< Zakariya 6 >

1 Na sāke ɗaga kai sama, sai ga kekunan yaƙi guda huɗu a gabana suna fitowa tsakanin duwatsu guda biyu, duwatsun tagulla!
Again I lifted up my eyes, and saw, and behold, four chariots came out from between two mountains; and the mountains were mountains of bronze.
2 Karusa ta farko tana da jajjayen dawakai, ta biyu kuma baƙaƙen dawakai,
In the first chariot were red horses. In the second chariot were black horses.
3 ta ukun farare dawakai, ta huɗu kuma dawakai masu ɗigo-ɗigo a dukan jikinsu, dukansu kuwa ƙarfafa.
In the third chariot were white horses. In the fourth chariot were dappled horses, all of them powerful.
4 Sai na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”
Then I asked the angel who talked with me, “What are these, my lord?”
5 Mala’ikan ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu na sama, waɗanda suka fito daga wurin Ubangiji na dukan duniya.
The angel answered me, “These are the four winds of the sky, which go out from standing before the Lord of all the earth.
6 Wannan mai baƙaƙen dawakai zai nufi wajen ƙasar arewa, mai fararen dawakai zai nufi wajen yamma, sai kuma mai dawakai masu ɗigo-ɗigo a jiki zai nufi wajen kudu.”
The one with the black horses goes out toward the north country; and the white went out after them; and the dappled went out toward the south country.”
7 Da ƙarfafa dawakan suka fito, sai suka yi marmari su ratsa dukan duniya. Sai ya ce, “Ku ratsa dukan duniya!” Saboda haka suka ratsa dukan duniya.
The strong went out, and sought to go that they might walk back and forth through the earth. He said, “Go around and through the earth!” So they walked back and forth through the earth.
8 Sai ya kira ni ya ce, “Duba, waɗanda suka nufi wajen ƙasar arewa sun ba wa Ruhuna hutu a ƙasar arewa.”
Then he called to me, and spoke to me, saying, “Behold, those who go toward the north country have quieted my spirit in the north country.”
9 Maganar Ubangiji ta zo mini, ta ce,
Yahweh’s word came to me, saying,
10 “Ka karɓi azurfa da zinariya daga masu zaman bauta Heldai, Tobiya, Yedahiya, waɗanda suka iso daga Babilon. A ranar kuma ka je gidan Yosiya ɗan Zefaniya.
“Take of them of the captivity, even of Heldai, of Tobijah, and of Jedaiah; and come the same day, and go into the house of Josiah the son of Zephaniah, where they have come from Babylon.
11 Ka ɗauki azurfar da zinariyar ka yi rawani, ka ɗora shi a kan babban firist, Yoshuwa ɗan Yehozadak.
Yes, take silver and gold, and make crowns, and set them on the head of Joshua the son of Jehozadak, the high priest;
12 Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji.
and speak to him, saying, ‘Yahweh of Armies says, “Behold, the man whose name is the Branch! He will grow up out of his place; and he will build Yahweh’s temple.
13 Shi ne zai gina haikalin Ubangiji, za a kuma martaba shi da daraja, zai kuma zauna yă yi mulki a kan kursiyinsa. Zai zama firist a kan kursiyinsa. Kuma a tsakanin biyun za a sami zaman lafiya.’
He will build Yahweh’s temple. He will bear the glory, and will sit and rule on his throne. He will be a priest on his throne. The counsel of peace will be between them both.
14 Za a ba Heldai, Tobiya, Yedahiya da kuma Hen ɗan Zefaniya kamar abin tunawa a cikin haikalin Ubangiji.
The crowns shall be to Helem, to Tobijah, to Jedaiah, and to Hen the son of Zephaniah, for a memorial in Yahweh’s temple.
15 Waɗanda suke nesa za su zo su taimaka gina haikalin Ubangiji, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Wannan zai faru in kuka yi biyayya sosai ga Ubangiji Allahnku.”
Those who are far off shall come and build in Yahweh’s temple; and you shall know that Yahweh of Armies has sent me to you. This will happen, if you will diligently obey Yahweh your God’s voice.”’”

< Zakariya 6 >