< Atti 20 >

1 ORA, dopo che fu cessato il tumulto, Paolo, chiamati a sè i discepoli, ed abbracciatili, si partì per andare in Macedonia.
Bayan da rikici ya kare, Bulus ya aika a kira al'majiran, ya karfafa su. Sa'annan ya yi bankwana da su, ya tashi zai tafi Makidoniya.
2 E, dopo esser passato per quelle parti, ed averli con molte parole confortati, venne in Grecia.
Bayan ya ratsa cikin lardunan yana yi wa masu bi gargadi sosai, sai ya zo kasar Helenawa.
3 [Dove] quando fu dimorato tre mesi, essendogli poste insidie da' Giudei, se fosse navigato in Siria, il parer fu che ritornasse per la Macedonia.
Sa'adda ya yi wata uku a wurin, Yahudawa suka kulla masa makirci, yayin da yake shirin hawa Jirgi zuwa Suriya, sai ya canza ra'ayi ya koma ta Makidoniya.
4 Or Sopatro Berreese l'accompagnò fino in Asia; e de' Tessalonicesi, Aristarco, e Secondo, e Gaio Derbese, e Timoteo; e di que' d'Asia, Tichico, e Trofimo.
Masu yi wa Bulus rakiyar zuwa yankin Asiya sun hada da Sobatarus dan Burus daga Biriya; Gayus mutumin Derbe; Timoti da Aristakus da Sakundus, dukansu masu bi ne daga Tasalonika; da Tikikus da Trofimus daga Asiya.
5 Costoro, andati innanzi, ci aspettarono in Troas.
Amma wadansu har suka rigaye mu, suka jira mu a Taruwasa.
6 E noi, dopo i giorni degli azzimi, partimmo da Filippi, e in capo di cinque giorni arrivammo a loro in Troas, dove dimorammo sette giorni.
Da muka shiga Jirgi daga Filibi bayan kwanakin Gurasa mara yisti; bayan kwanaki biyar muka iske su a Taruwasa; kwananmu bakwai a wurin.
7 E nel primo [giorno] della settimana, essendo i discepoli raunati per rompere il pane, Paolo, dovendo partire il giorno seguente, fece loro un sermone, e distese il ragionamento sino a mezzanotte.
A rana ta fari ga mako, da muka taru domin karya gurasa. Bulus ya yi wa masubi jawabi, don ya yi niyyar ya tafi da wayewar gari; jawabinsa ya kai har tsakar dare.
8 Or nella sala, ove eravamo raunati, vi erano molte lampane.
A benen da suka taru akwai fitilu da yawa.
9 Ed un certo giovanetto, [chiamato] per nome Eutico, sedendo sopra la finestra, sopraffatto da profondo sonno, mentre Paolo tirava il suo ragionamento in lungo, traboccato dal sonno, cadde giù dal terzo solaio, e fu levato morto.
Wani matashi mai suna Aftikos yana zaune a kan taga, barci mai nauyi ya dauke shi; da shike Bulus ya tsawaita jawabinsa, saurayin da shike barci mai nauyi ya dauke shi sai ya fado daga kan bene na uku aka dauke shi matacce.
10 Ma Paolo, sceso a basso, si gettò sopra lui, e l'abbracciò, e disse: Non tumultuate; perciocchè l'anima sua è in lui.
Sai Bulus ya sauka ya mike a bisansa ya rungume shi, sa'annan ya ce, “Kada kowa ya damu; domin yana darai bai mutu ba.”
11 Poi, essendo risalito, ed avendo rotto il pane, e preso cibo, dopo avere ancora lungamente ragionato sino all'alba, si dipartì così.
Sa'annan ya hawo kan bene domin cin gurasa tare da su, ya yi magana da su har gari ya waye daga nan ya bar su.
12 Or menarono [quivi] il fanciullo vivente, onde furono fuor di modo consolati.
Suka kawo saurayin da rai, sun sami ta'aziya ba kadan ba.
13 E noi, andati alla nave, navigammo in Asso, con intenzione di levar di là Paolo; perciocchè egli avea così determinato, volendo egli far quel cammino per terra.
Amma mu, da muka riga Bulus zuwa gun Jirgin, muka shiga zuwa Asos, mun shirya mu dauki Bulus a jirgi amma shi ya kudurta ya yi tafiya a kasa.
14 Ed avendolo scontrato in Asso, lo levammo, e venimmo a Mitilene.
Da muka sadu a Asos, mun dauke shi a Jirgin ruwa zuwa Mitilitus.
15 E, navigando di là, arrivammo il [giorno] seguente di rincontro a Chio; e il [giorno] appresso ammainammo verso Samo; e fermatici in Trogillio, il [giorno] seguente giungemmo a Mileto.
Bayan tashin mu daga can, washegari muka zo tsibirin Kiyos. Washegari kuma muka zo birnin Militus.
16 Perciocchè Paolo avea deliberato di navigare oltre ad Efeso, per non avere a consumar tempo in Asia; poichè egli si affrettava per essere, se gli era possibile, al giorno della Pentecosta in Gerusalemme.
Amma Bulus ya kudurta wucewa Afisa a Jirgi, don kada ya bata lokaci a Asiya, don yana sauri in ya yiwu ranar Fentekos ta same shi a Urushalima.
17 E DA Mileto mandò in Efeso, a far chiamare gli anziani della chiesa.
Daga Militus ya aika a kira masa dattawan iklisiyar Afisa.
18 E quando furono venuti a lui, egli disse loro: Voi sapete in qual maniera, dal primo giorno che io entrai nell'Asia, io sono stato con voi in tutto quel tempo;
Da suka zo wurinsa sai ya ce masu, “Ku da kanku kun san tun daga ranar da na sa kafata a Asiya, irin zaman da muka yi da kasancewar mu tare.
