< Zabura 64 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba. 2 Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta. 3 Sukan wāsa harsunansu kamar takuba su harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa. 4 Sukan yin kwanto su harbi marar laifi; sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro. 5 Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu, sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu; su ce, “Wa zai gan su?” 6 Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce, “Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa. 7 Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi. 8 Zai juya harshensu a kansu yă kuma kawo su ga hallaka; duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a. 9 Dukan mutane za su ji tsoro; za su yi shelar ayyukan Allah su kuma yi tunanin abin da ya aikata. 10 Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji su kuma nemi mafaka a gare shi; bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi!

< Zabura 64 >