< Zabura 87 >

1 Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki. 2 Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub. 3 Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, (Sela) 4 “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’” 5 Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.” 6 Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” (Sela) 7 Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”

< Zabura 87 >