< Ru’uya ta Yohanna 20 >

1 Sai na ga mala'ika na saukowa daga sama. Yana da makullin rami marar iyaka, yana kuma da babar sarka a hannunsa. (Abyssos g12)
And I saw an Angel, descending from heaven, holding in his hand the key of the abyss and a great chain. (Abyssos g12)
2 Sai ya dauki tsohon macijin, wanda shine iblis, ko shaidan, ya daure shi shekaru dubu.
And he apprehended the dragon, the ancient serpent, who is the devil and Satan, and he bound him for a thousand years.
3 Ya jefa shi cikin rami marar iyaka, ya rufe shi ya kuma sa hatimi a bisansa. Hakan ya faru ne domin kada ya kara yaudarar al'ummai har sai bayan shekaru dubu. Bayan wannan, dole a sake shi na dan lokaci. (Abyssos g12)
And he cast him into the abyss, and he closed and sealed it, so that he would no longer seduce the nations, until the thousand years are completed. And after these things, he must be released for a brief time. (Abyssos g12)
4 Sa'annan na ga kursiyoyi. Wadanda ke zaune a bisansu sune wadanda aka ba ikon hukunci. Na kuma ga rayukan wadanda aka fille wa kai saboda shaidar Yesu da maganar Allah. Ba su yi wa dabban sujada ba ko siffarsa, suka ki su karbi alamar a goshinsu ko a hannu. Sun sake rayuwa, suka yi mulki tare da Kristi shekaru dubu.
And I saw thrones. And they sat upon them. And judgment was given to them. And the souls of those beheaded because of the testimony of Jesus and because of the Word of God, and who did not adore the beast, nor his image, nor accept his character on their foreheads or on their hands: they lived and they reigned with Christ for a thousand years.
5 Sauran matattun basu sake dawowa da rai ba har sai da shekaru dubu din suka cika. Wannan shine tashin matattu na fari.
The rest of the dead did not live, until the thousand years are completed. This is the First Resurrection.
6 Mai albarka ne mai tsarki ne kuma wanda yake da rabo cikin tashin matattu na fari! Mutuwa ta biyu ba ta da iko akan wadannan. Za su zama firistocin Allah da na Almasihu za su kuma yi mulki tare da shi shekaru dubu.
Blessed and holy is he who takes part in the First Resurrection. Over these the second death has no power. But they shall be priests of God and of Christ, and they shall reign with him for a thousand years.
7 Sa'adda shekaru dubu suka zo ga karshe, za a saki shaidan daga kurkukunsa.
And when the thousand years will have been completed, Satan shall be released from his prison,
8 Za ya fito domin ya yaudari al'ummai da ke kursuyoyi hudu na duniya, Gog da Magog ya tattara su domin yaki. Yawan su zai zama kamar yashin teku.
and he will go out and seduce the nations which are upon the four quarters of the earth, Gog and Magog. And he will gather them together for battle, those whose number is like the sand of the sea.
9 Suka bazu a fuskar duniya suka kuma kewaye sansanin masu ba da gaskiya, kaunataccen birni. Amma wuta ta sauko daga sama ta lankwame su.
And they climbed across the breadth of the earth, and they encompassed the camp of the Saints and the Beloved City. And fire from God descended from heaven and devoured them.
10 Shaidan, wanda ya yaudare su, aka jefa shi cikin korama ta farin wuta mai ci, inda aka jefa dabban da makaryacin annabin. Za su sha azaba dare da rana har abada abadin. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
And the devil, who seduced them, was cast into the pool of fire and sulphur, where both the beast and the false prophetess shall be tortured, day and night, forever and ever. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
11 Sai na ga babban kursiyi da wanda ke zaune a kansa. Duniya da sama suka guje wa fuskarsa, amma babu wurin da za su tafi.
And I saw a great white throne, and One sitting upon it, from whose sight earth and heaven fled, and no place was found for them.
12 Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu.
And I saw the dead, great and small, standing in view of the throne. And books were opened. And another Book was opened, which is the Book of Life. And the dead were judged by those things that had been written in the books, according to their works.
13 Teku ta ba da matattun dake cikinta. Mutuwa da hades suka ba da matattun da ke cikinsu, aka yi masu shari'a gwargwadon abin da suka yi. (Hadēs g86)
And the sea gave up the dead who were in it. And death and Hell gave up their dead who were in them. And they were judged, each one according to his works. (Hadēs g86)
14 Aka jefa mutuwa da hades cikin tafkin wuta. Wannan shine mutuwa ta biyu - tafkin wuta. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
And Hell and death were cast into the pool of fire. This is the second death. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin tafkin wuta. (Limnē Pyr g3041 g4442)
And whoever was not found written in the Book of Life was cast into the pool of fire. (Limnē Pyr g3041 g4442)

< Ru’uya ta Yohanna 20 >