< Luka 16 >

1 Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Akwai wani mai arziki da yake da wakili, sai aka yi karan sa da cewa wannan wakili yana fallasar masa da dukiya.
Pravil pa je tudi učencem svojim: Bil je en človek bogat, kteri je imel pristavnika; in tega so bili ovadili pri njem, da mu razsiplje imenje.
2 Sai mai arziki ya kira shi ya ce masa, 'Labarin me nake ji game da kai? Kawo lissafin wakilcin ka, don ba za ka sake zama wakili na ba.'
In poklicavši ga, reče mu: Kaj to slišim za te? Daj račun od gospodarstva svojega, ker ne moreš dalje gospodariti.
3 Sai wakilin ya ce a ransa, 'Kaka zan yi, da yake maigida na zai karbe wakilci daga hannuna? Gashi, ba ni da karfin noma ina kuwa jin kunya in yi roko.
A pristavnik reče sam s seboj: Kaj bom storil, ko mi gospodar moj odjemlje gospodarstvo? Kopati ne morem, prositi me je sram.
4 Na san abin da zan yi domin idan an fitar da ni daga wakilcin, mutane su karbe ni a gidajensu.
Vém, kaj bom storil, da me bodo, kedar bom odstavljen gospodarstva, sprejeli v hiše svoje.
5 Sai wakilin ya kira kowanne daya da maigidansa ke bi bashi, yace wa na farkon, 'Nawa maigida na yake bin ka?'
In poklicavši vsakega posameznega od dolžnikov gospodarja svojega, reče prvemu: Koliko si dolžen gospodarju mojemu?
6 Ya ce, 'Garwan mai dari.' Sai ya ce masa, 'Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubuta hamsin.'
On pa reče: Sto mer olja. In reče mu: Vzemi svojo pismo, pa sedí hitro, in napiši petdeset.
7 Ya kuma ce wa wani, 'Nawa ake binka?' Ya ce, 'Buhu dari na alkama.' Ya ce masa, 'Ga tarkardarka, ka rubuta tamanin.'
Po tem reče drugemu: A ti koliko si dolžen? On pa reče: Sto korcev pšenice. In velí mu: Vzemi svoje pismo, in napiši osemdeset.
8 Sai maigida ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama 'ya'yan zamanin nan a ma'ammalar su da mutanen zamaninsu sun fi 'ya'yan haske wayo. (aiōn g165)
In gospodar pohvali krivičnega hlapca, da je pametno storil. Kajti sinovi tega sveta so pametniji od sinov svetlobe v svojem rodu. (aiōn g165)
9 Ina gaya maku ku yi abuta ta dukiya ta rashin gaskiya, saboda idan ya kare, su karbe ku a gidaje masu dauwama. (aiōnios g166)
Tudi jaz vam pravim: Naredite si prijateljev s krivičnim bogastvom, da vas, kedar ubožate, sprejmó v večna stanovališča. (aiōnios g166)
10 Wanda yake da aminci a karamin abu, mai aminci ne a babban abu, wanda yake marar gaskiya a karamin abu, marar gaskiya ne a babban abu.
Kdor je v najmanjem zvest, zvest je tudi v velikem; in kdor je v najmanjem krivičen, krivičen je tudi v velikem.
11 Idan fa ba ku yi aminci da dukiya mara adalci ba, wa zai amince maku da dukiya ta gaskiya?
Če torej v krivičnem bogastvu niste bili zvesti, kdo vam bo zaupal pravično?
12 Idan kuma ba ku yi aminci da kudin wani ba, wa zai ba ku kudin da ke naku?
In če v tujem niste bili zvesti, kdo vam bo dal, kar je vaše?
13 Ba bawan da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya ko kuwa ya amince wa dayan, ya raina dayan. Ba za ku iya bauta wa Allah ku kuma bauta wa dukiya ba.”
Noben hlapec ne more dvema gospodoma služiti: ali bo enega sovražil, in drugega ljubil; ali se bo enega držal, in drugega bo zaničeval. Ne morete Bogu služiti in mamonu.
14 Da Farisawa da ke da kaunar kudi suka ji dukan wadannan abubuwa, suka yi masa ba'a.
Poslušali so pa vse to tudi Farizeji, kteri so srebro ljubili, ter so ga zasmehovali.
15 Sai ya ce masu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abin da mutane suke girmamawa kwarai abin kyama ne a gun Allah.
