< Luka 5 >

1 Ya zama sa'adda mutane sun taru a wurin Yesu suna sauraron maganar Allah, yana kuma yana tsaye a bakin tabkin Janisarata. 2 Ya ga jiragen ruwa biyu tsaye a bakin tabkin. Masu kamun kifin kuwa sun fita daga cikin jiragen suna wanke tarunsu. 3 Yesu ya shiga daya daga cikn jiragen wanda shike na Bitrus ne, sai ya umarce shi ya dan zakuda da jirgin daga bakin tabkin kadan zuwa cikin ruwa. Sai ya zauna ya kuma koya wa mutane daga cikin jirgin. 4 Da ya gama magana, ya ce wa Siman, “Zakuda jirgin zuwa wuri mai zurfi sa'annan ka zuba tarunka domin kamu.” 5 Siman ya amsa ya ce, “Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun.” 6 Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa. 7 Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa. 8 Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, “Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne.” 9 Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama. 10 Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane.” 11 Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi. 12 Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, “Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni.” 13 Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, “Na yarda. Ka tsarkaka.” Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi. 14 Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, “Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu.” 15 Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu. 16 Amma ya kan janye zuwa wuraren da babu kowa ya yi addu'a. 17 Ya zama daya a cikin kwanakin da yake koyarwa, akwai Farisawa da malaman attaura da ke zaune a wurin wandanda suka zo daga kauyukan da suke kewaye da Galili da Yahudiya da kuma birnin Urushalima. Ikon Ubangiji yana tare da shi domin warkarwa. 18 A lokacin nan, wasu mutane suka zo dauke da wani mutum shanyayye a kan tabarma, suka kuma nemi yadda za su shigar da shi ciki, su kwantar da shi a gaban Yesu. 19 Ba su iya samun hanyar da za su shigar da shi ba saboda taron, sai suka hau saman gidan, suka saukar da shi daga rufin, a kan tabarman sa, zuwa tsakiyar mutanen, dai dai a gaban Yesu. 20 Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, “Maigida, an gafarta zunubanka.” 21 Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, “Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?” 22 Amma da Yesu ya fahimci abin da suke tunani, sai ya amsa ya ce masu, “Don me kuke sukar wannan a zuciyarku? 23 Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?” 24 Amma domin ku sani cewa Dan Mutum yana da yancin gafarta zunubai a duniya, na ce maka, 'Tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidanka.'” 25 Nan take, ya tashi a gabansu ya dauki tabarma da yake kwance; sai ya koma gidansa, yana daukaka Allah. 26 Kowa yana ta mamaki kuma suka daukaka Allah. Suna cike da tsoro, suna cewa, “Yau mun ga abubuwan al'ajibi.” 27 Bayan wadannan abubuwa sun faru, Yesu ya fito daga can sai ya ga wani mai karban haraji mai suna Lawi yana zama a wurin karban haraji. Ya ce masa, “Ka biyo ni.” 28 Sai Lawi ya bar komai, ya tashi, ya bi shi. 29 Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su. 30 Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, “Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?” 31 Yesu ya amsa masu, “Masu lafiya basu bukatar likita, wadanda ke marasa lafiya kadai ke bukatar likita. 32 Ban zo domin kiran masu adalci ba, amma na zo ne domin kiran masu zunubi zuwa ga tuba.” 33 Sun ce masa, “Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?” 34 Yesu ya ce masu, “Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su? 35 Amma kwanaki na zuwa wadanda za a dauke ango daga wurinsu, a kwanakin za su yi azumi.” 36 Sai Yesu ya sake fada masu wani misali. “Babu wanda zai yage kyalle daga sabuwar tufa, ya kuma yi amfani da ita ya dinka tsohuwar tufa. Idan ya yi hakannan, zai yage sabuwar tufar, kuma kyallen daga sabuwar tufar ba zai dace da kyallen tsohuwar tufar ba. 37 Kuma, babu mutum da zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsofafin salkuna. Idan ya yi haka, sabon ruwan inabin zai fasa salkunan, kuma ruwan inabin din zai zube, salkunan kuma za su lallace. 38 Amma dole ne a sa sabon ruwan inabi a sabobin salkuna. 39 Babu wanda zai yi marmarin sabon ruwan inabi bayan da ya sha tsohon, gama zai ce, “Tsohon ya fi sabon.”

< Luka 5 >