< Zabura 70 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo. Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni. 2 Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan masu sha’awar gani lalacewata su juye baya da kunya. 3 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su juye baya saboda kunyansu. 4 Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!” 5 Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.

< Zabura 70 >