< Zabura 61 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata. 2 Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi. 3 Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi. 4 Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. (Sela) 5 Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka. 6 Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa. 7 Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi. 8 Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.

< Zabura 61 >