< Luka 8 >

1 Bayan haka, Yesu da almajiransa goma sha biyu, su ka zagaya cikin birane da kauyuka dabam dabam, suna wa'azi da shelar labari mai dadi game da mulkin Allah,
Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,
2 mata da yawa wadanda Yesu ya warkar daga aljanu da cututtuka iri iri suna tafiya tare da su. A cikinsu akwai Maryamu wadda a ke ce da ita Magadaliya, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta,
da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.
3 da Yuwana matar Kuza wakilin Hirudus, da Suzanatu da kuma wasu mata da yawa. Daga abin hannunsu suka tanada masu.
Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.
4 Wata rana aka tara taron mutane da yawa, saboda mutane su na zuwa daga birane da yawa domin su ga Yesu. Ya yi magana dasu cikin misali.
Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce,
5 “Wani mai shuka ya tafi domin ya shuka iri. Sa'adda ya ke yafa iri, wadansu iri suka fada a kan hanya. Sai mutane suka tattake su, tsuntsaye kuma suka tsince wadansu suka cinye.
“Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su.
6 Wadansu kuma suka fada a kan duwatsu inda babu kasa da yawa. Da suka tsaro suka fara girma, sai nan da nan suka bushe saboda babu laima a wurin.
Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin.
7 Wadansu irin kuma suka fada inda yake da kayayuwa. Tsiretsiren kayayuwan suka fito tare da irin da aka shuka, suka shake su yadda basu iya yin girma ba.
Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su.
8 Amma wadansu irin suka fada a kan kasa mai kyau, suka yi girma sosai suka ba da anfani da yawa, har rubi dari.” Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi kira gare su, “Duk mai kunnen ji, bari ya ji.”
Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.” Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
9 Sai almajiran Yesu suka tambaye shi ya gaya ma su ma'anar labarin.
Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali.
10 ya ce da su, “Ku aka ba dama ku gane boyayyun abubuwa, na mulkin Allah. Amma ga sauran mutane ina yi masu magana cikin misalai, 'Domin ko da sun gani ba za su gane ba, kuma ko da sun ji ba za su fahimta ba.”
Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’
11 To ga ma'anar misalin. Irin shi ne maganar Allah.
“Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah.
12 Irin da ya fada a kan hanya sune mutanen da suka ji maganar Allah amma daga baya sai shedan ya zo ya dauke maganar daga cikin hankulansu, domin kada su bada gaskiya su tsira.
Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.
13 Sa'annan, wadanda suka fada kan duwatsu sune mutanen da, da zarar sun ji maganar, sukan karbe ta da murna, amma ba su da sauyu; su kan bada gaskiya na dan lokaci kadan kawai, da zaran gwaji ya same su sai su ridda.
Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.
14 Irin da suka fada cikin kayayuwa, sune mutanen da suka ji maganar, amma da suka ci gaba da rayuwa, sai suka bari matsalolin rayuwa kamar dukiya da jin dadin rayuwa suka fi karfinsu, sai ya zama ba su iya bada 'ya'yan da suka yi girma ba.
Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da’ya’ya.
15 Amma irin da suka fada a kan kasa mai kyau, wadannan sune mutanen da suka ji maganar, suka karbe ta da gaskiya da zuciya daya, sun rike ta kam-kam, suna jimrewa wurin ba da 'ya'ya.
Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da’ya’ya.”
16 Ba mai kunna fitila, ya rufe ta da kasko, ko su sa ta a karkashin gado. Amma sai a sa ta a wurin zaman ta domin duk wanda ya shigo ya iya ganin hasken ta.
“Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.
17 Babu abin da yake a boye wanda ba za a tone shi ba, ko wani asiri da ba za ya fito fili a san shi ba.
Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba.
18 Ku yi hankali da yadda kuke ji, domin duk mai abu, shi za a kara wa, kuma duk mara abu, dan kadan da yake tunani yana da shi ma, za a dauke.”
Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”
19 Sai mahafiyar Yesu da 'yan'uwansa, su ka zo wurinsa, amma ba su iya zuwa ko kusa da shi ba saboda taron jama'a.
Sai uwar Yesu da’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron.
20 Sai wani ya gaya masa, “Ga mahaifiyarka da 'yan'uwanka, su na tsayuwa a waje, su na son ganin ka.”
Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”
21 Amma Yesu ya amsa ya ce ma su, “Mahaifiyata da 'yan'uwana sune wadanda suke jin maganar Allah, suke yin biyayya da ita.”
Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”
22 Wata rana kuma Yesu ya shiga cikin jirgin ruwa, shi da almajiransa. Ya ce masu, “Ina so mu je dayan ketaren tafkin.” Sai su ka fara tafiya domin su ketare tafkin.
Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya.
23 Amma sa'adda su ke tafiya sai Yesu ya yi barci, sai wata iska mai karfi ta taso cikin tafkin, nan da nan sai jirgin ya fara cika da ruwa, kuma su na cikin hatsari.
Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.
24 Sai almajiran Yesu su ka zo su ka tashe shi daga barci. Suka ce da shi, “Ya Shugaba! Ya Shugaba! Za mu mutu!” Sai ya tashi ya umarci iskar, sai iskar mai hauka da tumbatsar ruwan sun tsaya tsit.
Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!” Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit.
25 Daga nan sai ya ce da su, “Ina bangaskiyar ku?” Almajiran suka tsorata suka yi mamakin abin da ya faru nan take. Suka ce wa junansu, “Wanene wannan wanda har zai ba iska da ruwa umarni kuma su yi masa biyayya?”
Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?” A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”
26 Suka zo yankin Garasinawa, wanda ke kusa da Gallili.
Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili.