Pa jim reče: Vi ste tisti, kteri se delate pravične pred ljudmí; ali Bog pozná srca vaša: kajti kar je pri ljudéh visoko, gnjusoba je pred Bogom.
16 Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta.
Zakon in preroki so do Janeza; odtlej se oznanjuje kraljestvo Božje, in vsak s silo va-nj tišči.
17 Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude.
Laže je pa nebu in zemlji prejti, nego enej pičici iz zakona izpasti.
18 Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina.
Vsak, kdor pustí ženo svojo in se oženi z drugo, prešestvuje; in vsak, kdor popuščeno od moža vzeme, prešestvuje.
19 Akwai wani mai arziki, mai sa tufafi na alfarma masu tsada yana shagalin sa kowace rana.
Bil je pa neki človek bogat, in oblačil se je v škrlat in tančico, in razveseljeval se je vsak dan sijajno.
20 Aka ajiye wani gajiyayye a kofarsa, mai suna liazaru wanda duk jikinsa miki ne,
Bil je pa neki ubožec po imenu Lazar, kteri jo ležal pred vratmi njegovimi, gnôjen,
21 Shi kuwa yana marmarin ya koshi da barbashin da ke fadowa daga teburin mai arzikin nan har ma karnuka sukan zo suna lasar mikinsa.
In hrepeneč nasititi se z drobtinami, ktere so padale z mize bogatina; ali tudi psi so dohajali, ter so lizali gnoj njegov
22 Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, malaiku kuma suka dauke shi suka kai shi wurin Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi,
Zgodí se pa, da ubožec umrè, in odnesó ga angelji na naročje Abrahamovo; umrè pa tudi bogatin, in pokopljejo ga.
23 yana cikin hades yana shan azaba, sai ya daga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a kirjinsa. (Hadēs g86)
In v peklu, ko je bil v bolečinah, povzdigne očí svoje, in ugleda Abrahama od daleč, in Lazarja na naročji njegovem. (Hadēs g86)
24 Sai ya yi kira ya ce, 'Baba Ibrahim, ka ji tausayi na, ka aiko Li'azaru ya tsoma dan yatsansa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.'
In on zaklicavši, reče: Oče Abraham! usmili se me, in pošlji Lazarja, naj omoči konec prsta svojega v vodi, in mi jezik ohladí, ker se mučim v tem plamenu.
25 Amma Ibrahim ya ce, 'Yaro, ka tuna fa a zamanka na duniya ka sha duniyarka, ka kuma karba abubuwa masu kyau, amma Li'azaru kuma sai wahala. Amma yanzu dadi ake bashi a nan, kai kuwa kana shan azaba.
Abraham pa reče: Sin! spomeni se, da si ti prejel dobroto svojo v življenji svojem, in ravno tako Lazar slabo. Sedaj pa; on se tolaži, a ti se mučiš.
26 Banda haka ma, akwai rami mai zurfi, domin wadanda suke son ketarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ketaro zuwa wurinmu daga can.'
In vrh vsega tega, med nami in vami je postavljen prepad velik, da kteri hočejo odtod sniti k vam, ne morejo, in kteri odondod k nam, da ne prehajajo.
27 Sai mai arziki ya ce, 'To ina rokonka, Baba Ibrahim, ka aike shi zuwa gidan mahaifina -
Pa reče: Prosim te torej, oče, da ga pošlji na mojega očeta dom,
28 domin ina da 'yan'uwa maza biyar, ya je ya yi masu gargadi kada su ma su zo wurin azaban nan.'
Ker imam pet bratov: da jim to izpriča, da ne pridejo tudi oni na ta kraj trpljenja.
29 Amma Ibrahim ya ce, 'Suna da Musa da annabawa; bari su saurare su.'
Velí mu Abraham: Mojzesa imajo in preroke; poslušajo naj jih.
30 Sai mai arziki ya amsa, 'A'a, Baba Ibrahim, idan wani daga cikin matattu ya je wurinsu, zasu tuba.'
On pa reče: Ne, oče Abraham! nego če kdo od mrtvih pride k njim, potem se bodo spokorili.
31 Amma Ibrahim ya ce masa, 'In dai har basu saurari Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su rinjayu ba.'”
Pa mu reče: Če Mojzesa in prerokov ne poslušajo, ne bodo verovali, če tudi kdo od mrtvih vstane.

< Luka 16 >