< Markus 3 >

1 Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami'a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu.
Καὶ εἰσῆλθεν πάλιν εἰς συναγωγήν, καὶ ἦν ἐκεῖ ἄνθρωπος, ἐξηραμμένην ἔχων τὴν χεῖρα.
2 Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi.
Καὶ παρετήρουν αὐτὸν, εἰ τοῖς Σάββασιν θεραπεύσει αὐτόν, ἵνα κατηγορήσωσιν αὐτοῦ.
3 Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun “Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa.”
Καὶ λέγει τῷ ἀνθρώπῳ τῷ τὴν χεῖρα ἔχοντι ξηράν, “Ἔγειρε εἰς τὸ μέσον.”
4 Sai ya ce wa mutane, “Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? “Amma suka yi shiru.
Καὶ λέγει αὐτοῖς, “Ἔξεστιν τοῖς Σάββασιν ἀγαθοποιῆσαι ἢ κακοποιῆσαι, ψυχὴν σῶσαι ἢ ἀποκτεῖναι;” Οἱ δὲ ἐσιώπων.
5 Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi.
Καὶ περιβλεψάμενος αὐτοὺς μετʼ ὀργῆς, συλλυπούμενος ἐπὶ τῇ πωρώσει τῆς καρδίας αὐτῶν, λέγει τῷ ἀνθρώπῳ, “Ἔκτεινον τὴν χεῖρα σου.” Καὶ ἐξέτεινεν, καὶ ἀπεκατεστάθη ἡ χεὶρ αὐτοῦ.
6 Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi.
Καὶ ἐξελθόντες, οἱ Φαρισαῖοι εὐθὺς μετὰ τῶν Ἡρῳδιανῶν συμβούλιον ἐποίησαν κατʼ αὐτοῦ, ὅπως αὐτὸν ἀπολέσωσιν.
7 Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya
Καὶ ὁ ˚Ἰησοῦς μετὰ τῶν μαθητῶν αὐτοῦ, ἀνεχώρησεν πρὸς τὴν θάλασσαν· καὶ πολὺ πλῆθος ἀπὸ τῆς Γαλιλαίας ἠκολούθησεν, καὶ ἀπὸ τῆς Ἰουδαίας,
8 Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa.
καὶ ἀπὸ Ἱεροσολύμων, καὶ ἀπὸ τῆς Ἰδουμαίας, καὶ πέραν τοῦ Ἰορδάνου, καὶ περὶ Τύρον καὶ Σιδῶνα, πλῆθος πολύ ἀκούοντες ὅσα ἐποίει, ἦλθον πρὸς αὐτόν.
9 Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi.
Καὶ εἶπεν τοῖς μαθηταῖς αὐτοῦ ἵνα πλοιάριον προσκαρτερῇ αὐτῷ διὰ τὸν ὄχλον, ἵνα μὴ θλίβωσιν αὐτόν.
10 Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi.
Πολλοὺς γὰρ ἐθεράπευσεν, ὥστε ἐπιπίπτειν αὐτῷ, ἵνα αὐτοῦ ἅψωνται ὅσοι εἶχον μάστιγας.
11 Duk sa'adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne.”
Καὶ τὰ πνεύματα τὰ ἀκάθαρτα, ὅταν αὐτὸν ἐθεώρουν, προσέπιπτον αὐτῷ καὶ ἔκραζον λέγοντα, ὅτι “Σὺ εἶ ὁ Υἱὸς τοῦ ˚Θεοῦ.”
12 Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi.
Καὶ πολλὰ ἐπετίμα αὐτοῖς ἵνα μὴ αὐτὸν φανερὸν ποιήσωσιν.
13 Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa.
Καὶ ἀναβαίνει εἰς τὸ ὄρος, καὶ προσκαλεῖται οὓς ἤθελεν αὐτός, καὶ ἀπῆλθον πρὸς αὐτόν.
14 Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi,
Καὶ ἐποίησεν δώδεκα, οὓς καὶ ἀποστόλους ὠνόμασεν, ἵνα ὦσιν μετʼ αὐτοῦ, καὶ ἵνα ἀποστέλλῃ αὐτοὺς κηρύσσειν
15 Ya kuma basu Ikon fitar da aljanu.
καὶ ἔχειν ἐξουσίαν ἐκβάλλειν τὰ δαιμόνια.
16 Ya zabi guda goma sha biyu wato Saminu kuma yaba shi suna Bitrus.
Καὶ ἐποίησεν τοὺς δώδεκα: καὶ ἐπέθηκεν ὄνομα τῷ Σίμωνι, Πέτρον,
17 Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau 'ya'yan tsawa,
καὶ Ἰάκωβον τὸν τοῦ Ζεβεδαίου, καὶ Ἰωάννην τὸν ἀδελφὸν τοῦ Ἰακώβου, καὶ ἐπέθηκεν αὐτοῖς ὀνόματα Βοανηργές, ὅ ἐστιν “Υἱοὶ βροντῆς”,
18 da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye,
καὶ Ἀνδρέαν, καὶ Φίλιππον, καὶ Βαρθολομαῖον, καὶ Ματθαῖον, καὶ Θωμᾶν, καὶ Ἰάκωβον τὸν τοῦ Ἁλφαίου, καὶ Θαδδαῖον, καὶ Σίμωνα τὸν Καναναῖον,
19 da Yahuza Iskariyoti wanda zai bashe shi.
