< 1 Korintiyawa 14 >

1 Ku dafkaci kauna kuma ku himmatu domin baye bayen ruhaniya, musamman domin kuyi anabci.
Segui a caridade, e procurai com zelo os dons espirituais, mas principalmente o de profetizar.
2 Domin wanda yake magana da harshe bada mutane yake magana ba amma da Allah. domin babu mai fahimtarsa saboda yana zancen boyayyun abubuwa ciki Ruhu.
Porque o que fala língua estranha não fala aos homens, senão a Deus; porque ninguém o entende, e em espírito fala de mistérios.
3 Amma wanda yake anabci da mutane yake magana domin ya gina su, ya karfafa su, kuma ya ta'azantar dasu.
Mas o que profetiza fala aos homens para edificação, exortação e consolação.
4 Wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ginawa, amma mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ginawa.
O que fala língua estranha edifica-se a si mesmo, mas o que profetiza edifica a igreja.
5 To, fatana ace dukan ku kuna magana da harsuna. Amma fiye da hakama, fatana ace kuyi anabci. Wanda yake anabci yafi wanda yake magana da harsuna ( sai dai idan wani ya fassara domin ikilisiya ta ginu).
E eu quero que todos vós faleis línguas estranhas, mas muito mais que profetizeis, porque o que profetiza é maior do que o que fala línguas estranhas, a não ser que também intérprete, para que a igreja receba edificação.
6 Amma yanzu, 'yan'uwa, in na zo wurin ku ina magana da harsuna, ta yaya zaku karu dani? ba zaya yiwu ba, sai idan nayi maku magana da wahayi, ko sani, ko anabci, ko koyarwa.
E agora, irmãos, se eu for ter convosco falando línguas estranhas, que vos aproveitaria, se vos não falasse ou por meio da revelação, ou da ciência, ou da profecia, ou da doutrina?
7 Idan kayan kida marasa rai suna fitar da sauti - kamar su sarewa da algaita - kuma basu fitar da amo daban daban, ta yaya wani zaya san irin amon da sarewar da algaitar suke kadawa?
Da mesma sorte, se as coisas inanimadas, que fazem sonido, seja flauta, seja Cithara, não formarem sons distintos, como se saberá o que se toca com a flauta ou com a Cithara?
8 Domin idan aka busa kaho da sauti marar ma'ana, ta yaya wani zaya san lokacin da ya dace ya shirya zuwa yaki?
Porque, se a trombeta der sonido incerto, quem se preparará para a batalha?
9 Haka yake game da ku. Idan kuka furta zance marar ma'ana, ta yaya wani zaya fahimci abinda kukace? zaku yita magana, kuma babu wanda zaya fahimce ku.
Assim também vós, se com a língua não pronunciardes palavras bem inteligíveis, como se entenderá o que se diz? porque estareis como que falando ao ar
10 Babu shakka akwai harsuna daban daban a duniya, kuma babu wanda baya da ma'ana.
Há, por exemplo, tantos gêneros de vozes no mundo, e nenhuma delas é sem significação.
11 Amma idan ban san ma'anar wani harshe ba, zan zama bare ga mai maganar, kuma mai maganar zaya zama bare a gareni.
Porém, se eu ignorar o sentido da voz, serei bárbaro para aquele a quem falo, e o que fala será bárbaro para mim.
12 haka yake gare ku. Tun da kuna da dokin bayyanuwar Ruhu, ku himmatu da habaka cikin gina ikilisiya.
Assim também vós, pois que desejais dons espirituais, procurai abundar neles, para edificação da igreja.
13 To wanda yake magana da harshe yayi addu'a domin ya iya fassarawa.
Pelo que, o que fala língua estranha, ore para que possa interpretar.
14 Domin idan nayi addu'a da harshe, ruhuna yayi addu'a, amma fahimtata bata karu ba.
Porque, se eu orar em língua estranha, o meu espírito ora bem, mas o meu entendimento fica sem fruto.
15 To, me zan yi? Zan yi addu'a da ruhuna, in kuma yi addu'a da fahimtata. Zan yi raira waka da ruhuna, kuma in raira waka da fahimtata.
Que farei pois? Orarei com o espírito, mas também orarei com o entendimento; cantarei com o espírito, mas também cantarei com o entendimento.
16 In ba haka ba, idan ka yi yabon Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake waje zai ce, “Amin” a kan godiyar da kake yi in bai san abin da kake fada ba?
Doutra maneira, se tu bendisseres com o espírito, como dirá o que ocupa o lugar de indouto, o amém, sobre a tua benção, visto que não sabe o que dizes?
17 Babu shakka kayi godiya sosai, amma wanin baya ginu ba.
Porque realmente tu dás bem as graças, mas o outro não é edificado.
18 Nagodewa Allah ina magana da harsuna fiye da ku duka.
Dou graças ao meu Deus, que falo mais línguas do que vós todos.
19 Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in yi magana da kalmomi biyar cikin fahimta saboda inganta wadansu fiye da dubu goma da harshe.
Porém eu antes quero falar na igreja cinco palavras na minha inteligência, para que possa também instruir os outros, do que dez mil palavras em língua estranha.
20 'Yan'uwa, kada ku zama yara cikin tunani, sai dai a wajen aikin mugunta, ku yi halin jarirai, amma a tunaninku ku girma.
