< ホセア書 9 >

1 イスラエルよ異邦人のごとく喜びすさむ勿れなんぢ淫行をなして汝の神を離る汝すべての麥の打塲にて賜はる淫行の賞賜を愛せり
Kada ku yi farin ciki, ya Isra’ila; kada ku yi murna kamar waɗansu al’ummai. Gama kun yi rashin aminci ga Allahnku; kuna son hakkokin karuwa a kowace masussuka.
2 打場と酒榨とはかれらを養はじ亦あたらしき酒もむなしくならん
Masussukai da wuraren matsin inabi ba za su ciyar da mutane ba; sabon ruwan inabi zai kāsa musu.
3 かれらはヱホバの地にとどまらずエフライムはエジプトに歸りアッスリヤにて汚穢たる物を食はん
Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba; Efraim zai koma Masar yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.
4 彼等はヱホバにむかひて酒を灌ぐべき者にあらずその祭物はヱホバの悦びたまふ所にあらずかれらの犠牲は喪に居もののパンのごとし凡てこれを食ふものは汚るべし彼等のパンは只おのが食ふためにのみ用ゐべくしてヱホバの家に入るべきにあらず
Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba, ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba. Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki; duk wanda ya ci su zai ƙazantu. Wannan abincin zai zama na kansu ne; ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba.
5 なんぢら集會の日とヱホバの節會の日に何をなさんとするや
Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar bukukkuwarku, a ranakun bikin Ubangiji?
6 視よかれら滅亡の故によりて去ゆきぬエジプトかれらをあつめメンピスかれらを葬らん蒺藜かれらが銀の寳物を獲いばら彼らの天幕に蔓らん
Ko da sun kuɓuta daga hallaka, Masar za tă tattara su, Memfis kuma za tă binne su. Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu, ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.
7 刑罰の日きたり應報の日きたれりイスラエルこれを知ん預言者は愚なるもの霊に感じたるものは狂へるものなりこれ汝の惡おほく汝の怨恨おほいなるに因る
Kwanakin hukunci suna zuwa, kwanakin ba da lissafi suna a kusa. Bari Isra’ila su san da wannan. Saboda zunubanku sun yi yawa ƙiyayyarku kuma ta yi yawa, har ake ɗauka annabi wawa ne, mutumin da aka iza kuwa mahaukaci.
8 エフライムは我が神にならべて他の神をも佇望めり預言者の一切の途は鳥を捕ふる者の網のごとく且その神の室の中にて怨恨を懐けり
Annabi, tare da Allahna, su ne masu tsaro a bisa Efraim, duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi, da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa.
9 かれらはギベアの日のごとく甚だしく惡き事を行へりヱホバはその惡をこころに記てその罪を罰したまはん
Sun nutse da zurfi cikin lalaci, kamar a kwanakin Gibeya. Allah zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta su saboda zunubansu.
10 在昔われイスラエルを見ること荒野の葡萄のごとく汝らの先祖等を看ること無花果樹の始にむすべる最先の果の如くなししに彼等はバアルペオルにゆきて身を恥辱にゆだねその愛する物とともに憎むべき者とはなれり
“Sa’ad da na sami Isra’ila, ya zama kamar samun inabi a hamada; sa’ad da na ga kakanninku, ya zama kamar ganin’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure. Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor, suka keɓe kansu wa gumaka bankunya sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.
11 エフライムの榮光は鳥のごとく飛さらん即ち產ことも孕むことも妊娠こともなかるべし
Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu, ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki.
12 假令かれら子等を育つるとも我その子を喪ひて遺る人なきにいたらしめん我が離るる時かれらの禍大なる哉
Ko da sun yi renon’ya’ya, zan sa su yi baƙin cikin kowannensu. Kaitonsu sa’ad da na juya musu baya!
13 われエフライムを美地に植てツロのごとくなししかどもエフライムはその子等を携へいだして人を殺すに付さんとす
Na ga Efraim, kamar birnin Taya, da aka kafa a wuri mai daɗi. Amma Efraim zai fitar da’ya’yansu ga masu yanka.”
14 ヱホバよ彼らに與へたまへ汝なにを與へんとしたまふや孕まざる胎と乳なき乳房とを與へたまへ
Ka ba su, ya Ubangiji Me za ka ba su? Ka ba su mahaifar da za su yi ɓarin ciki da busassun nono.
15 かれらが凡の惡はギルガルにあり此故に我かしこにて之を惡めりその行爲あしければ我が家より逐いだし重て愛することをせじその牧伯等はみな悖れる者なり
“Saboda dukan muguntarsu a Gilgal, na ƙi su a can. Saboda ayyukansu na zunubi, zan kore su daga gidana. Ba zan ƙara ƙaunace su ba; dukan shugabanninsu’yan tawaye ne.
16 エフライムは撃れその根はかれて果を結ぶまじ若し產ことあらば我その胎なる愛しむ實を殺さん
An ka da Efraim, saiwarsu ta bushe, ba sa ba da amfani. Ko da sun haifi’ya’ya zan kashe waɗanda suka fi ƙauna.”
17 かれら聽從はざるによりて我が神これを棄たまふべしかれらは列國民のうちに流離人とならん
Allahna zai ƙi su saboda ba su yi masa biyayya ba; za su zama masu yawo a cikin al’ummai.

< ホセア書 9 >