< Luka 3 >

1 A cikin shekara ta goma sha biyar da Tibariyus Kaisar ke mulki, Bilatus Babunti kuma ke jagorar Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, dan'uwansa Filibus yana sarautar yankin Ituriya da Tirakonitis, Lisaniyas kuma na sarautar yankin Abiliya, 2 kuma zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, maganar Allah ta zo wurin Yahaya dan Zakariya, a cikin jeji. 3 Ya yi tafiya cikin dukan yankuna da ke kewaye da Kogin Urdun, yana wa'azin baftismar tuba domin gafarar zunubai. 4 Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, “Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa! 5 Za a cika kowani kwari, za a fasa kowani dutse a kuma baje kowani tudu, za a mike karkatattun hanyoyi, za a cike hanyoyi masu gargada, 6 kuma dukan mutane za su ga ceton Allah.” 7 Sai Yahaya ya kara fada wa taron jama'ar da ke zuwa domin ya yi masu baftisma, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargadeku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8 Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu. 9 Yanzu kuwa, an rigaya an sa gatari a gindin itatuwa. Sabili da haka, duk itacen da bai ba da 'ya'ya masu kyau ba za a sare shi kasa a kuma jefa shi cikin wuta.” 10 Sai mutanen da ke cikin taron jama'ar suka tambaye shi cewa, “To me za mu yi?” 11 Ya amsa ya ce masu, “Idan wani yana da taguwa biyu, sai ya ba wanda bashi da ita daya, kuma wanda yake da abinci ya yi haka nan.” 12 Masu karban haraji ma suka zo domin a yi masu baftisma, suka ce masa, “Malam, me za mu yi?” 13 Ya ce masu, “Kada ku karba kudi fiye da yadda aka umarce ku.” 14 Wasu sojoji ma suka tambaye shi cewa, “To, mu fa? Yaya za mu yi?” Ya ce masu, “Kada ku kwace wa wani kudi, kada ku kuma yi wa wani zargin karya. Ku dogara ga albashinku.” 15 Ana nan da mutane ke sauraron zuwan Almasihu, kowa yana ta tunani a zuciyar sa game da Yahaya, ko shi ne Almasihu. 16 Yahaya ya amsa ya ce masu duka, “Game da ni dai, na yi maku baftisma da ruwa, amma akwai wani tafiye wanda ya fi ni iko, ban ma isa in kwance maballin takalmansa ba. Shi zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta. 17 Kwaryar shikarsa na hanun sa domin ya share masussukarsa da kyau ya kuma tara alkama a cikin rumbunsa. Amma zai kona buntun da wuta marar mutuwa. 18 Da gargadi masu yawa ya yi wa mutanen wa'azin bishara. 19 Yahaya kuma ya tsauta wa sarki Hirudus domin ya auri matar dan'uwansa, Hiruduya, da kuma sauran abubuwan da Hirudus ya yi. 20 Amma Hirudus ya kara yin wani mugun abu. Ya sa an kulle Yahaya a cikin kurkuku. 21 Ana nan, lokacin da ake yiwa dukan mutane baftisma, aka yiwa Yesu mai baftisma. Lokacin da yake yin addu'a, sai sama ta bude, 22 kuma Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa a kamanin kurciya, sai wata murya ta fito daga sama, “Kai ne kaunataccen Da na. Ina jin dadin ka.” 23 Ana nan Yesu da kansa, da ya fara, yana kimanin shekara talatin. Shi dan (kamar yadda ake tsammani) Yusufu ne, dan Heli, 24 dan Matat, dan Lawi, dan Malki, dan Yanna, dan Yusufu, 25 dan Matatiya, dan Amos, dan Nahum, dan Hasli, dan Najjaya, 26 dan Ma'ata, dan Matatiya, dan Shimeya, dan Yuseka, dan Yoda, 27 dan Yowana, dan Resa, dan Zarubabila, dan Shiyaltiyel, dan Niri, 28 dan Malki, dan Addi, dan Kosama, dan Almadama, dan Er, 29 dan Yosi, dan Aliyeza, dan Yorima, dan Matat, dan Lawi, 30 dan Saminu, dan Yahuda, dan Yusufu, dan Yonana, dan Aliyakima, 31 dan Malaya, dan Mainana, dan Matata, dan Natan, dan Dauda, 32 dan Yesse, dan Obida, dan Bu'aza, dan Salmon, dan Nashon, 33 dan Amminadab, dan Adimi, dan Arama, dan Hezruna, dan Feresa, dan Yahuda, 34 dan Yakubu, dan Ishaku, dan Ibrahim, dan Tera, dan Nahor, 35 dan Serug, dan Reyu, dan Feleg, dan Abiru, dan Shela, 36 dan Kainana, dan Arfakshada, dan Shem, dan Nuhu, dan Lamek, 37 dan Metusela, dan Anuhu, dan Yaret, dan Mahalel, dan Kainana, 38 dan Enosh, dan Shitu, dan Adamu, dan Allah.

< Luka 3 >