Irmãos, não sejais meninos no entendimento, mas sede meninos na malícia, e adultos no entendimento.
21 A rubuce yake a shari'a cewa, “zan yi magana da mutanen nan ta wurin mutane masu bakin harsuna, da kuma lebunan baki. Duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba”, in ji Ubangiji.
Está escrito na lei: Por gente de outras línguas, e por outros lábios, falarei a este povo; e ainda assim me não ouvirão, diz o Senhor.
22 Amma harsuna alamu ne, ba ga masu bada gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa alama ce ga masu ba da gaskiya, amma ba don marasa bangaskiya ba.
De sorte que as línguas estranhas são um sinal, não para os fieis, mas para os infieis; e a profecia, não para os infieis, mas para os fieis.
23 Saboda haka, in dukan ikilisiya ta taru, kowa kuwa yana magana da wasu harsuna, wadansu na waje da kuma marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun haukace ba ba?
Se pois toda a igreja se congregar num lugar, e todos falarem línguas estranhas, e entrarem indoutos ou infieis, não dirão porventura que estais loucos?
24 In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko wani daga waje ya shigo, maganar kuwa zata ratsa shi. Za a ma hukanta shi a kan maganar,
Mas, se todos profetizarem, e algum indouto ou infiel entrar, de todos é convencido, de todos é julgado.
25 asiran zuciyarsa kuma za su tonu. Sakamokon haka, sai ya fadi ya yi wa Allah sujada, zaya furta cewa lallai Allah yana tare da ku.
E assim os segredos do seu coração ficarão manifestos, e assim, lançando-se sobre o seu rosto, adorará a Deus, publicando que Deus está verdadeiramente entre vós.
26 Sai me kuma 'yan'uwa? idan kuka tattaru, wani yana da zabura, koyarwa, wahayi, harshe, ko fassara. Kuyi komai domin gina ikilisiya.
Que fareis pois, irmãos? Quando vos ajuntais, cada um de vós tem salmo, tem doutrina, tem língua estranha, tem revelação, tem interpretação. Faça-se tudo para edificação.
27 Idan wani yayi magana da harshe, bari a sami mutum biyu ko uku a yawansu, kuma kowa yayi daya bayan daya. Sai wani ya fassara abinda aka fada.
E, se alguém falar língua estranha, faça-se isso por dois, ou quando muito três, e por vezes, e um intérprete.
28 Amma idan babu wanda zaya fassara, bari dukansu suyi shiru a ikilisiya. Bari kowa yayi wa kansa maganar a gida shi kadai da kuma Allah.
Mas, se não houver intérprete, esteja calado na igreja; porém, fale consigo mesmo, e com Deus.
29 Bari annabawa biyu ko uku suyi magana, bari sauran su saurara tare da bambance abinda ake fada.
E falem dois ou três profetas, e os outros julguem.
30 Idan kuma anba wani fahimta wanda yana zaune a cikin sujadar, bari wanda yake ta magana kafin yanzu yayi shiru.
Porém, se a outro, que estiver assentado, for revelada alguma coisa, cale-se o primeiro.
31 Dukanku kuna iya yin annabci daya bayan daya, domin kowannen ku yayi koyi, a kuma samu karfafawa.
Porque todos podereis profetizar, uns depois dos outros; para que todos aprendam, e todos sejam consolados.
32 Gama ruhohin annabawa suna karkashin annabawa,
E os espíritos dos profetas estão sujeitos aos profetas.
33 domin Allah ba Allahn rudu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikllisiyoyin masu bangaskiya.
Porque Deus não é Deus de confusão, senão de paz, como em todas as igrejas dos santos.
34 Mataye suyi shiru a ikilisiyoyi. Domin ba a basu dama ba suyi magana. A maimako, su zama masu sadaukar da kansu, kamar yadda doka ta ce.
As vossas mulheres estejam caladas nas igrejas; porque lhes não é permitido falar, mas estejam sujeitas, como também ordena a lei.
35 Idan akwai abinda suke so su koya, bari su tambayi mazajen su a gida. Domin abin kunya ne mace tayi magana a ikilisiya.
E, se querem aprender alguma coisa, interroguem em casa a seus próprios maridos; porque é indecente que as mulheres falem na igreja.
36 Daga wurinku maganar Allah ta zo ne? ko kuwa a gare ku kadai ta iso?
Porventura saiu dentre vós a palavra de Deus? Ou veio ela somente para vós?
37 In wani yana zaton shi ma annabi ne, ko kuwa mai ruhaniya, to, sai ya fahimta, abin nan da nake rubuta maku umarni ne daga wurin Ubangiji.
Se alguém cuida ser profeta, ou espiritual, reconheça que as coisas que vos escrevo são mandamentos do Senhor.
38 In kuwa wani ya ki kula da wannan, shi ma kada a kula da shi.
Se alguém, porém, o ignora, ignore.
39 Saboda haka, 'yan'uwa, ku yi marmarin yin annabci sosai, sa'an nan kada ku hana kow yin magana da harsuna.
Portanto, irmãos, procurai, com zelo, profetizar, e não proibais falar línguas.
40 Sai dai a yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari.
Mas faça-se tudo decentemente e com ordem.

< 1 Korintiyawa 14 >