καὶ Ἰούδαν Ἰσκαριώθ, ὃς καὶ παρέδωκεν αὐτόν.
20 Sa'adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci,
Καὶ ἔρχεται εἰς οἶκον, καὶ συνέρχεται πάλιν ὁ ὄχλος, ὥστε μὴ δύνασθαι αὐτοὺς μηδὲ ἄρτον φαγεῖν.
21 Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, “Ai, baya cikin hankalinsa “
Καὶ ἀκούσαντες, οἱ παρʼ αὐτοῦ ἐξῆλθον κρατῆσαι αὐτόν, ἔλεγον γὰρ, ὅτι “Ἐξέστη.”
22 Marubutan da suka zo daga Urushalima suka ce “Ai Ba'alzabuba ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.”
Καὶ οἱ γραμματεῖς, οἱ ἀπὸ Ἱεροσολύμων καταβάντες ἔλεγον, ὅτι “Βεελζεβοὺλ ἔχει”, καὶ, ὅτι “Ἐν τῷ ἄρχοντι τῶν δαιμονίων, ἐκβάλλει τὰ δαιμόνια.”
23 Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, “Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan?
Καὶ προσκαλεσάμενος αὐτοὺς, ἐν παραβολαῖς ἔλεγεν αὐτοῖς, “Πῶς δύναται Σατανᾶς Σατανᾶν ἐκβάλλειν;
24 idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba.
Καὶ ἐὰν βασιλεία ἐφʼ ἑαυτὴν μερισθῇ, οὐ δύναται σταθῆναι ἡ βασιλεία ἐκείνη.
25 Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba.
Καὶ ἐὰν οἰκία ἐφʼ ἑαυτὴν μερισθῇ, οὐ δυνήσεται ἡ οἰκία ἐκείνη σταθῆναι.
26 Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan.
Καὶ εἰ ὁ Σατανᾶς ἀνέστη ἐφʼ ἑαυτὸν καὶ ἐμερίσθη, οὐ δύναται στῆναι, ἀλλὰ τέλος ἔχει.
27 Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa'an nan kuma ya kwashe kayan gidansa.
Ἀλλʼ οὐ δύναται οὐδεὶς εἰς τὴν οἰκίαν τοῦ ἰσχυροῦ εἰσελθὼν τὰ σκεύη αὐτοῦ διαρπάσαι, ἐὰν μὴ πρῶτον τὸν ἰσχυρὸν δήσῃ, καὶ τότε τὴν οἰκίαν αὐτοῦ διαρπάσει.
28 Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta,
Ἀμὴν, λέγω ὑμῖν ὅτι πάντα ἀφεθήσεται τοῖς υἱοῖς τῶν ἀνθρώπων τὰ ἁμαρτήματα καὶ αἱ βλασφημίαι, ὅσα ἐὰν βλασφημήσωσιν.
29 amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada.” (aiōn g165, aiōnios g166)
Ὃς δʼ ἂν βλασφημήσῃ εἰς τὸ ˚Πνεῦμα τὸ Ἅγιον, οὐκ ἔχει ἄφεσιν εἰς τὸν αἰῶνα, ἀλλὰ ἔνοχός ἐστιν αἰωνίου ἁμαρτήματος”– (aiōn g165, aiōnios g166)
30 “Yesu ya fadi wadannan abubuwa domin suna cewa yana da ba kazamin ruhu,”
ὅτι ἔλεγον, “Πνεῦμα ἀκάθαρτον ἔχει.”
31 Sa'an nan uwatasa, da “Yan'uwansa suka zo suna tsaye a waje. sai suka aika masa, suna kuma umurtar sa ya zo.
Καὶ ἔρχονται ἡ μήτηρ αὐτοῦ καὶ οἱ ἀδελφοὶ αὐτοῦ, καὶ ἔξω στήκοντες, ἀπέστειλαν πρὸς αὐτὸν καλοῦντες αὐτόν.
32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka.”
Καὶ ἐκάθητο περὶ αὐτὸν ὄχλος, καὶ λέγουσιν αὐτῷ, “Ἰδοὺ, ἡ μήτηρ σου καὶ οἱ ἀδελφοί σου, ἔξω ζητοῦσίν σε.”
33 Ya amsa masu, “Dacewa su wanene uwa-ta da “yan'uwa na? “
Καὶ ἀποκριθεὶς αὐτοῖς λέγει, “Τίς ἐστιν ἡ μήτηρ μου, καὶ οἱ ἀδελφοί μου;”
34 Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan!
Καὶ περιβλεψάμενος τοὺς περὶ αὐτὸν, κύκλῳ καθημένους λέγει, “Ἴδε, ἡ μήτηρ μου καὶ οἱ ἀδελφοί μου!
35 Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan'uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta.”
Ὃς γὰρ ἂν ποιήσῃ τὸ θέλημα τοῦ ˚Θεοῦ, οὗτος ἀδελφός μου καὶ ἀδελφὴ καὶ μήτηρ ἐστίν.”

< Markus 3 >