27 Sa'adda Yesu ya sauka kasa, sai wani mutum daga wannan yankin ya tarbe shi. Wannan mutum kuwa yana da aljanu. Mutumin ya dade ba ya sa tufafi, kuma ba ya zama a gida. Maimakon haka, sai a cikin kabarbura ya ke zama.
Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura.
28 Sa'adda ya ga Yesu, mutumin ya yi ihu da karfi, ya rusuna a gabansa da babban murya ya ce, “Me zan yi da kai, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka, kada ka ba ni azaba!”
Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!”
29 Domin Yesu ya umarci aljanun su fita daga cikinsa, domin sau da dama aljanun sukan kama shi. Ko an daure mutumin da sarkoki an kuma tsare shi, yakan tsuttsunke su, kazaman ruhohin sukan kora shi cikin jeji.
Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.
30 Sa'annan Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Sai ya ba da amsa, “Suna na dubbai.” Ya ce haka ne domin aljanu da yawa sun shiga wannan mutum.
Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa.
31 Aljanun suka yi ta rokon Yesu kada ya ummarce su su shiga cikin rami mai zurfi. (Abyssos g12)
Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis. (Abyssos g12)
32 Akwai babban garken aladu su na kiwo a kan tsauni kusa da wurin. Aljanun suka roki Yesu da ya barsu su shiga cikin aladun, shi kuwa ya yarda masu.
A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu.
33 Aljanun suka bar mutumin suka shiga cikin aladun, sai garken aladun suka gangara kwari suka fada cikin tafkin, suka nutse.
Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.
34 Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen.
Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari.
35 Don haka, mutanen da suka ji haka suka tafi domin su ga abin da ya faru, suka zo wurin da Yesu yake, suka ga mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa. Suka ga ya na sanye da tufafi, kuma ya na cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
36 Mutanen da suka ga abin da ya faru, suka gaya wa wadansu yadda aka warkar da mutumin da aljanu suke iko da shi.
Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun.
37 Sai dukan mutane wadanda suke cikin yankin Garasinawa da wadanda suke kewaye, suka roki Yesu da ya fita daga cikin yankin kasarsu domin sun ji tsoro kwarai da gaske. Daga nan Yesu da almajiransa suka shiga cikin jirgin ruwa suka koma.
Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi.
38 Mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa, ya roki Yesu cewa, “Ka barni in tafi tare da kai!” Amma Yesu ya sallame shi cewa,
Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce,
39 “Ka koma gida ka gaya wa mutanen ka abubuwa masu girma wadanda Allah ya yi maka.” Daga nan sai mutumin ya tafi yana ta gayawa dukan mutanen birnin game da abubuwan da Yesu ya yi masa.
“Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.
40 Sa'adda Yesu ya dawo, mutanen suka marabce shi, gama, dukansu suna jiransa.
Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa.
41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, daya daga cikin shugabannin majami'a, ya zo kusa da Yesu ya rusuna da kansa a kasa. Ya roke shi domin ya zo gidansa,
Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa,
42 saboda diyarsa mai kimanin shekara goma sha biyu ta na bakin mutuwa, kuma ita kadai ce diya a gare shi. Amma sa'adda yake tafiya, taron mutane da yawa suna matsa shi.
domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe.
43 Akwai wata mace a nan wadda take zubar jini har shekara goma sha biyu. Ta kashe kudinta duka a wurin likitoci, domin su warkar da ita amma ba wanda ya iya warkar da ita.
A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita.
44 Sai ta biyo ta bayan Yesu ta taba habar rigarsa. Nan take sai zubar jinin ya tsaya.
Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
45 Yesu ya ce, “Wanene ya taba ni?” Wadanda suke kewaye da shi, kowa ya ce bai taba shi ba, Bitrus ya ce, “Shugaba, mutane da yawa suna ta taruwa kewaye da kai suna ta matsowa kusa da kai.”
Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?” Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”
46 Amma Yesu ya ce, “Na sani, wani ya taba ni, domin iko ya fita daga wurina.”
Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”
47 Sa'adda matar ta gane cewa ba za ta iya boyewa ba, sai ta zo wurinsa cikin tsoro. Ta durkusa a gaban Yesu, ta fada a gaban dukan jama'a dalilin da ya sa ta taba shi kuma nan da nan ta warke.
Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take.
48 Sai ya ce da ita, “Diya, bangaskiyarki ta warkar da ke. Tafi cikin salama.”
Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
49 Yana cikin yin magana, wani daga cikin gidan shugaban majami'ar ya zo, ya ce, “Diyarka ta riga ta mutu, kada ka dami malam.”
Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”
50 Amma sa'adda Yesu ya ji haka, sai ya ce da shi, “Kada ka ji tsoro. Ka bada gaskiya za ta rayu.”
Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
51 Sa'adda ya zo gidan, bai bar kowa ya shiga gidan tare da shi ba sai Bitrus da Yahaya da Yakubu, da mahaifiyar yarinyar da babanta.
Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar.
52 Dukan mutane a wurin, suna ta kuka da karfi saboda sun damu da yarinyar ta mutu. Amma Yesu ya ce da su, “Ku dena kuka! Ba mutuwa ta yi ba! Barci ta ke yi kawai!”
Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”
53 Mutanen suka yi ma sa dariyan reni, saboda sun sani yarinyar ta mutu.
Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu.
54 Amma ya kama hannun ta yayi kira cewa, “Yarinya, na ce ki tashi!”
Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.”
55 Nan da nan ruhun ta ya dawo jikin ta sai ta tashi. Ya ce masu su ba ta wani abu ta ci.
Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.
56 Iyayenta suka yi mamaki, amma Yesu ya ce da iyayen kada su gaya wa kowa abin da ya faru.
Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.

< Luka 8 >