suka fito daga Masar, sun ƙwace mini ƙasa tun daga Arnon zuwa Yabbok, har zuwa Urdun. Yanzu ka mayar mini ita cikin salama.”
14 エフタはまた使者をアンモンの人々の王につかわして、
Yefta ya sāke aikan jakadu wurin sarki,
15 言わせた、「エフタはこう申します、『イスラエルはモアブの地も、またアンモンの人々の地も取りませんでした。
yana cewa, “Ga abin da Yefta yake faɗi, Isra’ila ba tă ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.
16 イスラエルはエジプトから上ってきたとき、荒野をとおって紅海にいたり、カデシにきました。
Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku har suka zo Kadesh.
17 そしてイスラエルは使者をエドムの王につかわして「どうぞ、われわれにあなたの国を通らせてください」と言わせましたが、エドムの王は聞きいれませんでした。また同じように人をモアブの王につかわしたが、彼も承諾しなかったので、イスラエルはカデシにとどまりました。
Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.
18 それから荒野をとおって、エドムの地とモアブの地を回り、モアブの地の東部に達し、アルノンの向こうに宿営しましたがモアブの領域には、はいりませんでした。アルノンはモアブの境だからです。
“Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.
19 次にイスラエルはヘシボンの王すなわちアモリびとの王シホンに使者をつかわし、シホンに向かって「どうぞ、われわれにあなたの国をとおって、われわれの目的地へ行かせてください」と言わせました。
“Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga Sihon sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon, ta ce masa, ‘Ka bar mu mu ratsa ƙasarka mu wuce zuwa wurinmu.’
20 ところがシホンはイスラエルを信ぜず、その領域を通らせないばかりか、かえってすべての民を集めてヤハヅに陣を取り、イスラエルと戦いましたが、
Sihon dai, bai amince da Isra’ila su ratsa ƙasarsa ba. Ya tattara dukan mutanensa suka yi sansani a Yahza suka kuwa yaƙi Isra’ila.
21 イスラエルの神、主はシホンとそのすべての民をイスラエルの手にわたされたので、イスラエルは彼らを撃ち破って、その土地に住んでいたアモリびとの地をことごとく占領し、
“Sa’an nan Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da Sihon da dukan mutanensa a hannun Isra’ila, suka kuwa ci nasara a kansu. Isra’ila ta ƙwace dukan ƙasar Amoriyawa da suke zaune a ƙasar,
22 アルノンからヤボクまでと、荒野からヨルダンまで、アモリびとの領域をことごとく占領しました。
suka ƙwace dukan yankin Amoriyawa tun daga ƙasar Arnon zuwa Yabbok, daga hamada har zuwa Urdun.
23 このようにイスラエルの神、主はその民イスラエルの前からアモリびとを追い払われたのに、あなたはそれを取ろうとするのですか。
“To, da yake Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya kori Amoriyawa a gaban mutanensa Isra’ila, wane’yanci kake da shi da za ka karɓe ta?
24 あなたは、あなたの神ケモシがあなたに取らせるものを取らないのですか。われわれはわれわれの神、主がわれわれの前から追い払われたものの土地を取るのです。
Ba za ka karɓi abin da allahnka Kemosh ya ba ka ba? Haka mu ma, duk abin da Ubangiji Allahnmu ya riga ya ba mu, za mu mallake shi.
25 あなたはモアブの王チッポルの子バラクにまさる者ですか。バラクはかつてイスラエルと争ったことがありますか。かつて彼らと戦ったことがありますか。
Ka fi Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne? Ka taɓa ji ya yi hamayya da Isra’ila ko yă yi yaƙi da su?
26 イスラエルはヘシボンとその村里に住み、またアロエルとその村里およびアルノンの岸に沿うすべての町々に住むこと三百年になりますが、あなたがたはどうしてその間にそれを取りもどさなかったのですか。
Shekara ɗari uku Isra’ilawa suka yi zamansu a Heshbon, Arower da ƙauyukan kewayenta da dukan biranen da suke gefen Arnon. Me ya sa ba ka karɓe su a lokacin ba?
