< Kolossiyawa 2 >

1 Ina so ku san yadda na sha faman gaske dominku, domin wadanda ke a Lawudikiya, da kuma wadansu da yawa da a jiki basu taba ganin fuska ta ba.
Porque quero que saibaes quão grande combate tenho por vós, e pelos que estão em Laodicea, e por quantos não viram o meu rosto em carne;
2 Na yi aiki saboda zuciyar su ta sami karfafawa ta wurin hada su cikin kauna zuwa dukan arziki na tabbaci da fahimtar asirin gaskiya na Allah, wato Almasihu.
Para que os seus corações sejam consolados, e estejam unidos em caridade, e em todas as riquezas da plenitude de intelligencia, para conhecimento do mysterio do Deus e Pae, e do Christo.
3 A cikinsa dukan taskar hikima da sani ke boye.
No qual estão escondidos todos os thesouros da sabedoria e da sciencia.
4 Na fadi haka domin kada wani ya yaudare ku da jawabi mai jan hankali.
E digo isto, para que ninguem vos engane com palavras persuasivas na apparencia.
5 Ko da yake ba na tare da ku a jiki, duk da haka ina tare da ku a cikin Ruhu. Ina murnar ganin ku a yanayi mai kyau da kuma karfin bangaskiyar ku cikin Almasihu.
Porque ainda que esteja ausente quanto ao corpo, todavia em espirito estou comvosco, regozijando-me, e vendo a vossa ordem, e a firmeza da vossa fé em Christo.
6 Kamar yadda kuka karbi Almasihu Ubangiji, ku yi tafiya cikinsa.
Pois, como recebestes o Senhor Jesus Christo, assim tambem andae n'elle,
7 Ku kafu da karfi a cikinsa, ku ginu a kansa, ku kafu cikin bangaskiya kamar yadda aka koya maku, ku yawaita cikin yin godiya.
Arraigados e sobreedificados n'elle, e confirmados na fé, assim como fostes ensinados, abundando em acção de graças.
8 Ku lura kada wani ya rinjaye ku ta hanyar ilimi da yaudarar wofi bisa ga al'adun mutane, bisa ga bin abubuwan duniya, ba na Almasihu ba.
Olhae que ninguem vos sobresalte por meio de philosophias e vãs subtilezas, segundo a tradição dos homens, segundo os rudimentos do mundo, e não segundo Christo:
9 A cikinsa ne dukan Allahntaka ta bayyana ta jiki.
Porque n'elle habita corporalmente toda a plenitude da divindade;
10 Ku kuwa kun cika a cikinsa. Shine gaban kowanne iko da sarauta.
E n'elle estaes perfeitos, o qual é a cabeça de todo o principado e potestade:
11 A cikinsa ne aka yi maku kaciya, ba kaciya irin da yan adam suke yi ba, ta cire fatar jiki, amma ta kaciyar Almasihu.
No qual tambem estaes circumcidados com uma circumcisão não feita por mão no despojo do corpo da carne, na circumcisão de Christo:
12 An binne ku tare da shi ta wurin baftisma. Kuma a cikinsa ne aka ta da ku ta bangaskiya a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga mutattu.
Sepultados com elle no baptismo, no qual tambem resuscitastes com elle pela fé no poder de Deus, que o resuscitou dos mortos.
13 A lokacin da kuke matattu cikin laifofinku, a cikin rashin kaciyar ku ta jiki, ya rayar da ku tare da shi kuma ya yafe maku dukan laifofinku.
E, quando vós estaveis mortos nos peccados, e na incircumcisão da vossa carne, vos vivificou juntamente com elle, perdoando-vos todas as offensas,
14 Ya share rubutattun basussukanku da ka'idodin da suke gaba da mu. Ya cire su duka ya kafa su a kan giciye.
Havendo riscado a cedula que contra nós havia nas ordenanças, a qual de alguma maneira nos era contraria, e a tirou do meio de nós, encravando-a na cruz.
15 Ya cire ikoki da sarautu. A fili ya falasa su ya shugabance su zuwa ga bukin nasara ta wurin giciyensa.
E, despojando os principados e potestades, os expoz publicamente á vergonha, e triumphou d'elles por ella.
16 Saboda haka, kada kowa ya shari'anta ku ta wurin ci ko sha, ko kuma sabon wata, ko game da ranakun Assabaci.
Portanto ninguem vos julgue pelo comer, ou pelo beber, ou por causa dos dias de festa, ou da lua nova, ou dos sabbados;
17 Wadannan sune inuwar abubuwan da ke zuwa nan gaba, amma ainihin shi ne Almasihu.
Que são sombras das coisas futuras, mas o corpo é de Christo.
18 Kada kowa wanda ke son kaskanci da sujadar mala'iku ya sharantaku ku rasa sakamakonku. Irin wannan mutum yana shiga cikin abubuwan da ya gani ya zama mai girman kai a tunaninsa na jiki.
Ninguem vos domine a seu bel-prazer com pretexto de humildade e culto dos anjos, mettendo-se em coisas que nunca viu; estando debalde inchado no sentido da sua carne;
19 Ba ya hade da kai. Daga kan ne dukan jiki da gabobi da jijiyoyi ke amfani suna kuma hade tare; yana girma da girman da Allah yake bayarwa.
E não estando ligado á cabeça, da qual todo o corpo, provido e organisado pelas juntas e ligaduras, vae crescendo em augmento de Deus.
20 In kun mutu tare da Almasihu ga ala'muran duniya, don me kuke rayuwa kamar kuna karkashin duniya:
Portanto, se estaes mortos com Christo quanto aos rudimentos do mundo, porque vos carregam ainda de ordenanças, como se vivesseis no mundo?
21 “Kada ku rike, ko ku dandana ko ku taba?”
Taes como: não toques, não proves, não manuseis:
22 Dukan wadannan abubuwa karshen su lalacewa ne in ana amfani da su, bisa ga kaidodi da koyarwar mutane.
As quaes coisas todas perecem pelo uso, segundo os preceitos e doutrinas dos homens;
23 Wadannan dokoki suna da hikima ta jiki irin ta addini da aka kago na kaskanci da kuma wahalar da jiki. Amma ba su da amfanin komai a kan abin da jiki ke so.
As quaes teem na verdade alguma apparencia de sabedoria, em devoção voluntaria, humildade, e mau tratamento do corpo, mas não são de valor algum para satisfação da carne

< Kolossiyawa 2 >