< Mattiyu 15 >
1 Sai wadansu Farisawa da malamai suka zo wurin Yesu daga Urushalima. Su ka ce,
2 “Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.”
3 Yesu ya amsa masu ya ce, “Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al'adunku?
4 Domin Allah ya ce, 'Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka; 'Shi wanda ya yi muguwar magana ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lallai zai mutu.
5 Amma kun ce, “Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, “Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,'”
6 wannan mutum ba ya bukatar ya girmama mahaifinsa. Ta wannan hanya kun maida maganar Allah wofi saboda al'adunku.
7 Ku munafukai, daidai ne Ishaya ya yi annabci akan ku da ya ce,
8 “Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni.
9 Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu.”
10 Sai ya kira taron mutane zuwa gare shi ya ce masu, “Ku saurara ku fahimta,
11 ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum.”
12 Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?”
13 Yesu ya amsa ya ce, “Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta.
14 Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.”
15 Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ka bayyana wannan misali a garemu,”
16 Yesu ya ce, “Ku ma har yanzu ba ku da fahimta?
17 Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga?
18 Amma abubuwan da ke fita daga baki suna fitowa ne daga zuciya. Su ne abubuwan da ke kazantar da mutum.
19 Domin daga zuciya mugayen tunani suke fitowa, kisan kai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, da zage-zage.
20 Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.”
21 Sai Yesu ya tafi daga nan ya nufi yankin biranen Taya da Sidon.
22 Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.”
23 Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, “Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu.”
24 Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.”
25 Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, “Ubangiji ka taimake ni.”
26 Ya amsa ya ce, “Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka.
27 Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.”
28 Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.”'Yarta ta warke a lokacin.
29 Yesu ya bar wurin ya tafi kusa da tekun Galili. Sai ya hau tudu ya zauna a can.
30 Taro mai yawa suka zo gunsa. Suka kawo masa guragu, makafi, bebaye da nakasassun mutane da yawa, da wadansu marasa lafiya. Suka kawo su gaban Yesu, sai ya warkar da su.
31 Don haka mutane da yawa suka yi mamaki a lokacin da suka ga bebaye suna magana, nakasassu sun warke, guragu suna tafiya, makafi suna gani. Sai suka daukaka Allah na Isra'ila.
32 Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.”
33 Almajiran suka ce masa, “A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan.”
34 Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.”
35 Sai Yesu ya umarci taron su zauna a kasa.
36 Ya dauki gurasar nan bakwai da kifin, bayan ya yi godiya, ya kakkarya gurasar ya bada ita ga almajiran Sai almajiran suka ba taron.
37 Jama'a duka suka ci suka koshi. Suka tattara gutsattsarin abincin da ya rage, kwando bakwai cike.
38 Wadanda suka ci su dubu hudu ne maza, banda mata da yara.
39 Sai Yesu ya sallami taron ya shiga cikin jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.