27 わたしはあなたに何も悪い事をしたこともないのに、あなたはわたしと戦って、わたしに害を加えようとします。審判者であられる主よ、どうぞ、きょう、イスラエルの人々とアンモンの人々との間をおさばきください』」。
Ban yi maka laifi ba, amma kana musguna mini ta wurin kawo mini hari. Bari Ubangiji yă zama Alƙali, yă yanke hukunci tsakani Isra’ilawa da Ammonawa.”
28 しかしアンモンの人々の王はエフタが言いつかわした言葉をききいれなかった。
Duk da haka sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika ba.
29 時に主の霊がエフタに臨み、エフタはギレアデおよびマナセをとおって、ギレアデのミヅパに行き、ギレアデのミヅパから進んでアンモンの人々のところに行った。
Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Yefta. Sai ya haye Gileyad da Manasse, ya ratsa ta Mizfa zuwa Gileyad, daga can kuma ya kai wa Ammonawa hari.
30 エフタは主に誓願を立てて言った、「もしあなたがアンモンの人々をわたしの手にわたされるならば、
Yefta kuwa ya yi wa’adi da Ubangiji ya ce, “In ka ba da Ammonawa a hannuwana,
31 わたしがアンモンの人々に勝って帰るときに、わたしの家の戸口から出てきて、わたしを迎えるものはだれでも主のものとし、その者を燔祭としてささげましょう」。
duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don yă tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙi da Ammonawa, zai zama na Ubangiji, zan miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”
32 エフタはアンモンの人々のところに進んで行って、彼らと戦ったが、主は彼らをエフタの手にわたされたので、
Sa’an nan Yefta ya haye zuwa wajen Ammonawa don yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuwansa.
33 アロエルからミンニテの附近まで、二十の町を撃ち敗り、アベル・ケラミムに至るまで、非常に多くの人を殺した。こうしてアンモンの人々はイスラエルの人々の前に攻め伏せられた。
Ya hallaka birane ashirin tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-Keramim. Haka Isra’ila ta cinye Ammonawa ƙaf.
34 やがてエフタはミヅパに帰り、自分の家に来ると、彼の娘が鼓をもち、舞い踊って彼を出迎えた。彼女はエフタのひとり子で、ほかに男子も女子もなかった。
Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi,’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko’ya.
35 エフタは彼女を見ると、衣を裂いて言った、「ああ、娘よ、あなたは全くわたしを打ちのめした。わたしを悩ますものとなった。わたしが主に誓ったのだから改めることはできないのだ」。
Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito!’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.”
36 娘は言った、「父よ、あなたは主に誓われたのですから、主があなたのために、あなたの敵アンモンの人々に報復された今、あなたが言われたとおりにわたしにしてください」。
Ta ce, “Mahaifina, idan ka riga ka yi wa Ubangiji magana, sai ka yi da ni yadda ka yi alkawari, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa.”
37 娘はまた父に言った、「どうぞ、この事をわたしにさせてください。すなわち二か月の間わたしをゆるし、友だちと一緒に行って、山々をゆきめぐり、わたしの処女であることを嘆かせてください」。
Sai ta kuma ce, “Sai dai, ka biya mini wannan bukata guda. Ka ba ni wata biyu in yi ta yawo da ni da ƙawayena a kan duwatsu mu yi makoki, domin ba zan yi aure ba.”
38 エフタは「行きなさい」と言って、彼女を二か月の間、出してやった。彼女は友だちと一緒に行って、山の上で自分の処女であることを嘆いたが、
Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba.
39 二か月の後、父のもとに帰ってきたので、父は誓った誓願のとおりに彼女におこなった。彼女はついに男を知らなかった。
Bayan watanni biyu ɗin sai ta komo wurin mahaifinta ya kuwa yi da ita yadda ya yi wa’adi. Ita kuwa ba tă taɓa san namiji ba. Wannan ya zama al’ada a Isra’ila,
40 これによって年々イスラエルの娘たちは行って、年に四日ほどギレアデびとエフタの娘のために嘆くことがイスラエルのならわしとなった。
cewa kowace shekara’yan mata sukan fita kwana huɗu don yin bikin tunawa da’yar Yefta mutumin Gileyad.

< 士師記 11 >