< Luka 5 >

1 Ya zama sa'adda mutane sun taru a wurin Yesu suna sauraron maganar Allah, yana kuma yana tsaye a bakin tabkin Janisarata.
Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,
2 Ya ga jiragen ruwa biyu tsaye a bakin tabkin. Masu kamun kifin kuwa sun fita daga cikin jiragen suna wanke tarunsu.
sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin abin kamun kifinsu.
3 Yesu ya shiga daya daga cikn jiragen wanda shike na Bitrus ne, sai ya umarce shi ya dan zakuda da jirgin daga bakin tabkin kadan zuwa cikin ruwa. Sai ya zauna ya kuma koya wa mutane daga cikin jirgin.
Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.
4 Da ya gama magana, ya ce wa Siman, “Zakuda jirgin zuwa wuri mai zurfi sa'annan ka zuba tarunka domin kamu.”
Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”
5 Siman ya amsa ya ce, “Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun.”
Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.”
6 Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa.
Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa.
7 Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa.
Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa.
8 Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, “Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne.”
Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!”
9 Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama.
Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama.
10 Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane.”
Yaƙub da Yohanna,’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”
11 Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi.
Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.
12 Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, “Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni.”
Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.”
13 Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, “Na yarda. Ka tsarkaka.” Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi.
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
14 Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, “Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu.”
Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”
15 Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu.
Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.
16 Amma ya kan janye zuwa wuraren da babu kowa ya yi addu'a.
Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a.
17 Ya zama daya a cikin kwanakin da yake koyarwa, akwai Farisawa da malaman attaura da ke zaune a wurin wandanda suka zo daga kauyukan da suke kewaye da Galili da Yahudiya da kuma birnin Urushalima. Ikon Ubangiji yana tare da shi domin warkarwa.
Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo.
18 A lokacin nan, wasu mutane suka zo dauke da wani mutum shanyayye a kan tabarma, suka kuma nemi yadda za su shigar da shi ciki, su kwantar da shi a gaban Yesu.
Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu.
19 Ba su iya samun hanyar da za su shigar da shi ba saboda taron, sai suka hau saman gidan, suka saukar da shi daga rufin, a kan tabarman sa, zuwa tsakiyar mutanen, dai dai a gaban Yesu.
Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.
20 Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, “Maigida, an gafarta zunubanka.”
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”
21 Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, “Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?”
Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”
22 Amma da Yesu ya fahimci abin da suke tunani, sai ya amsa ya ce masu, “Don me kuke sukar wannan a zuciyarku?
Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?
23 Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?”
Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?
24 Amma domin ku sani cewa Dan Mutum yana da yancin gafarta zunubai a duniya, na ce maka, 'Tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidanka.'”
Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”
25 Nan take, ya tashi a gabansu ya dauki tabarma da yake kwance; sai ya koma gidansa, yana daukaka Allah.
Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.
26 Kowa yana ta mamaki kuma suka daukaka Allah. Suna cike da tsoro, suna cewa, “Yau mun ga abubuwan al'ajibi.”
Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”
27 Bayan wadannan abubuwa sun faru, Yesu ya fito daga can sai ya ga wani mai karban haraji mai suna Lawi yana zama a wurin karban haraji. Ya ce masa, “Ka biyo ni.”
Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”
28 Sai Lawi ya bar komai, ya tashi, ya bi shi.
Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.
29 Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su.
Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.
30 Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, “Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?”
Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
31 Yesu ya amsa masu, “Masu lafiya basu bukatar likita, wadanda ke marasa lafiya kadai ke bukatar likita.
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
32 Ban zo domin kiran masu adalci ba, amma na zo ne domin kiran masu zunubi zuwa ga tuba.”
Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”
33 Sun ce masa, “Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?”
Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”
34 Yesu ya ce masu, “Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su?
Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?
35 Amma kwanaki na zuwa wadanda za a dauke ango daga wurinsu, a kwanakin za su yi azumi.”
Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”
36 Sai Yesu ya sake fada masu wani misali. “Babu wanda zai yage kyalle daga sabuwar tufa, ya kuma yi amfani da ita ya dinka tsohuwar tufa. Idan ya yi hakannan, zai yage sabuwar tufar, kuma kyallen daga sabuwar tufar ba zai dace da kyallen tsohuwar tufar ba.
Sai ya faɗa musu wannan misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyalle daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba.
37 Kuma, babu mutum da zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsofafin salkuna. Idan ya yi haka, sabon ruwan inabin zai fasa salkunan, kuma ruwan inabin din zai zube, salkunan kuma za su lallace.
Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace.
38 Amma dole ne a sa sabon ruwan inabi a sabobin salkuna.
A’a, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna.
39 Babu wanda zai yi marmarin sabon ruwan inabi bayan da ya sha tsohon, gama zai ce, “Tsohon ya fi sabon.”
Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’”

< Luka 5 >