< Zabura 8 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai. 2 Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru. 3 Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu, 4 wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi? 5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma. 6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa, 7 dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji, 8 tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku. 9 Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!

< Zabura 8 >