19 servendo al Signore, con ogni umiltà e con molte lagrime, e prove, le quali mi sono avvenute nelle insidie de' Giudei.
Na bauta wa Ubangiji da tawaliu har da hawaye, da wahalun da na sha saboda makircin Yahudawa.
20 Come io non mi son ritratto d'annunziarvi, ed insegnarvi, in pubblico, e per le case, cosa alcuna di quelle che son giovevoli;
Kun sani ban ji nauyin sanar da ku kowanne abu mai amfani ba, na bi ku gida gida ina koyar da ku abubuwa a sarari.
21 testificando a' Giudei, ed a' Greci, la conversione a Dio, e la fede nel Signor nostro Gesù Cristo.
Kunsan yadda na gargadi Yahudawa da Hellenawa game da tuba ga Allah da bangaskiya ga Ubangiji Yesu.
22 Ed ora, ecco, io, cattivato dallo Spirito, vo in Gerusalemme, non sapendo le cose che mi avverranno in essa.
Yanzu fa, gashi, zan tafi Urushalima, Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a fili dole in je, ban san abin da zai faru da ni a can ba.
23 Se non che lo Spirito Santo mi testifica per ogni città, dicendo che legami e tribolazioni mi aspettano.
Sai dai Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a kowanne gari cewa, sarkoki da wahalu suna jira na.
24 Ma io non fo conto di nulla; e la mia propria vita non mi è cara, purchè io adempia con allegrezza il mio corso, e il ministerio il quale ho ricevuto dal Signore Gesù, [che è] di testificar l'evangelo della grazia di Dio.
Amma ban dauka cewa raina yana da wani amfani gare ni ba, domin in cika tsere da hidimar da na karba daga wurin Ubangiji Yesu, ta shaidar bisharan alherin Allah.
25 Ed ora, ecco, io so che voi tutti, fra i quali io sono andato e venuto, predicando il regno di Dio, non vedrete più la mia faccia.
Yanzu fa, duba, na san dukanku, wadanda na yi wa wa'azin mulkin Allah, ba za ku kara gani na ba.
26 Perciò ancora, io vi protesto oggi, che io son netto del sangue di tutti.
Don haka na shaida maku a wannan rana, ba ni da alhakin jinin kowanne mutum.
27 Perciocchè io non mi son tratto indietro da annunziarvi tutto il consiglio di Dio.
Don banji nauyin sanar maku da dukan nufin Allah a gare ku ba.
28 Attendete dunque a voi stessi, ed a tutta la greggia, nella quale lo Spirito Santo vi ha costituiti vescovi, per pascer la chiesa di Dio, la quale egli ha acquistata col proprio sangue.
Saboda haka ku kula da kanku, da masubi da Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku shugabanni. Ku kula ku yi kiwon iklisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.
29 Perciocchè io so questo: che dopo la mia partita, entreranno fra voi de' lupi rapaci, i quali non risparmieranno la greggia.
Na sani cewa bayan tafiyata, kyarketai masu zafi za su shiga tsakaninku, kuma baza su rangwanta wa masubi ba.
30 E che d'infra voi stessi sorgeranno degli uomini che proporrano cose perverse, per trarsi dietro i discepoli.
Na sani har daga cikinku wadansu mazaje za su zo su fadi gurbattatun zantattuka, domin su janye almajirai zuwa gare su.
31 Perciò, vegliate, ricordandovi che per lo spazio di tre anni, giorno e notte, non son restato d' ammonir ciascuno con lagrime.
Saboda haka ku yi lura. Ku tuna da cewa shekara uku ban fasa yi wa kowannenku gargadi da hawaye dare da rana ba.
32 Ed al presente, fratelli, io vi raccomando a Dio, e alla parola della grazia di lui, il quale è potente da continuar d'edificarvi, e da darvi l'eredità con tutti i santificati.
Yanzu ina mika ku ga Allah, da maganar Alherinsa, wadda take da ikon gina ku ta kuma ba ku gado tare da dukan wadanda ke cikin kebabbu na Allah.
33 Io non ho appetito l'argento, nè l'oro, nè il vestimento di alcuno.
Ban yi kyashin azurfa, ko zinariya, ko tufafin wani ba.
34 E voi stessi sapete che queste mani hanno sovvenuto a' bisogni miei, e di coloro ch'erano meco.
Ku da kanku kun sani na yi aiki da hannuwana, na biya bukatu na da na wadanda ke tare da ni.
35 In ogni cosa vi ho mostrato che affaticandosi, si convengono così sopportar gl'infermi; e ricordarsi delle parole del Signore Gesù, il qual disse che più felice cosa è il dare che il ricevere.
Na zama maku abin koyi a kowace hanya game da yadda za ku taimaka wa nakasassu ta wurin aiki, da yadda za ku tuna da maganar Ubangiji Yesu, maganar da shi da kansa ya ce: ''Bayarwa tafi karba albarka.''
36 E quando ebbe dette queste cose, si pose in ginocchioni, ed orò con tutti loro.
Bayan da ya yi magana haka, ya durkusa ya yi addu'a tare da su duka.
37 E si fece da tutti un gran pianto; e gettatisi al collo di Paolo, lo baciavano;
Dukansu kuwa suka yi kuka mai tsannani, suka rungume shi kuma suka sunbace shi.
38 dolenti principalmente per la parola ch'egli avea detta, che non vedrebbero più la sua faccia. E l'accompagnarono alla nave.
Suka yi bakin ciki musamman domin abin da ya ce masu, ba za su kara ganinsa ba. Sai dukansu suka yi masa rakiya zuwa wurin jirgin ruwa.

< Atti 20 >