< Luka 14 >

1 Wata ranar Asabaci, ya shiga gidan wani daya daga cikin shugabanin Farisawa domin cin abinci, mutane kuwa suna sa masa idanu. 2 Sai ga wani a gabansa mai ciwon fara. 3 Yesu ya tambaye masanan attaura da Farisawa, “Ya halata a wakar a ranan Asabaci, ko a'a?” 4 Amma suka yi shiru. Yesu kuwa ya kama shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi. 5 Sai yace masu, “Wanene a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya fadi a rijiya ran Asabaci, ba zai fitar da shi nan da nan ba?” 6 Sai suka kasa ba da amsar wadannan abubuwa. 7 Sa'adda Yesu ya lura da yadda wadanda aka gayyato sun zabi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali yana ce masu, 8 “Sa'adda wani ya gayyace ka zuwa bikin aure, kada ka zauna a wuri mai daraja, domin yana yiwuwa an gayyaci wani wanda ya fi ka daraja. 9 Sa'adda wanda ya gayyace ku duka biyu ya zo, zai ce maka, 'Ka ba mutumin nan wurinka,' sa'annan a kunyace za ka koma mazauni mafi kaskanci. 10 Amma idan an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi kaskanci, domin idan wanda ya gayyace ka ya zo, yana iya ce maka, 'Aboki, hawo nan mana'. Sannan za ka sami girma kenan a gaban dukan wadanda kuke zaune tare a kan teburi. 11 Duk wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, wanda ya kaskantar da kansa, kuma daukaka shi za a yi”. 12 Yesu ya ce wa mutumin da ya gayyace shi, “Idan za ka gayyaci mutum cin abinci ko biki, kada ka gayyaci abokanka, ko 'yan'uwanka, ko danginka, ko makwabtanka masu arziki, kamar yadda suna iya gayyatar ka, sai ya zama an maida maka. 13 Amma idan za ka kira biki sai ka gayyace matalauta, da nakasassu, da guragu, da makafi, 14 za ka kuwa sami albarka da yake ba su da hanyar saka maka. Gama za a saka maka a ranar tashin masu adalci.” 15 Da daya daga cikin wadanda ke zama akan teburi da Yesu ya ji wadannan abubuwa, sai ya ce masa, “Albarka ta tabbata ga wanda zai ci abinci a mulkin Allah!” 16 Amma Yesu ya ce masa, “Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa. 17 Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa ya ce wa wadanda aka gayyata, “Ku zo, duk an shirya kome.” 18 Sai dukansu, suka fara kawo dalilai. Na farko ya ce masa, 'Na sayi gona, lalle ne in je in gan ta. Ina rokonka ka dauke mani.' 19 Sai wani ya ce, 'Na sayi shanu garma biyar, ina so in gwada su. Ina ronkan ka, ka dauke mani.' 20 Wani mutum kuma ya ce, 'Na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.' 21 Da bawan ya zo ya fadi wa maigidansa wadannan abubuwa, sai maigidan yayi fushi, ya ce wa bawansa, jeka da sauri ka bi cikin titunan birni da kwararo-kwararo, ka kawo gajiyayyu, da nakasassu, da makafi, da guragu.' 22 Sai bawan ya ce, 'Maigida, abin da ka umarta an gama, amma har yanzu da sauran wuri.” 23 Sai maigidan ya ce wa bawan, 'Jeka, ka bi kwararo-kwararo da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. 24 Gama ina gaya maku, babu ko daya daga cikin mutanen da na gayyata da farko da zai dandana bikina.” 25 Ana nan, taron suna tafiya tare da shi, sai ya juya ya ce masu, 26 “Duk mai zuwa wurina amma bai ki mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa maza da mata ba - I, har da ransa ma, ba zai iya zama almajirina ba. 27 Duk wanda bai dauki gijiyensa ya biyo ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28 Wanene a cikinku wanda yake niyyar gina bene, da ba zai zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba tun da farko, ko yana da ishashen kudi da zai iya kare aikin? 29 Kada ya zama bayan da ya sa harsashin ginin, ya kasa gamawa, har duk wadanda suka gani su fara yi masa ba'a, 30 su rika cewa, ga mutumin nan ya fara gini amma ya kasa gamawa.' 31 Ko kuwa wanne sarki ne, in za shi je yaki da wani sarki, da ba zai zauna da farko ya yi shawara ya ga ko shi mai jarumawa dubu goma zai iya karawa da dayan sarkin mai jarumawa dubu ashirin ba? 32 In kuwa ba zai iya ba, to tun wancan yana nesa, sai ya aiki wakili ya kuma tambayo sharudan salama. 33 Haka ma, ba wani a cikinku wanda bai rabu da duk abin da ya mallaka ba, da zai iya zama almajirina.” 34 “Gishiri abu ne mai kyau, amma idan gishiri ya sane, da me za a dadada shi? 35 Ba shi da wani anfani a kasa, ko ya zama taki. Sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, ya ji.”

< Luka 14 >