< Mattiyu 10 >

1 Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da kazaman ruhohi, su warkar da kowacce irin cuta da rashin lafiya.
et convocatis duodecim discipulis suis dedit illis potestatem spirituum inmundorum ut eicerent eos et curarent omnem languorem et omnem infirmitatem
2 To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya;
duodecim autem apostolorum nomina sunt haec primus Simon qui dicitur Petrus et Andreas frater eius
3 Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus;
Iacobus Zebedaei et Iohannes frater eius Philippus et Bartholomeus Thomas et Mattheus publicanus et Iacobus Alphei et Thaddeus
4 Saminu Bakairawane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.
Simon Cananeus et Iudas Scariotes qui et tradidit eum
5 Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, ''Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa.
hos duodecim misit Iesus praecipiens eis et dicens in viam gentium ne abieritis et in civitates Samaritanorum ne intraveritis
6 Sai dai ku je wurin batattun tumaki na gidan Isra'ila.
sed potius ite ad oves quae perierunt domus Israhel
7 Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'.
euntes autem praedicate dicentes quia adpropinquavit regnum caelorum
8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tada matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljanu. Kyauta kuka samu ku ma ku bayar kyauta.
infirmos curate mortuos suscitate leprosos mundate daemones eicite gratis accepistis gratis date
9 Kada ku rike zinariya, ko azurfa, ko tagulla a jakarku.
nolite possidere aurum neque argentum neque pecuniam in zonis vestris
10 Kada kuma ku dauki zabira a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci abincin sa.
non peram in via neque duas tunicas neque calciamenta neque virgam dignus enim est operarius cibo suo
11 Kowanne birni, ko kauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma zauna a wurin har lokacin da za ku tashi.
in quamcumque civitatem aut castellum intraveritis interrogate quis in ea dignus sit et ibi manete donec exeatis
12 In za ku shiga gida ku ce, salama a gareku.
intrantes autem in domum salutate eam
13 Idan gidan akwai dan salama, salamarku za ta ta tabbata a gare shi. Idan kuwa babu, salamarku za ta komo maku.
et siquidem fuerit domus digna veniat pax vestra super eam si autem non fuerit digna pax vestra ad vos revertatur
14 Ga wadanda su ka ki karbar ku ko sauraron ku, idan za ku fita garin ko gidan, sai ku karkade kurar kafafunku.
et quicumque non receperit vos neque audierit sermones vestros exeuntes foras de domo vel de civitate excutite pulverem de pedibus vestris
15 Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni.
amen dico vobis tolerabilius erit terrae Sodomorum et Gomorraeorum in die iudicii quam illi civitati
16 ''Duba, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai, don haka sai ku zama masu wayo kamar macizai, da kuma marasa barna kamar kurciyoyi.
ecce ego mitto vos sicut oves in medio luporum estote ergo prudentes sicut serpentes et simplices sicut columbae
17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi maku bulala a majami'unsu.
cavete autem ab hominibus tradent enim vos in conciliis et in synagogis suis flagellabunt vos
18 Za su kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku bada shaida a gabansu, da kuma gaban al'ummai.
et ad praesides et ad reges ducemini propter me in testimonium illis et gentibus
19 Idan har sun bada ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku fada, domin za a ba ku abin da za ku fada a lokacin.
cum autem tradent vos nolite cogitare quomodo aut quid loquamini dabitur enim vobis in illa hora quid loquamini
20 Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.
non enim vos estis qui loquimini sed Spiritus Patris vestri qui loquitur in vobis
21 Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su.
tradet autem frater fratrem in mortem et pater filium et insurgent filii in parentes et morte eos adficient
22 Kowa kuma zai ki ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai tsira.
et eritis odio omnibus propter nomen meum qui autem perseveraverit in finem hic salvus erit
23 In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo.
cum autem persequentur vos in civitate ista fugite in aliam amen enim dico vobis non consummabitis civitates Israhel donec veniat Filius hominis
24 Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba yafin ubangijinsa.
non est discipulus super magistrum nec servus super dominum suum
25 Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa!
sufficit discipulo ut sit sicut magister eius et servus sicut dominus eius si patrem familias Beelzebub vocaverunt quanto magis domesticos eius
26 Don haka kada kuji tsoron su, domin ba abin da yake boye da ba za a bayyana ba.
ne ergo timueritis eos nihil enim opertum quod non revelabitur et occultum quod non scietur
27 Abin da nake fada maku a asirce, ku fada a sarari. Abin da kuma kuka ji a cikin rada, ku yi shelarsa daga kan soraye.
quod dico vobis in tenebris dicite in lumine et quod in aure auditis praedicate super tecta
28 Kada ku ji tsoron masu kisan jikin mutum, amma ba sa iya kashe rai. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon kashe jiki ya kuma jefa rai cikin jahannama. (Geenna g1067)
et nolite timere eos qui occidunt corpus animam autem non possunt occidere sed potius eum timete qui potest et animam et corpus perdere in gehennam (Geenna g1067)
29 Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba.
nonne duo passeres asse veneunt et unus ex illis non cadet super terram sine Patre vestro
30 Ai, ko da gashin kan ku ma duk a kidaye yake.
vestri autem et capilli capitis omnes numerati sunt
31 Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa.
nolite ergo timere multis passeribus meliores estis vos
32 ''Saboda haka duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, ni ma zan yi shaidar sa a gaban Ubana wanda ya ke cikin Sama.
omnis ergo qui confitebitur me coram hominibus confitebor et ego eum coram Patre meo qui est in caelis
33 Amma duk wanda ya yi musun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi musun sanin sa a gaban Ubana da yake cikin Sama.''
qui autem negaverit me coram hominibus negabo et ego eum coram Patre meo qui est in caelis
34 ''Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.
nolite arbitrari quia venerim mittere pacem in terram non veni pacem mittere sed gladium
35 Domin na zo ne in hada mutum da ubansa gaba, 'ya da uwatarta, mata da kuma surukarta.
veni enim separare hominem adversus patrem suum et filiam adversus matrem suam et nurum adversus socrum suam
36 Zai zama na kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa.
et inimici hominis domestici eius
37 Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.
qui amat patrem aut matrem plus quam me non est me dignus et qui amat filium aut filiam super me non est me dignus
38 Wanda kuma bai dauki gicciyensa ya biyo ni ba, bai cancanci zama nawa ba.
et qui non accipit crucem suam et sequitur me non est me dignus
39 Dukan mai son ya ceci ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, yana ceton sa ne.
qui invenit animam suam perdet illam et qui perdiderit animam suam propter me inveniet eam
40 ''Wanda ya marabce ku, ya marabce ni ke nan.
qui recipit vos me recipit et qui me recipit recipit eum qui me misit
41 Wanda ya marabce ni kuwa, ya marabci wanda ya aiko ni. Wanda ya marabci annabi domin shi annabi ne, zai karbi lada kamar na annabi. Wanda kuma ya marabci mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami lada kamar na mai adalci.
qui recipit prophetam in nomine prophetae mercedem prophetae accipiet et qui recipit iustum in nomine iusti mercedem iusti accipiet
42 Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba.''
et quicumque potum dederit uni ex minimis istis calicem aquae frigidae tantum in nomine discipuli amen dico vobis non perdet mercedem suam

< Mattiyu 10 >